← Book details Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 112

Sashe 108

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mohd dake driven bae zarce koina ba sae gidan sa wanda tun lokacin da ya shigo gate d'in gidan Ryynt ke kallon sa da mamaki har ya parker mota kafin tace komai wayar sa tayi qara ya d'aga wayar ya fito mota ya zagaya ta gefenta ya bud'e mata yaja hannun ta suka shiga ciki suka tsaya a falo sae kallon sa take yana waya.
Yana gama wayar tace"Mk kai da kace min family house zamu je ya kuma kazo damu nn"
Yayi murmushi yace"wayon manya na miki ba wani family house da zamu je nn nake nufin zamu zo"
Tace"to meyasa?
Yace"har kya tambaya ko kin manta na gaya miki cewa da kinyi arba'in zaki dawo ne"
Tace"uhm kaima dae da wasa kake Mk abu sae kace tulin wanki haka kawae ba shiri ka kwaso mu kace mun dawo knn,da akwai dae abinda ka shigo d'auka je ka d'auko mu tafi kasan mun bar alawiyya da yara a mota"
Yace"Allah da gaske nake miki mun dawo knn ba wani abunda nazo d'auka"
Tace"Mk bana son irin wasar nn dan Allah ka maida mu gida dan wlh ni ban shiryi dawowa ba"
Yace"Ryynt wane irin shiri kuma idan kayane gobe zanje da kaina gidan inna na kwaso maku komai"
Haba mk haka kawai zan dawo banje nayiwa kowa sallama ba nida nake son har qauyen mu sae naje.
Gaskiya Ryynt ni bazan iya harakar al'ada d'in nn ba wae ace don mutum yayi arba'in sae yaje yawo gidajen mutane kiyi haquri bana so ba kuma zakiyi ba amma zuwa qauyen ku bazan hanaki ba ko gobe kike so zan kaiki.
Ryynt ta girgiza kanta tace"gaskiya ni kawae ka maida ni bazan iya wnn abin kunyar ba ae sae ace da had'in bakina tunda ko inna bata sani ba"
Da mamaki yace"abin kunya kuma Ryynt kina mata ta dan na maida ki shine ya zamo abun kunya"
Tace"eh mana yau yau fa da yin arba'in se aji kawae na dawo haba gaskiya ni ka maidani"
Yace"wlh bari kiji ba inda zan maida ki kin dawo knn"
Cikin muryar kuka tace"wlh ni kuma bazan zauna ba sae na koma"
Rae 6ace mohd yace"shike nn gaki ga hanya jeki bazan hanà ki ba amma wlh kar ki kuskura kice zaki je min da yara ,kiga idan baza mu rayu ba dan ba ke"
A fusace ta fita tana fad'in ae dama bance da yaran naka zan tafi ba.
Cikin 6acin randa tafito d'auke dashi taje taja alawiyya zasu bar gidan ,
Alawiyya tace"Anti ina zamuje munbar su Ammar a mota?
Ryynt tace"ki barsu ubansu zae ji dasu"
Daga haka alawiyya bata sake cewa komai ba har suka fita suka tari napep suka wuce sae gidan inna.

Billy giro😊
[10:07PM, 5/2/2017] Billy giro😊: ```🔮BAZAN BARSHI BA🔮```

🔮🔮🔮
*page 92*
Suna shiga gida suka sami inna zaune a falo tana kallo wacce tana ganin su tace"Aa lafiya jim kad'an da fitar ku sae gashi har kun dawo?
Ryynt bata iya ce mata komai ba sbd kukan da take ji sosai tayi sauri ta shiga d'akin ta ta zauna gefen gado tare da fashewa da kuka.
Sae ga inna ta shigo d'akin ta zauna a kusa da ita ta dafa kanta tana fad'in subuhanalillahi lafiya Ryynt me yake faruwa?
Cikin kuka Ryynt ta shiga yiwa inna bayanin abinda ya faru tsakaninta da mohd.
Inna ta jinjina kae tace"cabd'i! lallai muhammadu ba d'an rainin wayo irin sa daga cewa zaku tafi wancan gidan shine zae d'auke ku ya tafi daku gidan sa a cewar kun koma knn ba tare da ya ko snr dani ba bare zancen shiri,kinga yi shiru daina kuka zae zo ya same ni shasha shan yaro marar kunya fitsararre ae gwanda da kika masa haka ina nn zae zo ya sameni sae naji in ubansa kabiru ne ya turo sa yayi hakan.
Tana kaiwa nn sae ga allawiya ta shigo d'akin da sallamar ta mohd ya aiko ta a cewar yana da magana da inna ,inna ta tashi tana fad'in shashasha dama nace ina nn zae zo ya sameni bari inje inji da wane shashan cin kuma yazo min dashi.
Ta fita bata ganshi a falo ba sae d'akinta ta same shi sae safa da marwa yake yaransa na ajiye gefe cikin keken su na turawa sae da inna ta zauna snn ya zauna suna fuskantar juna.
Cikin fad'a inna tace"shasha sha wane kuma shashancin ka zo min dashi ne iye fad'i ina jinka"
Mohd dake kallonta yace"haba inna ni gaskiya abinda Ryynt ta min sam banji dad'i ba amma kuma kinxo kina ganin laifina"
Inna ta dunqule yatsunta biyar ta watsa masa tace"ungo nn dan uwarka idan banga laifin ka ba laifin wa zan gani ne iye shashashà marar kunya ace yarinya yau yau da yin arba'in haka kawae zaka wani d'auke ta ka maida ba wani shiri ba tare da kuma ka sanar dani ba sbd ban isa da kai ba bani na haife ka ba koh!

