← Book details Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 112

Sashe 48

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

8:30pm
Inna ce zaune a falo ita da Rynt suna cin abinci bayan sun gama Rynt tace"inna nifa gobe bana da kayan sawa idan zanje makaranta duk suna gidan can"
Inna tace"ayyo ai tuni an kwaso maki kayanki suna a d'akin ki nasa nasiru yakai ,
ai a cikin kayan ne ma na d'ebo wasu en kyn sawa nakai miki a d'akina"
Tace"inna kayan mami fa?
Tace"yo ai kaji fa amma bari na kira nasiru naji da yaje kwaso maki kaya har da kayan mami ya kwaso ya had'o ko kuwa"
Nan ta d'auki wayarta ta kira nasir bayan sun gama wyr ne tace ma Rynt yace duka har kyn mami d'in ya had'o ya kwaso wanda tun d'azun yaso yazo ya d'auki kayn nata yakai gida sae bae sami lokaci ba amma yace yanzu zai zo ya d'auki kayan"
Rynt tace"to bari naje na had'a masa kayan kafin ya iso"
Inna tace"to"
Snn Rynt ta tashi ta nufi d'akinta da take zama a daa.
Kan gado ta sami kayan nasu komai har akwatinan lefenta wad'anda kallo d'aya ta musu ta kauda idonta ta d'auki akwatin mami ta bud'e taga komai nata na ciki ta rufe akwatin ta ajiye ta gefe kusa da qofar d'akin snn taje ta bud'e akwatin ta wacce inna ta saya mata ta samu itama komai nata na ciki zata rufe kenan akwatin ta sa6ule ta fad'i sae duk kayan suka fita nn ta hango tsofuwar ajiyar ta ,ta kai hannu a hnkli ta d'auki viva ledar ta bud'e .
Kayan da marigayi anwar ya bata ne a ciki nn ta shiga ciro kayan d'ai d'ai tana kallo.
Hawayenda suka cika mata ido ne suka shiga gangarowa a hankali yayinda ta ciro bandir d'in 1k guda biyu masu d'auke da jini a jikin su nn taji inna ta qwala mata kira tayi saurin mayarda kud'in har kynda anwar ya bata snn ta amsa kiran da inna ke mata had'e da share hawaye ta kama hanya zata fita sae ga nasir ya shigo d'akin yace"har kin gama had'a kayan?
tace"na samu kayan a had'e suke"
Yace "eh hkne ni na had'a kyn tun can sbd a wardrobe d'inta na sami akwatin ta shine na saka mata duk kayan da ke cikin wardrobe d'in haka kema"
Tace"mungode"
Snn yace"zancen da mukayi jiya dake ban manta ba ina son sae na sami lokaci ne sae nazo muje a cire cikin ko?
Tace"to"
Yace"yauwa sae ki maida hnkli ki ci gaba da zuwa mkrnta kinji"
Nn ta gyad'a mishi kae shi kuma yaja akwatin mami ya fita.
Ita kuma taje ta gyra kayan akwatinta da suka zube ta rufe sae dae kafin ta rufe akwatin sae da ta cire kynta na zuwa school ta d'auke su ta tafi dasu d'akin inna.

12:00 na dare
Man ne ya fito d'akin shi wanda bai zarce koina ba sae d'akin Rynt .
A nn bakin qofa yayi tsaye yana qarewa d'akin kallo sae can ya qarasa shiga d'akin yaje gun wardrobes ya bud'e yaga ba komai kaf an kwashe ya maida wardrobes d'in ya rufe .
Har zai fita sae ya hango farar suit jacket d'inshi kan sofa yaje ya d'auki jacket d'in a hnkli yana kallo,
Se kuma yayi saurin kauda idonsa kan jacket d'in ya kuma jefar da ita kan sofa ya fita.

Washe gari da safe Rynt ce ta kammala shirinta tsaf na school inna ta ciro d'ari biyar ta bata Rynt ta kar6i kud'in tace"ba canji ne inna?
Inna tace"canjin me kud'in ki ne fa da zaki tafi dasu makaranta na cin abinci ko basa isar ki?
Rynt ta bud'e ido tace"inna ai kud'in sunyi yawa ai d'ari biyu ma sun isa kuma ina ma da kud'i a hannu na da kin barshi kawae inna"
Inna tace"yo Rynh kud'in hannunki ai naki ne,wad'an nn kuma na cin abincin mkrntr ki ne kabiru ya bayar a riqa baki"
Tace"to inna nagode amma dae zan dawo da sauran canji dan sun min yawa"
Inna tace"to er albarka a dawo lafiya Allah tsare min ke ya kuma bada sa'ar karatu"
Tace"amin inna"snn ta fita ta samu driver na jiranta a qofar gida taje ta shiga motar yaja suka tafi.

Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[10:00PM, 5/2/2017] Billy giro😊: ```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```

🔮🔮🔮🔮
*page* *```49```*
Ana sauke Rynt a school sae kawai taji ihun mami tazo aguje ta rungumeta.
cike da murmushi Rynt ke kallonta tace"mami kece waya ya kawo ki?
Washe da baki tace"Abbana ne yanzu ya wuce"
Sae kuma tasha toka tare da fad'in"Anti wae meyasa kika koma gidan inna da zama?
Rynt tayi shiru tana kallonta can tace"to ai dama can gidan inna nake zama ko kin manta"
Tace"Aa ni nafi son ki koma gidan yaya sbd na fi son a riqa kawo mu school tare"
Rynt tace"ai ko ba'a kawo mu tare ba, ba gashi muna had'uwa ba"
Turo baki tayi tace"um um anti hk ba dad'i"
Rynt tace"kinga jeki 6angaren ku za'a fara assembly kar kiyi letti kinji"
Mami tace"to Anti gsky ni sae kin gaya min yaushe zamu koma gidan yaya"
Rynt tace"to kisa ido duk rnr da kika ga raqumi ya shiga akurki kizo da gudu ki gaya min sae mu koma ko"
Da murna mami tace"dgske anti!
Rynt tace"eh"
Mami tace"meye ma raqumi wnn abun mae girma kmr doki ko"
Rynt tace"eh"
Mami ta daka tsalle tace"Allah kuwa da jimawa na ta6a ganin shi hnyar kasuwa,gobe ma zan cewa umma muje kasuwa da na ganshi zanyi ta kallon shi har sae naga ya shiga akurki sae nazo har gidan inna na gaya miki,sae mu koma abin mu gobe gidan yaya ko.
Rynt tayi murmushi had'e da girgiza kanta ta tafi tana fad'in"to naji zan neme ki a break"
Tace"ok anti bye"

5:00pm
Rynt ce ta dawo daga mkrnta ta sami inna a falo duk ta raja'a gun kallo har sallama tayi kusan sau biyu amma bata ji ba, tayi tsaye d'auke da murmushi tana kallon inna snn taje a hnkli kan jikin inna ta rungumeta,
a tsorace inna ta juyo ganin Rynt ce ta sauke numfashi tace"yo Rynh kece aini har kinsa na tashi guduwa ,
Rynt tace"haba dae inna da tsufanki kk shirin guduwa?inna tace"yo ai shi tsoro ba ruwan shi da tsufa "
Dariya Rynt tayi tace"hln ma meya tsorota ki ne inna?
Tace"yo Rynh ina zaune qalau kawae naji an hau kan jikina bayan nsn ni kad'ai ce a falon ban kuma ji shigowarki ba
Tace"to inna ai nayi sallama har sau biyu kece dae bakiji ba sae kallo kike tayi abinki"
Inna tace"ayyo inafa zanji na maida hnkli gun shiriritar banzar nn da ba zata fisshe ni ba"
Murmushi kawae Rynt tayi ta tashi tare da fad'in "inna ni zanje na d'an watsa ruwa"
Tace"to er Albarka sae kin fito"
Nan Rynt ta wuce inna kuwa taci gaba da kallo.

Tana gama wanka ta shirya ta ciro wata baqar leda a cikin jakarta ta mkrnta ta fito ta tafi kitchen sae gata ta dawo d'auke da agwalima cikin bowl.
Taje ta zauna qasa kusa da kujerar da inna ke zaune akai ta d'auki d'aya zata fara sha tare da fad'in" inna ga agwalima"
Inna tace"yo Rnynh ni na d'auka ko abinci ne kika d'ebo"
Tace"Uhm agwalima ce na wanko na d'an sha ko d'aya ce sae naci abinci "
Inna tace"lallai kam ki hanzarta kici abinci kafin mai miki dasarin yazo"
Tace"inna ni idan ma da fura ita kawae zansha ba sae naci abinci ba dan bana jin yunwa"
Tace"to tashi kije ki d'ebo furar tana can a cikin firijin tayi sanyi kuwa.
Ba musu Rynt ta tashi ta d'ebo furar tazo tayi zaune ta shanye agwalimar hannunta snn tasha fura tana gamawa taje ta had'o komai nata na lesson ta fito ta samu inna na kar6a sallama inna na ganinta tace yauwa je d'auko tabarma don inaga mae miki dasarin ne yazo,nn Rynt ta koma d'aki ta d'auko tabarma ta fita.

6angaren mohd kuwa kwance yake a falo shi kad'ai kan 3 seater ya lumshe ido kmr mae bacci.
Da damuwa ya bud'e idonsa had'e da guntun tsaki sbd door bell d'inda yaji ana fmn dannawa kan dole ya tashi yaje ya bud'e qofa, ganin wanda ke tsaye yasa ya d'an saki fuskar shi ya bashi hannu suka gaisa har yana masa ya hanya.
Wanda ba kowa bane face lesson teacher d'in su Rynt wanda tun lokacinda yayi tafiya sae yau ne ya dawo.
Man bai iya bashi hanya ba sae nazarin abinda zai ce masa yake can ya kallesa yace"kayi hqr fa yaran basa nn sunyi tafiya"
Lesson teacher yace"to shikenn amma yaushe ne zasu dawo?
Shiru man yayi can yace"ka tafi kawae dae"
Ba musu lesson teacher d'in yayi sallama dashi ya wuce.
Man ya rufe qofar ya juya ya sami malika a tsaye tace"my man waye ne?
Yace" Lesson teacher ne
Tace"au shi baisan matsiyaciyar tayiwa kanta tsiya ba"
Komai bai ce da ita ba sae zama yayi ya jingina bayansa tare da lumshe idonsa .
Nn taje ta zauna kusa dashi tare da kwanciya kan qirjinsa yace "pls malika im nt in mood n i just wnt me alone ki tafi d'akin ki kinji "
Zata ce wani abu knn yace"pls just go"
Jiki sanyaye ta tashi ta tafi zuwa d'akinta,haka shima ya tashi ya bar falon ya tafi d'akin shi.

2 dayz later
haka mohd ya cigaba da rashin son damuwa komai qanqantar ta kuwa shiyasa ko yaushe yafi son ya kasance shi kad'ai wanda ko asibiti yaje baya wani jimawa yake dawowa.
Chapter 48 · 0% Book details