Sashe 72
Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
🔮🔮🔮🔮
*```Page 67```*
Wacce ta kauda fuskarta gefe sbd qamshin turaren sa.
Mohd yakai hannu ya juyo fuskarta ,
ta watsa masa manyan idanuwan ta a cikin nashi cikin yanayi na alamar mene ne?
Yace"Ina son zamuyi magana ne"
Ta maida fuskar ta gefe tace"inajinka"
Yace"ba wata magana bace magana d'aya ce wacce kika sani wato zancen komawar ki gidana"
Ta girgiza kanta a natse ba tare da kalle sa ba tace"Aa ni bazan koma ba"
Yace"yi haquri dae kinji"
Tace"kawae kayi haquri kaima"
Yace"ni bazan iya bane"
Tace"amma kake tunanin ni zan iya"
Tayi mgnr ne yayinda ta kalle sa snn ta kauda kai.
Yace"meyasa baza ki iya haqura ba"
Tace"sbd rayuwar gidanka rayuwa ce da bazan iya taba"
Mohd yace"wnn rayuwar da kike tunani ae a dane amma ynz sabuwar rayuwa ce zamu gina nida ke"
Tace"Aa ni nafi son rayuwata a nn sbd nafi samun kwanciyar hankali"
Mohd yace"can ma d'in zaki sami kwanciyar hnkli fiye da tunanin ki"
Tace"fiye da tunani na zan sha duka na sani amma dai ba kwanciyar hnkli ba kam"
No Ryynt ki ajiye duka gefe dmn nayi miki alqawarin bazan ta6a sake kai hannu na a jikin da niyyar sake dukanki ba.
Tace" ta yaya bayan idan ranka ya 6aci baka da wani hukunci sae duka ,
rayuwar zo mu zauna kuwa bawai kullum cikin farin ciki ake zaune ba dole yau da gobe sae an sami sa6ani kuma ta yaya kake tunanin zan koma gidanka byn idan aka gaya ma magana yarda kake har ka d'auki hukunci ba tare da kayi bincike akai ba.
Numfashi ya fitar d'auke da alamar damuwa yace"Ryynt abinda ya faru ya riga da ya faru ina son dan Allah ki manta shi ki d'auka cewa yanzu wata sabuwar rayuwa ce zakiyi mai dad'in gaske da ba wani qunci ko tashin hnkli a cikinta"
Ryynt ta girgiza kanta a natse tace"ko d'aya bazan ta6a hangen abinda bashi bane"
Mohd yace"plz Ryynt ki fhmce ni.......
Ryynt da duk qamshin turaren sa ya soma fizgarta na son taji kanta a jikin sa tana mae shaqar qamshin ,
ta miqe tsaye da sauri tace"Dan Allah ka fita na gaya maka baxan koma ba wlh"
Cikin yanayi na alamar zai rarrasheta yaje zuwa riqo hannunta,taja baya da sauri had'e da fad'in "kar ka ta6ani bana so kuma dan Allah ka fita"
Mohd yace"yi haquri ki saurareni"
Tace"wlh indae akan komawa gidanka ne bazan ta6a saurararka ba don haka kawai ka fita"
Cikin mugun damuwa kmr zai yi kuka ya jawota da sauri zuwa jikin sa yace"haba Ryynt wae ta yaya kike tunanin zan iya rayuwa ne ba ke"
Ryynt dake yunqurin qwatar kanta tace"kan me wae ni to tunda dama can bada ni kake rayuwa ba"
Idanuwansa ya d'aura a cikin nata cikin muyar natsuwa yace"sbd ina sonki Ryynt"
Wani irin kallo ta mae snn ta girgiza kanta le6ace da baki tace"ni kuwa meye abin so a tare dani,nida sae wanda uwar sa ta mae baki ko zai soni"
Kallon ta yayi a sanyaye dan ya fhmci inda ta dosa yace"pls Ryynt ki daina zancen da ya riga ya wuce dan Allah"
Ta fizge kanta daga jikin sa rae 6ace tace"Dan Allah ka fita to"
Numfashi ya fitar cikin yanayin damuwa yana kallonta d'auke da idanuwansa da duk ya shiga damuwa sae sunyi jajur sun canza kala.
Bata tare da yace komai ba ya juya ya fita daga d'akin.
Ya wuce Saliha dake zaune a falo tana kallo,wacce ta bisa da kallo har ya fita sbd yanayin damuwar da ta gani a tare da shi.
Nan ta tashi ta nufi d'akin Ryynt wacce ta sama rae 6ace.
Taja hannunta suka zauna kan bed snn tace"Me yake faruwa ne Ryynt ko gida yake so ku koma baki tashi bane"
Ryynt ta kalle ta kawae dan ta fhmci bata san komai ba.
Saliha tace"kinga idan a kaina ne kawae ki koma gida gobe zanje can sae ma naje miki da mami ko"
Ryynt ta qirqiro d'an guntun murmushi tace"saliha knn nifa a nn nake zama yanzu rabona da wancan gidan har na manta"
Cikin mamaki saliha tace"kmr ya ban gane ba?
Ryynt tace"uhm kedai mu bar zancen muci gaba da firar mu kawai"
Saliha ta girgiza kanta tace"ina fa zancen fira kin d'auko min wata magana da najita banbarakwai me ya faru da kika dawo gidan inna da zama ko kin kusa haifuwa ne?
Da sauri Ryynt tace" haifuwa?
Saliha tace"eh mana ba kmr ciki na gani a jikin ki ba yanzun da na shigo.
Ryynt da ko kad'an bata ta6a kawo cikin yayi girman da za'a gane ba ta kalli saliha kmr zata yi kuka tace"wae ana ganin cikin?
