← Book details Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 112

Sashe 76

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

🔮🔮🔮🔮
*```Page 70```*
Washe gari mohd ne ya tashi daga bacci ya kalli Ryynt dake kwance kusa dashi tana bacci yakai hannu ya yaye farin handkerchief d'inda ke kan goshin ta ya d'aura tafin hannun sa akai yaji still akwai zafi a goshin nata,ya lumshe ido cike da damuwa yana tunanin dole sae ya mata allura knn dan jiya cikin dare sosai ciwon kan ya dame ta sae kuka take ta kasa bacci har sae da ya koma bata magani ya kuma yi zaune da farin handkerchief d'in sa yana tsomawa a ruwa idan ya matse snn ya d'aura mata kan goshinta yana rage mata zafin kan har ya samu tayi bacci.
Jiki sanyaye ya sauka kan gadon yana mae kallonta snn ya nufi bathroom koda ya fito ya same ta zaune kan bed ta had'e kai da guiwa yaje ya zauna gab da ita ya d'ago kanta ya ta6a goshinta yana kallon fuskarta yace"har yanzu kan bae daina maki ciwo ba ko"
Cikin sanyin murya tace"um um ya daina min"
Ya sauke ajiyar zuciya yace"to ya naji jikin naki da zafi ko wani abu ke maki ciwo ne?
Ta girgiza kanta tace"ba komai"
To muje na kai ki bathroom kiyi arwala ko,
Ta kalle sa tace"zan iya zuwa da kaina"
Nan ya barta ta tashi sae kallon ta yake har ta shige bathroom snn ya tashi ya fita.
Koda ya dawo ta idar da sallah tana kwance kan darduma tana bacci yaje a hnkli ya cire mata hijab ya maida ta kan bed.

Sae guraren qarfe goma ta tashi koshi wayar da man keyi ne ya tashe ta,
Ya katse wayar ya kalli Ryynt da ta tashi zaune cikin jin bacci yace"sorry Ryynt na tashe ki ko"
Bata ce komai ba sae sauka taje zuwa yi kan gadon da sauri, ya riqo ta yace"amae"
Ta sadda kanta qasa cikin jin kunya tace"Aa zanyi fitsari ne"
Yace"to jeki"
Nan ta tashi ta wuce bathroom bayan tayi fitsari ta cire tufafin jikinta tayi wanka ta jawo towel ta d'aura taxo tayi tsaye riqe da kayan da ta cire a hannunta ta kasa fitowa sbd hijab d'inda bata tare dashi.
Tana tsaye kusan minti biyar taji an turo qofar bathroom d'in sukayi ido hud'u da man tayi saurin sadda kanta qasa shi kuma yayi murmushi had'e da kar6ar kayan da ke hannunta yace"me kike so ne da kika kasa fitowa?
Ba tare da ta d'ago ta kalle sa ba tace"hijab nake so"
Ba musu ya juya yaje ya d'auko mata hijabin ya kawo mata ta saka hijabin snn ta fito shi kuma ya fita ya bar mata d'akin domin ta shirya.

Sae da ya tabbatar ta kammala shiri snn ya dawo ya sameta riqe da wayarta a hannunta tana neman gurin saka caji ya kar6i wayar yaje ya saka mata caji snn yaja hannun ta zuwa kan dining ya ja mata kujera ya zaunar da ita snn shima ya zauna kusa da kujerar da take zaune ya zuba musu abinci a plate da'ya wato arish, plantain da kuma soyayyen qwai sae ruwan zafin tea da man ya zuba a cups ya had'a musu snn ya kalli Ryynt da kallon sa kawae take yana aikin.
Ya d'ebo arish a fork spoon zae kai bakinta ta kalle sa had'e da kar6ar fork d'in ta shiga ciyadda kanta shima ya shiga ci sae yi yake yana kallonta sbd yaji dad'in ganin bata ji amae ba don tun lokacinda ya bud'e kula yake ta Allah Allah kar tace zatayi amae.

Bayan sun kammala cin abincin ne sae ga matar Amir ta shigo gaida Ryynt da jiki a nn Ryynt ke tambayar ta sadiq tace wlh sun fita shida Abban shi nn suka zauna shiru sae jefi jefi suke magana sbd ba wani sabawa akayi da juna ba man kuwa tun lokacinda ta shigo suka gaisa ya fita ya basu guri wanda ya jima kafin yake dawowa ya samu matar Amir tuni ta koma 6angaren su sae Ryynt kad'ai ya samu kan bed kwance lamo kamar mai bacci yaje gab da ita ya durqusa ta d'ago ido ta kalle sa kmr zata yi kuka dan duk ta soma jin kanta a kad'ai ci.
A hnkli ya shafo gefen fuskarta yace"mene ne?
Cikin yanayin kukan da take d'auke da shi ta janye hannun sa dake kan fuskarta tace"ni ka kira min inna"
Sae da ya tada ta zaune snn ya ciro wayar sa a aljihu ya kira mata inna ,ya miqa mata wayar ta kar6i wayar da hanzarinta ta kara wayar a kunenn ta cikin amsa sallama dan lokacin har inna ta d'auka.
Washe da baki inna tace"Ryynh kece"
Ryynt tace"eh inna ina wuni"
Tace"lfy lau Ryynh ai ni duk kun tashi hankali na ko na kira ba'a samun wayar ko d'ayanku sae ata min wani banzan turanci can "
Ryynt tace"eh inna ni wayata ba caji a kashe take"
Inna tace"ayyo haka kuwa nasiru ya gaya min cewa wayoyin naku duk a kashe suke wae lokacinda na kira baku sauka a jirgi ba amma yayi waya da Amir bayan saukar ku yace masa kun isa lafiya har ma kuna masauki,
inace kuna zaune qalau dae ko"
Ryynt tace"eh inna"
Inna tace"to ya nake jin muryar ki kmr marar lafiya"
Sae da ta kalli man ta gefen ido snn tace"lafiya ta qalau inna ba komai"
Inna tace"to muhammadu fa"
Ryynt tace"gashi"had'e da miqa masa wayar ya kar6a d'auke da murmushi ya kara wayar a kunnen sa suka gaisa daga haka ya soma yin dariya yana ta ba inna haquri,Ryynt sae kallon sa take dan kmr bata ta6a ganin dariyar sa ba sae yau.
Yana gama wayar ne ya kalleta d'auke da sauran dariyar da ke kan fuskar sa yace"wae kinji inna sae fad'a take ta min wae ban kirata nace mun iso lafiya ba shine nake bata haquri"
Ryynt dae bata ce komai ba sae d'an murmushi da tayi a fuskarta man dake kallonta d'auke da nashi murmushi ya tashi yaje ya d'auko wayarta da ya saka mata caji ya saka mata sabon layin da ya siyo mata ya bata wanda ya cire yace"ki ajiye wnn sae idan mun koma zaki ci gaba da aiki dashi,
a nn kuma wanda na saka miki d'in nn ynx shi zaki riqa amfani dashi kinji"

