← Book details Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 112

Sashe 20

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Washe gari sae da Rynt tayiwa mami wanka snn ita ma tayi nata wnkn.
Ta gama shiri kenan taji an turo qofa saliha ta shigo mami taje da gudu ta rungumeta Rynt kuwa tazo cikin sakin fuska saliha tace "amarsu ta ango ya amarci?murmushi kawai Rnyt tayi snn tace"nidai yasu umma? Lafiyar su qalau tana ma gaida ke ,ta fad'i hkne tare da ajiye basket d'inda ke hannunta tace"ga break fast inji umma,Rynt tace"mun gode"
Byn sun zauna saliha
ke cewa yaya fa?Rynt tayi kmr ma bata ji ta ba tace"wai shin saliha yaushe ne kika ce zaku koma makaranta?
Saliha tace "kinsan na gaya miki cikin satin nn hutun mu ya qare sae aurenku yazo ya tsaida mu amma yanzu rnr lahadin nn zamu koma,Rynt tayi shiru can tace"to yaushe ne ake saka sabbin d'auka? Da zarar mun tafi yanzu munyi third term muka dawo gida mukayi hutu se mu koma first term to a lokacin ne ake kai sabbin d'auka sbd anyi canjin aji,yanzu za'ayi kmr wata nawa kafin haka don ni tunda inna tamin albishir d'in bokon nn na qagu naga na fara boko nn wlh,saliha tace"hm boko ko wahala ,komai wahalar sa zan so nayi saliha sbd a rayuwa ba abinda ke birge ni kmr ilimi, gskyr ki ne Rynt sbd ba abinda ya kai ilimi dad'i.....qofa suka ga an tura koda suka duba Ameera ce yamutse da fuska tace da saliha"wae ke a nn kika shigo, nikam ki sameni 6angaren anti malika, saliha tace"to sae idan zamu koma xaki ganni"
nn Ameera ta ka6a kai ta fita,Rynt tace"ai da kin bita kun tafi d'in"saliha ta ta6e baki tace"um um sae idan zamu koma"
Rynt bata sake cewa komai ba sae zama sukayi zasu ci abinci sae ga wani saqon abinci daga gurin inna, sosai Rynt taji dad'i sbd abincin da take mugun so ne inna ta aiko mata.

Ameera kuwa koda taje 6angaren su malika ko bud'e qofa basuyi ba sae da tayi ta fmn danna door bell snn sae can ta samu aka bud'e .
Man ne da malika rungume a jikinshi da gani yanzu ne tashin su don malika farin bedsheets ma ne a jikinta man kuwa yana sanye da white bathrobe yayinda fuskar sa take d'aure tamau yana kallon Ameera yace"lfy zaki mana wnn sammako hk?kafin Ameera tace"komai malika tace"haba my man ba qanwar ka bace? Ko qanwa tace sae tazo ta takura ni, kiss ta d'ora masa a gefen fuska tace"kuma fa tayi laifi amma ayi haquri ta shigo ta zauna sae muje muyi wanka ko,lumshe mata ido yayi alamar suje d'in ,ba tare da kowanen su yace da Ameera ta shiga ta zauna ba suka juya zasu tafi, malika ta kalli mohd tace"my man me xai hana ta d'aura mana break fast kafin mu fito don wlh yunwa nake ji"ba musu ya juyo ya kalli Ameera da bata riga ta shigo ba yace"ke shigo kije kitchen ki d'aura mana girki"
Ameera ta shigo tare da rufe qofa tana ji kmr ta fasa ihu don ta tsani aiki ba kad'an ba.
Mohd kuwa suna shiga d'aki malika ta jefar da bedsheets din jikinta ta dawo nakedness,hm mohd sae d'aukar ta yayi suka je toilet.

Bayan sati 1 da faruwar haka tuni su saliha sun koma school ,mohd da malika kuwa sae cin amarcin suke inda ko sau d'aya mohd bai ta6a leqa 6angaren Rynt ba.
Sam Rynt bata damu ba wacce har yanzu inna na aiko mata abinci,kuma bata da wani kad'ai ci sbd still mami na nn da kullum tare suke cin abincin su suna kallo.

Yau tun da safe da suka tashi mami keta kuka ita gida take son zuwa gun ummarta duk Rynt ta shiga damuwa tayi rarrashi har ta gaji amma fafau taqi shiru ita sae taje taga mamarta.
Ba yanda Rynt ta iya dole ta shirya dmn kaita gida tunda ba waya ne da ita ba bare ta kira azo a d'auke ta kuma ko banza tana son zuwa gida don zaman banzan nn ya isheta tana son komawa islamiyya.
Hijabinta har qasa ta zuba ta jawo hannun mami suka fito suna kawowa harabar gidan ta sami kanta da mamakin ganin mohd zaune kan resting chair shida wani mai kama dashi sak har ma baka babance su,sam mami bata kula dasu ba sae kuka ta ajiye wae Rynt ta d'auketa ita bacci take ji,nn Rynt ta d'auke ta tare da d'aura ta kan kafad'a sae jin tayi tace "lah anti ga yaya da anti amarya sun fito"a hnkali Rynt ta juya bayanta don ganin wad'anda mami ke nufi sae kawai taga mohd shida malika ta kalli gun resting chair taga still wad'an can su biyun suna nn zaune abinsu suna fira ga kuma mohd shida malika tsaye mutum uku kenan fa iri d'aya nn kan Rynt ya d'aure sosai tana tunanin shin dama su en uku ne.

