← Book details Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 112

Sashe 10

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

7 days later
Rayyanat ce a kitchen ta gama wanke kwanika tana goge kitchen bayan ta gama ta koma d'aki.
Saliha ce ta shigo gidan ta sami Mohd shida inna sae fira suke sae da ta gaishe su snn ta zauna har inna na tambayar ta ya mutanen gida tace duk suna lafiya tace"to ya na ganki yau ke kad'ai ba abokiyar yawonki Ameera? Tana gida wai yau bata jin fita tace"ayyo to ya hajiyarki tana lfy dai ko?lfiya qalau wlh ta ma ce a gaida ke,ina amsawa ai yau tama kirani a waya mun gaisa kmr kullum,eh inna Rayyanah fa? Shiga daga ciki yanzun nn ma ta shiga.
Rayyanat na zaune tana duba litattanfanta na islamiya sae ga saliha ta shigo da sallamarta ,da sakin fuska Rayyanat ta tarbe ta ta nemi guri ta zauna tare da jawo littafan Rayyanat na Islamiya tace"ke yau fa Alhamis ko kin manta" Rayyanat tace"ai ba shirin zuwa makaranta nake yiba ina muraji'a ne sae gashi na sami kaina da mantuwa da wani gun a cikin littafin ishmawee babun sallati janazatee gun da ake cewa....cab ai ke ban kai babin ba wlh kad'an dai ya rage,nn taja hannunta tare da fad'in "amma muje gun yaya Man ya tuna miki kafin ya fita "cikin rashin fahimta Rayyanat tace "waye kuma haka?oops baza ki san sunan ba sbd da Muhammadu inna ke kiran shi, Man kuma complete name d'inshi ne frnds d'insa suka had'e wato Muhammad Aminullah Nasir shine har mu qannansa ke kiransa dashi sbd koda muka taso mun samu ana kiransa da sunan.
Ta6e baki tayi ba tare da tace komai ba Saliha tace "muje ya tuna maki ko"um um nafi son na tuna da kaina sbd zanfi riqe abun da kyau"to amma dai zaki ajiye muraji'an nn har zuwa dare tukun sbd ina son muje ki rakani familyn mamana,a natse Rayyanat ta ware kyawawan idanuwanta tana kallon saliha snn tace"ni d'in nn? Eh man ai anguwar ba nisa da nn kuma wa ke kad'ai na biyo gidan nn wlh ,don hk ki tashi ki shirya mu tafi,nifa ban son shiga inda ban sani bane saliha ki tafi kawai abunki kinji,
,kinji Ki sae kace wacce za'a cinye dan Allah nidai tashi ki shirya mu tafi ai da sannu ake yin sabo ba wai zama zakiyi tayi kice ba kya shiga mutane ba.
Turo qofar da akayi ne ya katse Rayyanat da abinda tayi niyyar fad'a,Saliha tace"yauwa inna dan Allah ina son Rayyanat xata rakani gidan Baaba.
Ba musu inna ta amince da su tafi.
Duk da Rayyanat bata so ba amma haka ta haqura Saliha ta tasa ta gaba tana mata kwalliya yayinda tace ta rufe idonta har sae an gama kwalliyar ko zata bud'e,
byn an gama kwalliyar Rayyanat na bud'e idanuwanta ta wani ware su kan tsananin kyawon da taga tayi har ma ta fara shakkun anya ita ce kuwa tace"saliha wnn kwalliyar na tafi ina dashi nikam rage min ita don wlh ni ko kwalliya ma banayi bare na iya fita da wnn kwalliyar haka,,,um um gsky ba abinda zan rage maki ,
kawai don baki saba kwalliya bane kika ga kmr tayi yawa amma dai dai take, da qyar Rayyanat ta iya yarda aka bar kwalliyar saliha ta bata Arabian gown ta saka ta jawo qatoton hijabinta zata zuba saliha ta dalla mata harara da wasa tace"meye haka zan gani ki wani zuba hijabi har qasa sae kace zaki tafi islamiyya ?ban gane ba saliha to dame kike son na fita?saliha bata ce mata komai ba sae hijabin ta cire mata ta d'auko top d'in gown ta roller mata, duk da cewa Rayyanat ba wata fara bace amma shirin ya matuqar d'aukar ta sae dai faffau tace bata iya fita da shirin sae tasa hijab Saliha ta buga qasa da sama a cewar ta duba ita ma fa irin shirin ne da ita amma ina sam Rayyanat bata yarda ba, bbu ynda Saliha ta iya da ita hka ta kyaleta da hijab din suka sallami inna da ke kitchen suna wainar flower da baaba hurera, inna na ganinsu ta washe baki tace "Ma'sha Allahu" saliha tace "ku fa ajiye mana namu inna, don nasan kina iya kwashewa gaba daya ki ba ma yaya" saliha na kai wa nn ta ja hannun Rayyanat suka fice daga kitchen din, kwance suka tar da shi a falo idonsa lumshe kmr mai bacci, lkci daya ya bude ido yana kallonsu, Saliha ta dan hade rae tace "sae mun dawo yaya" Rayyanat kam kauda kai tayi ita ma fuskarta a daure, mikewa yyi xaune da sauri yace "ina xa ki?" Dauke kai tayi tace "gidan fa kaka xa mu, kuma Hajiya ta sani" kallon Rayyanat ya tsaya yi da mmki ganin ynda ta wani hade rae, can ya mike ya nufi kitchen sae ga shi ya fito inna na biye da shi a baya tana cewa "lfya me ya faru?" Sae da suka karaso cikin falon snn ya juya yana kallon innar da kyau yace "dama tambaya ce xan maki, wae wnn yarinyar me aiki ce ko ko a ina kika jajubo ta" ya fadi yana nuna Rayyanat, inna ta ja dogon tsaki ta balla masa harara tace "uwar ka ce ba me aiki ba, wnn tayi maka kama da mai aiki, hka kawae kasa ma yarinya ido a gida, uwar me ta tsare maka, to in kai maye ne sae dae ka ci kanka wllh" a fusace ya karasa gaban Rayyanah yana mata wani mugun kallo fuskarsa a daure ya dago fuskarta da kyau yana kallo, ta kuma hade rae ita ma tana kallonsa da manyan idanuwanta, a nutse ya fara mgna, "daga yau, I mean daga this vry moment kika kuma min wani irin kallo a gidan nn, ko kuma kika gan ni kika ki gaida ni sae na....." Kukan da inna ta fashe da yasa ya tura ta da karfi, ya juya yana kallon innar, kwashe wayoyinsa yyi da ke kan kujera ya juya ya fice daga falon kmr xae tashi sama, inna ta bi sa da ja'irin yaro kawai, ta karaso gun Rayyanat tana matsar kwalla tace "kiyi hkuri kin ji 'yar nn, tambada yake ji yau shi yasa yyi maki hka, amma ki kyaleni da shi, da ubansa ma xan hada sa ni ya ja masa kunne ya daina xuwa min gida don baya tsinanani da komae da ma, sae dae in dafa in basa ya ci ya bar min kwanukan a nn ya kara gaba" Rayyanah tayi murmushi kawae tace "bbu komae inna" saliha da ko kadan bata ji ddin abinda yayan nata yyi ma Rayyanah ba ta ja ta a sanyaye suka fice daga falon don xuwa inda xa su.
Sae da suka fita daga gidan Saliha tace "kiyi hkuri Rayyanah hka yaya yake wani lkcn" Rayyanah tayi murmushi tace "A'a ni bn ji haushi ba wllh," saliha tace "yauwa, kuma don Allah ki dinga gaishesa in kun hadu" Murmushi kawae Rayyanat tayi bata ce komae ba, saliha tace "ke komae murmushi, ba sae ki ce min to ba" Rayyanat ta kuma yi mata murmushin tace "toh naji Saliha" saliha tayi dariya tace "yauwa ko ke fa."

Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[2:38PM, 5/2/2017] Billy giro😊: 🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮

```Na Billy giro😊```

28/12/2016

*🔮```12```🔮*
Washe gari kaf gidan Rayyanat ce ta gyare shi har wajen gidan wato gun faka motoci duk sae da ta share tsaf koina ya haskaka.
Snn taje kitchen don taya baaba hurera aikin abinci, baaba hurera tace "Aa Rayyanah yau kinyi aiki da yawa je kawai kiyi wanka kinsan yau juma'a qaramin lokaci ce," Rayyana tace "aa baaba bari kawai na tayaki wlh," "wlh jeki ai saura kad'an na qarasa tafi kiyi wanka kinji er albarka," cewar baaba hurera knn, murmushi kawai Rayyanat tayi ta juya ta fice daga kitchen.
wanka ta je tayi ta shirya cikin riga da skirt na atamfa da inna tayi mata, sukayi mata kyau kmr ba tashin qauye ba kan yanda sukayi d'as a jikinta.
qur'ani ta d'auko ta shiga karatun suratul kahfi, a dakin da inna ta bata ita kadae duk da ba kwana take ciki ba don tsoro.

Tunda daga kan gate da mohd ya shigo gidan yake qare ma ko ina na gidan kallo ganin yanda gidan yayi haske yayi kyau, as in very neat ba wai don ba a share gurin ba a'a sae don ganin sharar yau ta daban ce da kullum.

Faka motar sa yayi ya fito cikin motar cike da tafiyar sa ta qasaita ya isa cikin gidan yana duba agogon wrist dinsa.
Inna ya samu xaune a falo ta miqe qafafu tana casbi har yana jin sautin salati na fita a bakinta, murmushi yyi hade da mata sallama, kin amsawa tayi sae ma wani kallon masifa da ta watsa mai tace "idan kasan yau ma tambad'ar ce ta kawo ka ftr min daga gida!"
Muhd yayi murmushi ya karaso cikin falon tare da ajiye ledar hannunsa gefenta yana kallonta yace "ni abinci naxo ci" inna bata kula sa ba sae hannu da takai tana bud'e ledojin da ya ajiye mata 'ya'yan fruits ne da gasasshen naman rago sae gassashiyar qullin hantar rago gefe, lkci daya inna ta washe baki tace "Auu! sannu da xuwa mai gida, Allahu yyi maka albarka ya kuma nuna min aurenka" daga haka ta qwalawa Rayyanah kira.
Cikin hanzari Rayyanat ta fito daga d'aki tana ganin muhd zaune ta rage saurin da take inna na washe da baki har lkcn tace "zo er albarka ki kai ma hurera 'ya'yan itacen nn ta yanyanka mana daga nn ki biyo ma maigidana da nasa abinci idan an kammala."
Rayyanah tace "to" ta kar6i ledar fruit wacce sae a snn ta gaida muhd, dake bin ta da harara tun shigowarta, ba yabo ba fallasa ya amsa.
Chapter 10 · 0% Book details