Ta gyad'a masa kai had'e da kar6ar wayarta da ya bata koda ta duba har copying numbers yayi mata don duk ta sami numbobinta a ciki.
Sai da ya d'an fita snn ta kira umman saliha wacce tana ganin numbar waje ta san cewa Ryynt ce tana d'aga wyr kuwa taji muryar Ryynt nn suka gaisa fuskar kowannen su d'auke da murmushi sae waya suke lokaci mai tsayo cike da nishad'i dan har saliha da mami duk sae da tayi waya dasu ai kuwa duk wani kad'ai cin da ta soma ji taji ya tafi.

Da yamma man ne cikin shirin sa zai fita sbd wasu kayan amfani da yake son siyo musu yayiwa Ryynt sallama ya kama hanya zae fita har yakai hannu zae bud'e qofa sae kuma ya juyo,
Ryynt dake kallon sa tayi saurin sadda kanta qasa yazo gab da ita ya d'ago fuskarta yana kallon manyan idanuwanta da suka ciko da qwalla yace"mene ne ko kina zuwa muje?
Da sauri ta gyad'a masa kai, yaje ya d'auko mata hijab ya saka mata da kanshi yaja hannunta suka fita.

Kan hanya Ryynt sae kallon gurare take tayi da suka mugun bata sha'awa har suka isa wani makeken mall,
nn fa ta shiga ba ido haqqinsa don gurin ya had'u iya had'uwa kmr wata aljannar duniya yayinda man ke janye da ita yana musu siyayya ya tafi da ita gurin rigunan bacci ya ciro kusan kala biyar masu shegen kyau da baza su wuce iya cinya ba ita dae Ryynt sau d'aya ta kalli kayan ta kauda fuskarta dan jin tayi kmr ta nitse don kunya dan taga tsiraicin kayan sosai wacce duk a tunanin ta malika ya siyawa dan ita taga tana saka irin su.
Bayan sun dawo gida har anyi sllr magrib da isha'i Ryynt na kwance kan darduma lumshe da ido tana jin bacci mae dad'i na son fizgarta,
bata ji shigowar man ba sae qamshin turaren sa da taji gab da ita nn ta bud'e idanunta a hnkli ta ware su akanshi ya dafa goshinta tare da fad'in"jikin ne?
Tace"um um bacci nake ji"
Yace"to muje muci abinci sae ayi wanka koh?
Ba musu ta tashi suka je kan dining sae dae bata wani ci abincin sosai ba sbd baccin da ya mata yawa a ido ta ture plate d'in gabanta zata tashi man ya riqo ta yace"ba dae amae ba?
Kallon sa tayi snn tace"um um wanka zanyi nayi bacci"
Yace"indae wanka ne zan miki zauna ki qarasa cin abincin ki tukun"
Tace"um um ya ishe ni fa"
Yace"yi haquri dae ki qara ko kad'an ne kinji"
Ta girgiza kanta alamar a'a bae kula ta ba sae jawo plate d'inta da ta ture yayi zae ci gaba da ciyadda ita,cikin yanayin jin bacci d'auke da shagwa6a ta fashe mai da kuka,
da sauri ya ture plate d'in yace"yi haquri muje ayi wankan to"
Tace"um um nida kaina zanyi"
Yace"to tashi kije ki cire kayan jikin ki kafin na had'a maki ruwan wanka"
Nan ta tashi taje zuwa cire kaya shi kuma ya nufi bathroom ya had'a mata ruwan d'umi ya fito snn taje ta shiga.

Koda ta fito ta samu ya ajiye mata d'aya daga cikin rigunan baccin da taga ya siyo ai kuwa ta zaro ido tana kallon rigar snn tayi murmushin mamaki wae ita ya siyo ma kayan knn ashe kuwa zasu tabbata ba'a sa ba.
Nan ta wuce abinta ta bar rigar taje ta ciro turarukkan da umman saliha ta bata ta shafa.
Bayan ta gama shafa turarukkan ne ta bud'e wardrobe ta nemi kayan baccin ta sama da qasa bata gansu ba nn tasan cewa mohd ne ya d'auke su don kawae tasa waccan rigar da ya ajiye mata.
Rai 6ace cikin kukan shagwa6a taje tayi kwanciyar ta kan bed ta soma yin baccinta sanye da hijab da towel d'in da ta fito wanka dasu.
Chapter 76 · 0% Book details