← Book details Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 112

Sashe 102

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Washe gari tun da safe mohd ya tafi ya bar Ryynt sae kuka take wanda ba irin rarrashin da bae mata ba amma taqi shiru hkn ya tafi ba a son ransa ba wanda ba don tafiyar ta zamar masa dole ba da ya fasa.
Malika kuwa ba kad'an ba taji dad'in tafiyar sa sbd wani tunanin da ya fad'o mata a rae da zata samu tacika burinta kafin ya dawo shiyasa yana barin gidan tasa qafa ta fita.
Bata wani jima sosai ba ta dawo bata zarce koina ba sae d'akin Ryynt bata shiga ba ta la6e tana jiyo sautin kukan Ryynt a hankali dan har lokacin bata daina kuka ba.
Le6ace da baki malika ta baro qofar tana mae fad'in"wae ke miji dad'i zaki ci ubanki an jima don wlh sae kinyi naqudar baki shirya ba"

Da dare ta sake dawowa ta samu Ryynt na bathroom tana wanka mami kuwa har tayi bacci.
Kai tsaye ta nufi fridge har zata bud'e ta hango ruwa da cup a ajiye kan bedside drawer nn taje da sauri ta bud'e gorar ruwan ta saka wani tablet qwara biyu a ciki ta shiga jijjiga gorar ruwan har maganin ya narke tsaf snn ta ajiye ta fita ta la6e a bakin qofar d'akin ta jira har sae da Ryynt ta fito daga wanka tana kallo Ryynt ta tafi kae tsaye gun bedside drawer ta tsiyaya ruwa a cup tasha snn ta nufi dressing mirror ta zauna tana shafa Vaseline.

Nan Malika ta bar qofar d'akin cike da murna ta kira fa'iza tace"tayani murna fa'iza wnn abar dae tasha maganin"
Fa'iza tace"dagaske?
Malika tace"wlh kuwa a gaban idona ina kallo tasha nasan ko ta kira kafin dae azo a tafi da ita asibiti abinda ke ciki ya gama hallakewa ita kuma kin san sauran"
Nan fa'iza ta fashe da dariya tace"aikin ki na kyau malika kika ce dae gobe akwai labari mae dad'i"
Malika tace"hm bari kawae kedai zan kiraki goben"
Daga nan ta katse wayar.

Ryynt kuwa lafiya lau ta gama shirinta na bacci mohd ya kirata a waya suka jima suna waya bayan sun gama wayar ne snn ta kwanta bacci a cikin baccinta ne wani irin ciwon baya ya farkadda ita wacce tun tana jin abun sannu sannu har abun ya soma yawa sae juyi take ta kasa komawa bacci.
A gurin mohd ma haka ta kasance don yana cikin baccin sa haka kawae yaga ya farka ya kuma rasa me ke masa dad'i sae tuñanin Ryynt da yake.
Nan kawae ya jawo wayar sa ya kira ta ba tare da ya damu da ganin ko qarfe nawa na dare ba shidae yaji lafiyar ta.
Ryynt da har ta zame kan bed tana durqushe kan guiwoyinta cikin matsanancin hali taji wayarta ta soma ring ganin mohd ne mea kiran yasa ta iya d'aga kiran amma kuma ta kasa cewa komai sae mohd ne keta magana bata iya bashi amsa.

Billy giro😊
[10:07PM, 5/2/2017] Billy giro😊: ```🔮BAZAN BARSHI BA🔮```

🔮🔮🔮
*page 88*
Sae can Ryynt ta samu da qyar tace"Mk bana jin dad'i ka bari da safe mayi waya"
Daga haka bata jira me zae ce ba ta katse kiran ta ajiye waya ta soma kuka a hnkli sbd zafin ciyon abinda take ji ya soma kaita maqura.
Mohd kuwa duk ya rud'e sae kiranta yake tayi amma bata d'aga ba nn kawai ya kira Nasir da inna ya sanar dasu halin da ake ciki.
A cikin daren Nasir ya tashi ya shirya yaje ya d'auko inna suka zo gidan.
Kai tsaye suka nufi d'akin Ryynt Nasir ya tsaya a bakin qofa inna ta shiga daga ciki ta sami Ryynt kwance cikin jini duk ta galabaita sae kuka take a wahal ce tana juyi a qasan tiles d'in d'akin.
A rud'e Inna ta qwalawa Nasir kira ya shigo d'akin wanda bae tsaya wata wata ba ya kama Ryynt inna ta kama masa suka fito da ita suka saka ta a mota ,
inna ta zauna baya tare da ita Nasir yaja motor a gaggauce suka bar gidan.
Nan itama malika ta fito ta shiga motar ta ta bisu dan tun shigowar su gidan tana sane asali ma ita da kanta ta bud'e musu qofa a lokacinda taji suna knocking.
Man hospital suka nufa ta parker motar ta tayi zamanta a ciki tana kallo aka shiga da Ryynt ta saki shu'umin murmushi d'auke da chewing gum a bakinta tana taunawa ta d'auki wayarta ta kira fa'iza ring d'aya biyu sae ga fa'iza ta d'aga ,
malika tace"au bakiyi bacci ba knn"
Fa'iza tace" inafa hubby bae barni ba kinsan yau ya dawo daga tafiya da qyar ma na samu ya saurara min yanzu haka ma yana bathroom yana wanka sae dae kuma ke ya akayi bakiyi bacci ba har yanzu?
Hm lallai fa'iza har kya tambaya ae yau banga ta bacci ba sae komai ya gama faruwa a gaban idona tukun don yanzu har wnn abar ta kira wnn tsofuwar da ake kira inna sun zo ita da Nasir suka kawo ta asibiti shine na biyosu sae kallon su kawae nake dan na tabbatar ba abinda likitawan zasu iya mata don kafin ma su iya yin komai abinda ke ciki ya riga ya gama hallakewa haka itama zafin aikin maganin da wahalar naquda bazai bar ma ta rayu ba don kan aje koina ma har ta fara bleeding"
Fa'iza tace"Au haba?
Malika tace"Wlh kuwa ae overdose na had'a mata maganin ynx jira kawae nake in ga an fito da gawar er banza.
Fa'iza tace"kae kinyi dae dae wlh,
ashe koni banga ta bacci ba yau sae dae najira kiran wayarki dmn naji kyakkyawan labari"
Malika tace"lallai
dae kam ki saurari kirana ko yaushe don yau kan farin ciki ma har sadaka sae nayi abinda ban ta6a yi ba a rayuwata kuwa"
Fa'iza tayi er dariya tace"kinga bye sae kin kirani dan naji alamar hubby zae fito daga bathroom baccin qarya nake so zanyi dan nasan halinsa in yaga ban koma bacci ba ko yayi wanka wlh zai iya sake nemana a second round"
Malika tayi er dariya tace"ae kima yi baccinki dan koni idan naga zasu 6ata min time gida zan koma dole dae da safe zanji labari don mutuwa dae ba 6oyuwa take ba kawae dae ki saurari kirana"
Fa'iza ta fashe da dariya tace"kae malika bakida dama wlh"
Malika tace"uhm kedai sae anijma"
nn suka katse wayar.
Daga nn ma kawai malika taja motar ta ta koma gida.
Chapter 102 · 0% Book details