← Book details Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 112

Sashe 30

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da dare Rynt ce ta gama sllr isha'i tayi zaune shiru tana tuna irin wnn lokaci ne byn sllr isha'i mutanen qauyen su suka d'auki gawar mahaifinta izuwa maqabarta har tabi su tana ta kuka har sae da matan qauyen suka rirriqe ta......shigowar mohd ne ya katse ta ta kalle shi sau d'aya ta kauda kai tare da kai hannu ta share hawayen fuskarta.
Yazo ya miqa mata wata babbar leda dake hannunshi yace"kar6i"ta kai hannu ta kar6a ba tare da ta ko kalle shi ba"yace"fito da duk abubuwan da ke cikin ledar"
Sae da ta qara share hawayenta snn tayi komai yanda yace.
School bag ce baqa mai kyau wankan gefe da littafan makaranta da biros da duk wani abu dai na aikin aji sae takalman mktrnta baqaqe da farar socks har da sabon niqabi yace" ki gwada takalman idan sun miki shikenan idan kuma basuyi ba kibawa mami ta maida min"
Still sae da ta sake share qwallah snn ta gyad'a masa kai, shi kuma ya fita ba tare da ya damu da ganin kukan da take ba.

Koda ta gwada takalmin dai dai qafar ta takai ta ajiye komai a cikin wardrobe d'inta sae ga mami ta shigo d'akin itama da nata kayan makarntar sae murna take itama za'a sata boko.

Washe gari da safe mohd ya shigo d'akin yace da Rynt ya kyn komai yayi?tace"eh amma uniform sun min yawa, yace"u are very stupid! tun yaushe uniform d'in suke hannun ki baki tashi gaya min ba sae yau, wae ke bagidajiya ko, nifa ba haka bane ban duba kayan bane sae yau, oya je gwada kayan kixo in gani,tace"kawai ni a rage min ba sae na gwada ba"yace"ai sae kiyi ta zama dasu hkn nn tunda baza ki iya gwadawa ba, ya fad'i haka ne tare da juyawa zai bar d'akin tayi saurin cewa "dawo zan gwada,nn yaje kan sofa ya zauna ita kuma ta nufi toilet ta sako kayan ta fito tana d'an kame kame, qyar Man ke kallonta don bai ga abin kame kame a jikin ta ba, kawai dai ya fhmci yrnya ce sosai har dai da ta sanya uniform amma duk da haka dai baza tayi J.s.s ba SS one yake da burin sata in yaso ya kira mai lesson ya qara fhmtar da ita a gida.
Yace"je cire kayan ki kawo taje ta cire ta kawo mai

Bai kar6i kayan ba sae tsaki ya mata snn yace"to haka kike nufin zan fita da kayan ba leda"
Kai tsaye taje ta saka kayan a leda ta kawo mai ya kar6a ya fita.
Ajiyar zuciya ta sauke sbd ganin masifa irin tashi koba komai dai zata bishi a hnkli don ganin ta samu tayi bokon nn tukun.

Sae dare ya maida mata kayan yace taje ta koma gwadawa ya gani idan sunyi,ta nufi toilet taje ta sako ta fito,abin mamaki idon sa ya kasa d'aukewa akan albarkatattun qirjinta da suka ciko rgr sae rgr ta mata mugun kyau,har dai da ta kasance farar riga ce mai dogon hannu da kuma corler ,saurin kauda idon sa yayi ya maida duban sa ga baby face d'inta yana mamakin jiya da ta saka kayan bai ma ga qirji a tare da ita ba ko don tufafin sun mata yawa sosai ne ,
nn dai ya basar yace"oya je cire rgr ki kawo min"taje bathroom ta cire uniform d'in ta kawo mai ,riga kawai ya kar6a ya bar wando a hannunta,tana tsaye ya bud'e buttons d'in rgr ya birkice ta,yaga da aka rage rgr ba'a yanke ta ba,hkn yayi masa dad'i don walwale d'inkin yake so zai yi ya maida ta er gidan jiya.
Ya d'ago ya kalli Rynt tare da fad'in"bani reza"tace"me kuma zakayi?yace"har kya tambaya ke baki ga yanda rgr ta miki bane"tace"nifa dai dai tamin kuma haka nake son abuta"yace"kina da hknli ya zaki je da wnn riga a makaranta"tace"to ai da hijabi akai...koda hijabi akai idan aka yi rashin sa'a iska mai qarfi ya kad'a hijabin yazo ya kwashe malaman mkrntr suka ga yanda rgr ta miki kice me!shaye da toka tace"me kuma ya kawo wnn tunanin"tsaki kawai yaja tare da jefar da rgr ya fita daga d'akin.
Ta bishi da ido tare da ta6e baki snn taje ta d'auki rgr ta linke kayan ta saka a wardrobe.

Washe gari ne Monday tasha fad'a sosai a gun man kafin take gama shiri sbd tayi lettin tashi.