Ni inna kinsan ba haka bane harakar al'ada d'in nn ne na zuwa yawon sallama gidajen mutane ne bazan iyaba shiyasa kawae ban sanar da ke ba.
Inna tace"yo lallai muhamnadu abu tun kakannin kakannin kace kae baka yarda dashi ba to bari kaji ba inda Ryynt zata koma sae taje tayi sallama da mutane kuma har qauyen su sae taje kaji in gaya ma.
Rae 6ace mohd yace"gaskiya inna ina buqatar matata ta koma bazan iya haquri har tayi wnn yawance yawance ba ta bari in taje can tayi"
Inna tace"dan uwarka a ina ka ta6a ganin anyi haka kuma da kace baka iya haqurin jiranta tayi wnn yawace yawacen ae duk dad'ewar dae ba zae wuce kwana uku ko hud'u ba idan anyi ququwa sati d'aya a cikin na biyu.......haba habà inna gaskiya ni bazan iyaba, na gaji da kad'aicin da nake d'auke dashi a bani matata kawae mu koma idan baso ake na shiga wani hali ba.
Inna tace"yo ka jima baka shiga wani halin ba shasha shan yaro marar kunya ba inda Ryynt zata je kumà maza fita a nn in daina ganin ka"
A fusace mohd ya tashi zae bar d'akin inna tace"wa kuma ka bar ma yaran naka ne iye?
Mohd ya juyo ya kalli yaransa snn ya kalleta cikin marairaice fuska yace"inna ya zanyi ne idan na tafi dasu bayan Ryynt bata can kuma kince bazata koma ba"
Tace"yo ae sae ka tambayi kanka daa da kace ta bar maka yaran ya kake tunanin zakayi dasu ne iye"
Shiru mohd yayi dan shi kansa yasan a lokacin zafin zuciya ne ya d'ebe sa ya kaisa ga cewa hakan.
Inna tace"kana jina kayi min shiru"
Yace"inna wnn zafin zuciya ne dmn bana da nufin zaluntar su na raba su da mahaifiyar su da ita kad'ai ce zata iya kula dasu yanda ya dace"
Inna tayi shiru tana kallon sa tace"matsalar ka knn muhammadu zafin zuciya abinda sam bayada anfani,yana da kyau mutum ya riqa tausasa zuciyar sa kafin ya fad'i magana dan kaga yanzu ba wata riba kuma sanin kanka ne yanda ka 6ata ran Ryynt ba lallai bane ta kar6i yaran nn kai tsaye sae kayi kamar kanayi.
Mohd yayi shiru kafin yake cewa"inna kiyi haquri dan Allah na barsu a hannun ki nasan idan kika lalla6a min ita zata haqura ta kar6e su dan yanzu nasan ni ko naje ba zata saurare ni ba"
Inna tace"Aa ni baxa ka bar min yaranka ba,ba kuma zanje na lallashi Ryynh ba kaje da kanka ae da zaka maida ta gidan ka bakayi shawara dani ba sae ma qarya da kamin sbd ka maida ni shasha sha"
Mohd yace"inna dan Allah kiyi haquri naji nayi kuskure zan kuma bi duk yanda kuke so koma yaushe ne zan haqura,kawae bana son fad'an da mukayi da ita ya shafi yarana dan Allah inna kije ki rarrasheta.
Inna ta nisa snn tace"naji zanje na rarrashe ta d'in"
Mohd ya mata godiya snn ya fita a cewar zae tafi ya dawo.
Inna tayi zaune shiru dan sae duk taji mohd ya bata tausayi amma bata jin zata iya bashi Ryynt su koma yau d'in nn dan ko ba komai tana son qara gyara ta da kyau.
Nan ta tashi ta nufi d'akin Ryynt dmn rarrashinta.
Chapter 108 · 0% Book details