← Book details Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 112

Sashe 69

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

🔮🔮🔮🔮
*```Page 65```*
Bai iya ci gaba da tsayuwa ba sae jin yayi ya zube qasa kan guiwoyin sa yana ci gaba da kallon kud'in yayinda idanuwansa suka kad'a zama d'aya sukayi jajur snn bakinsa ya shiga rawa kmr zai ce wani abu amma ya kasa sae kansa da ya dafe had'e da rufe idanun sa yana mai tuna komai sak yanda ya faru.
Nan kowa yayo kansa yana tambayar Aamil lafiya me yake faruwa,
kuka ya fashe dashi sosai ,
ya bud'e ido yana kallon Abba dake gaban sa dafe dashi riqe da kud'in da abin hannun da Ryynt ta bashi a nn ya rumtse idon sa da sauri dan ko kad'an baya son ganin kayan.
Abba ya ajiye abubuwan da sauri yana tambayar lafiya Aamil wani abu ya sami idanun naka ne?
Bud'e idanuwan nasa yayi yana kallon Abba cikin kuka yace"Abba nine wlh ba mohd bane nine Abba.......kaine me Aamil?
Cikin rawar murya Aamil yace"Abba nine na kashewa Ryynt Baffanta!
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!!!
shine abinda kowa ya shiga fad'i ba adadi akasin Ryynt da komai ta kasa cewa sae ja baya tayi da qarfi tana kallon Aamil d'auke da hawayen da suka zubo mata kai tsaye kmr yanda shima yake kallonta da nashi hawaye akan fuskar sa.
Nan kawai ta fashe da kuka ta tafi da gudu zuwa d'aki man ya tashi da sauri ya bita sae dai bai iya shiga d'akin ba sae jikin qofar ya tsaya sbd tasa makulli ta rufe d'akin amma ana jiyo tsaf sautin kukanta sbd a nn jikin qofar ta zame tana kuka.
Aamil ne yazo ya sami man tsaye a bakin qofar ya gurfana kan guiwoyin sa ya rungume qafafuwan man cikin kuka yace"i beg u yhu ka bata haquri wlh ba a kan hnkli na nayi kisan ba qaddara ce......
Abba ne yazo a fusace ya tada shi tsaye ya kifa masa wawan mari yace"wace irin qaddara ce wnn Aamil ko ka fara shaye shaye ne ban sani ba!
Aamil yayi shiru dmn tabbas ba zai ta6a mantawa ba yafi to daga gurin shaye shayen sa ya kad'e Baffan Ryynt.
Abba ya daka mai tsawa yace "dan uwarka gaya min garin ya ka kashe mata mahaifi kuma akan wane dalili!
Aamil yace"Abba qaddara ce wlh ba nayi kisan da niya bane asalima ban san cewa ya mutu ba"
Kaga bashi nake son ji ba ka gaya min ta yaya akayi har ka kashe mata mahaifi?
Ba musu Aamil ya gayawa Abba komai yanda abin ya faru ba tare da ya 6oye masa komai ba har magagin giyar da yake ciki kuwa duk sae da ya gaya mae.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un shine abinda Abba ke ta furtawa, yayinda ya cire hular kanshi yana fifita ta a jikin sa sbd wani irin zafin bala'i da gumi dake tsastsafo mai ta koina a jikin sa had'e da wani irin ciwo da yake ji ta 6angaren zuciyarsa,
ya dafe gurin da sauri yaje zuwa fad'uwa Nasir da man sukayi hanzarin tarbarsa inda a rud'e suka tafi dashi kan doguwar kujera suka kwantar ,
inna ta tafi cikin rud'u da firgici ta bud'e fridge ta ciro ruwa ta kawo musu suka yayyafa masa.
Amma bai farfad'o ba sae d'aukar sa sukayi zuwa asibiti yayinda man da Amir ne ke kansa har suka samu ya farfad'o suka mai allurai ciki har da ta bacci.
Koda suka fito suka sami inna sae kuka take tana fmn sirfawa Aamil zagi yayinda Nasir ke gefen ta yana ta fmn lallashi wacce tana ganin su Amir sun fito ta nufe su tana tambayar halin da Abba ke ciki nn suka nuna mata ba wata matsala bace dan har ma ya farfad'o sun mai allurar bacci,
a nn ta nemi ta ganshi basu hanata ba suka barta ta shiga tare da Nasir yayinda su ma suka juya zasu bi bayansu sae ga hjyr su da man ya kira tazo cikin rud'u tana tambayar sa abinda ya faru da Abban su,
Man yayi shiru kawae yana kallonta ya kasa ce mata komai sae Amir ne ya bud'e baki yace"umma muje dae kiga Abba tukun"
Bata musa musu ba tabi bayan su suka shiga dan dama ta matsu taje ta ganshi.
Ta sami Nasir ya jawo wa inna kujera ta zauna nn gefen gadon da Abba ke kwance akai.
Ta qarasa ciki tare da gaida inna yayinda ita kuma nasir ya gaida ta ta amsa tana mai kallon Abba dake kwance yana bacci ,
ta sauke numfashi tana ci gaba da kallon sa snn ta kalli su man tace"na tambaye ku tun a waje me yake damun sa baku gaya min ba sae cewa kukayi na shigo na ganshi"
Amir ne ya sadda kansa qasa cikin jimamin baqin cikin abinda zae snr da ita ya d'ago had'e da share er qwallar baqin cikin da ta fito masa ta gefen ido snn ya shiga snr da ita lbrn komai abinda ya faru cikin nuna baqin ciki da damuwa"
Yana gama bata labarin ne kafin tace komai sae Aamil ta hango tsaye a bakin qofar d'akin yazo gab da ita ya durqusa a gabanta d'auke da idanuwan sa da sukayi jajur kan kuka,ita kuwa sae kallon sa take cikin mugun 6acin rae yace"umma ki yafe min,a yau nayi babbar nadamar qin daina abinda kika hana ni wato shan giya da ke kad'ai kika sani sae kuma Amir,kuma kunyi iya bakin qoqarin ku na ganin na daina amma sae na kasa har takai ga na aikata babbar 6arna,wacce tun daga rnr wlh ban sake yarda nasha giya ba umma duk da cewa ban san nayi kisa ba amma ko kad'an banji dad'in abinda ya faru ba a lokacinda hnkli na ya dawo gare ni wanda tun daga rnr nake fmn istigifari a gurin ubangiji na ina neman yafiya a gurin shi,dmn dama tun farko bada niya na fara ba sharrin frnds ne da kuma sharrin shaid'an da har ta kai ga na aikata abinda har mutuwa ta ba zae ta6a kankaruwa ba.
Ya qarasa maganar ne cikin muryar kuka mai qunshe da baqin ciki,
umma kuwa sae kuka ta fashe dashi tace"lallai Aamil ka riga ka cuci rayuwar ka tun farko sae da na gaya maka wnn banzar tabi'ar sam bata dace dakai ba ka daina ta amma kaqi yanzu gashi ka aikata abinda har mu mutuwar mu baza mu manta ba ,ka 6ata mana suna ka wulaqanta mutuncin gidan ku da kaf dangi ma baki d'aya,
shashasha kawae fita a nn in daina ganin ka!