Kuyi hqr da wnn.

Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[2:48PM, 5/2/2017] Billy giro😊: [ 1/11/2017]
🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮

🔮🔮🔮
_*page*_ *```25```*
Ita tasan a qauyen su akwai en uku amma biyu ke kama da juna se d'ayar ta fita daban amma su wad'anan su duka uku kama suke har ba'a banbance su........Malika ce ta katse ta da tunanin da take da tace"my man me wnn abar ta shigo yi mana a gida!
fita batun malika yayi yace da Rynt "ina zaki tafi?tace"gida mana"wa kika tambaya?ta6e baki tayi tace"tambaya"sae kawai ta juyawar ta zata wuce mami ta qwace daga jikinta ta tafi da gudu gun wad'an can mutane dake fira,man kuwa ya dakawa Rynt tsawa yace "kar ki kuskura ki qara ko tako d'aya!Rynt ta juyo shaye da toka tare da watsa masa idanuwanta a cikin nashi kafin yace komai
Malika ta riga shi da cewa "wae bala'i ni ban gane ba!ko kana nufin ka aureta d'in!yace"wace magana ce kuma wnn koma daga ciki ki jirani,tace"kam bala'i har akwai wata mace da ta isa!hm!ai kuwa yanzun nn zaki bar duniyar nn baki shirya ba!nn ta duqa cikin zafin nama ta ciro takalminta mai d'an karan tsini tayi kan Rynt zata doka mata a ka,mohd ya riqe takalmin ya kuma riqe malika dake fizge fizge zata qwace kanta,yace"meye haka ne malika aurenta dake kaina dashi da babu fa duk d'aya don ba kulata zanyi ba kinsani, cikin masifa tace"wlh koma yaya ne bazata rayu a matsayin mtr ka ba don sae na rabata da duniyar nn idan har baka sake ta ba,,a natse yace be wise mana malika na gaya miki fa aurena da ita na d'an wani lokaci ne kuma kinsan halina duk abinda nace hk ne koda sama da qasa zasu had'e kuwa,
ya fad'i hakane tare da rungume ta a qirjinsa,ita ko ta fashe masa da kukan shagwa6a tace"to kasan yanda zakayi da ita don wlh bana son na qara ganinta a gidan nn!to naji daina kukan ,nn yajata yana rarrashi ya shigar da ita cikin gida ya dawo.
Ya samu Rynt bata nn da ita har mami, kenan ta fita yayi shu'umin murmushi snn ya qarasa gurin en uwanshi, yace"ina wnn yrnyr take? D'ayan yace " ta fita yanzu but me yake faruwa ne kaida matn naka? Yace"is nothing ku tashi muje kuyi sallama da malika d'in sbd fita zamuyi yanzu zuwa gaida su Abba,nn suka tashi suka shiga daga cikin gidan.

Rynt kuwa da qyar ta sami napep sbd yanayin anguwar ,
basu zarce koina ba sae gidan su man suna shiga suka had'u da Abba zai fita, Rynt ta durqusa da ladabi tana gaida shi, fuskar shi wasae yake amsa mata gaisuwar snn ya dafa kan mami yace"autar mama ya sabuwar anguwar taku? ba dad'i kullum mu kad'ai a cikin gida daga ni sae anti ba mai kawo mana fira kuma mu kad'ai ke baccin mu yaya baya zuwa taya mu,kai Abba gabad'aya ma tunda mukaje gidan sae yau kad'ai da zamu fita naga yaya sun fito shida anti amarya zasu tafi anguwa har mai wae Anti amarya ta tashi du......Rynt ce tayi saurin kwa6ar ta Abba kuwa ya shiga jinjina kai yace"lallai yau zai zo ya same ni a gidan nn"
ya sake cewa "shiga daga ciki Rynh zai zo ya sameni ne yau"

6angaren su saliha suka tafi wanda kafin su shiga sae da Rynt ta kwa6i mami kan kar ta sake irin srtn nn.
Murna sosai umman saliha tayi da ganin su,
sae dai Rnyt bata wani jima sosai ba tace"zata je ta kaida hjyr su pretty da kuma sauran mutanen gidan snn se ta tafi gidan inna.

Haka ko akayi ta tafi kowane 6angare ta kaida su sae dai 6angaren hjyr pretty ba irin sallamar da bata yi ba aka qi amsa mata bayan kuwa pretty da hjy suna jinta sukayi banza da ita, tayi zama har ta gaji da qarshe tayi tafiyarta.

Mohd kuwa suna shigowa gidan shida malika ya had'u da fushin Abba don yayi masa fad'a sosai ,mohd ya cika fam dan duk d'aukar sa Rynt ce ta kawo qarar shi,don har quduri ya d'auka a ransa sae yayi maganin ta idan suka koma gida,don ba abinda ya qara 6ata masa rai irin yanda Abba ya tilasta shi kan cewa duk safiya dole sae yaje duba lfyr Rynt ko ba ita keda duty ba kuwa.
Chapter 20 · 0% Book details