Sunyi kyau sosai ita da mami dmn uniform d'in sun kar6e su.
White hijab ,white head tight ,farar riga da kuma blue d'in wando, amma ita mami akan fara rgr ta akwai handlees jacket snn hijab d'in qarami ne sosai don da kad'an ya wuce wuya,na Rynh kuwa ya kai mata a cinya wanda tsaf ya rufe farar rgr da ke ciki.
Duk makaranta d'aya za'a kaisu sbd makarantar tun daga kan nursery up to secondary school ake yi a ciki kuma mkrntr intanational ce ba laifi.

Malika ce can sama a balcony tana shan iskar safiyar rnr ,sae dariya take hango Rynt da tayi wae ace zago zago da ita sae yanzun zata fara secondary school ko ya en j.s.s one d'in zasu kalleta ne oho,nn ta koma kwashewa da wata dry.

6angaren su Rynt kuwa man ne ya fito gidan sauri sauri wanda duk fad'an da Rynt tasha kan lettin da tayi sae gashi ta riga shi kammala komai ita da har mami sae da ta shirya ma.
Yana isowa gurin ya kalli Rynt yace"bangane ba haka kike nufin zaki tafi fuskar ki a sake sae kace mai tallar fuska"tace"kmr ya bangane ba? Yace"bana son raini ina niqab d'inda kika gani a tare da kayan ne"tace"niqab a boko kuma ba sae lokacin islamiyya ko zan saka ba"ya watsa mata mugun kallo snn yace"da Allah malama ciro ki saka bana son raini!
Rai 6ace ta bud'e jakarta ta shiga fito da littafan ta long books da suka nemi cika mata hannu bata kuma kai ga niqab d'in ba.
Mohd yace"kar ki 6ata mana lokaci malama a ina niqab d'in yake? Tace" yana a cikin jakar"nn yasa hannu ya ciro niqab d'in,inda kai tsaye ya d'oro goshinta a qirjinsa yana d'aura mata niqab d'in sbd baya jin zai iya jiranta har ta mayarda littafan da ke hannun ta.
Niqab d'in sae ya mata kyau sosai sbd yanda yalwatacciyar girarta ta fito tmkr ansa gazal had'e da manyan idanuwanta farare da kuma rabin karan hancinta ba kmr nata na islamiya ba da ba'a ganin komai na fuskarta.
Mohd kuwa kallon wuyanta yake ta jikin hijabinta da yaga alamar bata kwantar da kwalar rgr ta ba.
Guntun tsaki yayi had'e da zira hannun sa cikin hijabinta yana gyara mata kwalar rigar.

Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[10:00PM, 5/2/2017] Billy giro😊: [ 1/24/2017]
🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮

🔮🔮🔮
*page* *34*
Saurin ja baya Rynt tayi shaye da toka tace"meye haka wae? Mohd ya dalla mata harara yace"bana son raini fa daga kawai kin samu na taimaka miki,da haka zakije collar riga a tsaye kina nuna musu asalin ke bagidajiya ce"
Kallon sa tayi rai 6ace wacce ko niqabin da ya d'aura mata wani irin haushi ya bata har niyyar tayi ma ta ture shi sae kuma ta tuna mami na gurin.
Yace"da Allah shiga mota kinyi tsaye kina kallon uwa wani baqonki!
Nan taje ta shiga motar zuciyar ta sae quna take.
Malika kuwa tun lokacinda taga man zai d'aurawa Rynt niqab ta sami kanta da miqewa zumbur sae kawai taga abinda yafi hkn wato hannun sa da ya zira a cikin hijabin Rynt.
A zafafe cikin masifa ta kama hnyr saukowa ,sae dae koda ta fito tuni motar su tabar gidan.
Wani irin qololon baqin ciki ne ya tokare ta a wuya, tace"kut zai dawo ya same ni ne wlh"

Nan tayi zaune a falo sae zaman jiran sa take wanda yayi 30 mnt kafin yake dawowa, yana shiga ta tari gaban shi riqe da qugu ,yace"ke lfyrki meye hk? cikin masifa tace "har ka tambaya wane irin abin kunya ne naga kana aikatawa a d'azun ,bayan ka d'aura mata niqab bai ishe ka ba shine ka wani xira haunnunka a cikin hijabinta tir!A fusace yace"ba a hijabinta na zira hannu na ba a cikin rgrta na zira, very stupid in ke uwar cikina ce da zaki wani tasa ni gaba kina tuhuma ta da wani banzan shirmen ki can.
Nn ya buga uban tsaki ya ra6a ta gefenta zai wuce, tayi saurin shan gaban shi ya dalla mata muguwar harara, da kanta tayi saurin bashi hnya ya wuce ta bishi da ido har sae da ya shige 6angaren shi snn tace"cabd'i lallai sae na tashi tsaye akan wnn er iskar yrnya,kai kuma dani kake zancen wlh zamu had'u a d'aki ne ai!snn ta tafi fuuu!zuwa d'akinta.
Chapter 30 · 0% Book details