Hawaye ne suka sailalo a hknli kan kumatun sa snn ya kama hanya ya fita d'akin jiki sanyaye.
Nan man ya kama hanya zai fita d'akin, umma ta takadar dashi ta hnyr cewa "ba dai bin Aamil d'in zakayi ba"
man ya girgiza kansa yana kallon ta sbd shi ba inda zae je ba knn gun Ryynt yake son ya tafi.
Bata ce dashi komai ba sae Abba ta kalla da ya soma tari wanda ya bud'e idonsa a hnkli had'e da tashi zaune ,
umma ta qarasa gurin sa tana mai sannu haka ma inna da su Amir duk suka mae sannu yayinda Man yaje ya kawo masa ruwa had'e da masa sannu Abba ya kar6i ruwan yasha.
Bayan ya gama shan ruwan ne ya kalli man yace"Ryynt fa?
A hnkli man ya sadda kansa qasa yace"tana gida"
Nan Abba ya maida duban sa gun nasir yace"je ka zo min da ita"
Nasir yace"to"snn ya fita d'akin wanda ya d'an jima kafin yake dawowa suka shigo d'akin shida Ryynt wacce kallo d'aya zakayi mata kasan taci kuka har na fita rai don duk idanunta sun kumbura sunyi jajur tayi tsaye kawae a bakin qofa kanta qasa ta kasa kallon kowa.
Abba dake kallonta yace"qaraso daga ciki Ryynt"
Cikin tako mai natsuwa ta qarasa gurin Abba wanda ya kalleta da kulawa yace"Ryynt ko kad'an banji dad'in abinda kikayi niyya ba amma kuma banga laifin ki ba dmn babban mai laifi shine Aamil da duk shine yayi silar haddasa faruwar komai ,
ya haddasa miki baqin ciki da quncin rayuwar da kika shiga a matsayin ki na er qaramar yarinya da har yasa kika yi tunanin abinda bai dace dake ba,da hk nake son kiyi haquri ki ajiye wnn tunanin ki bar komai a hannu na dmn nida kaina zan sa a kama Aamil a kuma yanke masa hukunci dae dai dashi ta yanda duk wani mai banzar tabi'a irin tasa bazai ta6a sha'awar aikata abinda ya aikata ba.
Girgiza kanta tayi had'e da share qwallar da suka zubo mata tace"Abba ka barshi,
dama duk a tunani da gayya yayi kisan shiyasa na d'auki wnn alqawarin wanda na d'auki
alqawarin ne cikin baqin ciki da jin zafin yanda aka kad'e Baffana da kuma sanin cewa ko na kai qara a hukuma ba lallai bane abi min haqqina a wnn lokacin kasancewar mu talakawa en qauye da ba'a d'auke mu a bakin komai ba shiyasa amma ni ynx na yafe masa Abba"
Abba ya girgiza kansa yace"ai ba ubanda ya ake sa shan giyar dn hk sae na nuna masa kuskuren sa ta yanda zaiyi babbar nadamar fara shan giya a rayuwar sa"
Ryynt ta sake share qwallar da suka zubo mata tana tunanin hallaci irin nasu tace"Abba dsgke na yafe masa kawai ka barshi"

Abba yace" ko d'aya Ryynt ke yarinya ce mai kirki da mutunci da ya zama dole abi maki haqqin ki kan zaluntar da ya miki,dmn ya zalunce ki mafi zalunta .
Inna ta kama masa sae masifa ita ma take kan lallai fa sae an hukunta shi tun da shi yajawa kansa ba wanda yaja masa.
Ryynt tayi shiru kawai tana sauraren su sae hawaye dake fmn sauka kan fuskarta yayinda taji har ranta mutanen sun qara shiga ranta wad'anda had'i da hallacin da suka mata ne yasa taji ta yafewa Aamil dmn sun cancanci fiye da haka a gurinta sae dai kunyar su da kuma tsanar Aamil da zata zauna a ranta bazata bar ta iya ci gaba da zama tare dasu ba shiyasa ta shiga tunanin suna komawa gida tafiyar ta kawae zatayi ba tare da kowa ya sani ba.
Chapter 69 · 0% Book details