Saliha tace"eh nima sae yanzu na fahimta da na shigo"
Kuka Ryynt ta fashe dashi saliha tace"kan me to tunda ba shege bane"
Ryynt bata ce komai ba sae kukanta take don ba abinda take tunani irin qila ma a school kowa ya gane tana d'auke da ciki byn ko da kuskure bata ta6a yarda ta nuna cewa mtr aure bace sbd bata so a sani.
Saliha dake kallonta za tayi magana knn wayar Ryynt ta shiga ruri saliha ce ta d'auko mata wayar kan bedside drawer ta bata wacce kafin ta kar6a sae da ta tsagaita kukanta ta kalli mae kiran wato umman saliha snn ta d'aga had'e da kara wayar a kunnen ta.
Tace"Na'am mama,eh ina ji"
Daga haka se tayi shiru lokaci mai tsawo tana sauraren umman saliha dake ta bata magana cikin rarrashi kan tayi haquri ta koma gidan mohd,wanda da fitar sa bai zarce koina ba sae gurinta dan yasan Ryynt zata ji maganar ta.
Ryynt sae sauraren umman saliha take cike da qwalla tap a idonta don ko kad'an bata son komawa gidan mohd amma ba yanda ta iya dole ta amince akan zata koma d'in sbd ta d'auki umman saliha tamkar uwa da bazata iya musa mata ba.
Tana gama wayar ne da en mintina sae ga kuma nasir ya sallamo da shima Man ne ya turo shi akan yaxo dan Allah ya qara bawa Ryynt haquri.
wanda duk da cewa yasan irin zamanda Ryynt tayi a gidan man yana son ta koma dmn ya fhmci irin nadamar da man yayi,kuma ko don qaruwar da suka samu a tsakanin su yana son ta koma.
Bayan sun amsa masa sallama ne ya shigo yasa Ryynt gaba yana rarrashi da ban haquri had'e da fhhmtr da ita ta kwantar da hnklinta inshaa Allah wnn karon zata ji dad'in zama ba kmr wancan karon ba.
Ita dae saliha sae sauraren su take har nasir ya gama rarrashin da yake ya fita ita kuma ta d'aura da nata dmn a iya abinda ta fhmta sa6ani Ryynt ta samu da man,wacce ta fhmci hkne tun daga kan wayar da taji tana yi da ummarta da kuma haqurin da nasir yazo yana qara bata.
Ita dae Ryynt gabad'aya jikin ta yayi sanyi dan ganin take shike nn rayuwar ta zata koma cikin qunci da rashin walwala.
Da dare guraren qarfe tara mohd ne ya shigo gidan ya sami inna a falo tana kallo ,ya gaida ta ta amsa ba yabo ba fallasa ya zauna jim kad'an snn yace"Ryynt fa?
Inna tace"tana ciki na rasa meke damunta kmr wata marar lfy nake ganin ta yau"
Man yayi shiru kawai don yasan ba wani abu bane ke damunta sae rashin son komawarta gidan shi.
Yace da inna "bari naje na ganta to"
Tace"to"
snn ya tashi ya tafi d'akin Ryynt ya sameta kwance tana bacci yaje gab da ita ya duqa a hnkli yana kallon fuskarta da ke mai mugun kyau idan tana bacci.
Ya jima a haka kafin yake maida dubàn sa kan jikinta da komai ya cicciko 6ul 6ul ya qara kyau da haske a nn idonsa yakai kan qirjinta da ya taso saman rgrta sbd yanda rgr ta d'an kama ta,
kai tsaye ya kauda idon sa a gun ya maida duban sa kan cikinta had'e da d'aura hannunsa akai ya shafa d'an cikinta da ya taso snn ya kai hannu zuwa yaye rgr jikinta dmn yaga cikin.
Se Ryynt ta shiga juyi a hnkli had'e da gyara kwanciyarta ta juya mishi baya.
Nan ya miqe tsaye ya kalle ta kawae snn ya juya ya bar d'akin yayinda Ryynt ta bisa da ido dan dama ba bacci take ba jin zai shigo yasa ta qirqiro baccin qarya.
Shi kuwa mohd a nn falo ya sami inna naci gaba da kallonta ya zauna yayinda inna ta kalle sa tace"ya akayi jikin ne ko kuwa?
Yace"Aa inna inaga bacci ne kawai don naji jikin nata ba zafi sae vacci da na samu tana yi"
Inna tace"inaga fa hkne sbd yau duk bata samu tayi baccin da ta saba yi ba sae fira da suka zauna ma yi ita da saliha wacce sae da yamma sosai ta bar gidan nn,
Mohd bai ce komai ba sae cewa yayi"to inna yaushe za'a bani Ryynt mu koma tunda dae ta amince zata koma.
Inna tayi shiru don tun d'azu da yamma yazo da kanshi ya snr da ita cewa Ryynt ta amince zata koma gidan sa har taji dad'i a ranta don ynx sae taji tana son Ryynt ta koma sbd ko kad'an bata son idan sunje qauyen su Ryynt mai gari yaji cewa har auren Ryynt ya mutu shiyasa ta qara jawa mohd kunne sosai kan ya riqe Ryynt amana kmr yanda Abba ya masa da yaje ya snr dashi.
Inna tace"muhammadu ai kasan ko zata koma sae munje qauyen su tukun don tun ba yau ba kabiru ke jiran idan Ryynt sunyi hutu se muje"
Mohd yace"inna idan qauyen nasu ba wani nisa me zae hana gobe muje don Allàh dmn so nake jibi mu fara shiryen shiryen tafiyar mu nida Ryynt.
Inna da dama tasan da zancen tafiyar sbd d'azun da yazo ya snr da ita ,
tace"to ai sae kaje ka snr da kabiru duk abinda yace kaga sae kazo ka snr dani.
Mohd yace"to"snn ya tashi ya fita.