← Book details Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 112

Sashe 64

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da yamma sae ga su sun dawo kamar yanda suka tsara man ya tsaya a qofar gidan shi kuma Amir ya shiga daga ciki.
Bai wani jima ba sae gashi ya dawo jiki sanyaye,
mohd yayi saurin qarasawa gurin sa yace"ya akayi ne?
Amir yace"Rynt d'in bata da lafiya"
A rud'e man yace "me yake damunta ne?
Amai take tayi sosai kuma byn ya tsaya mata sae fmn yunqurin aman take baya zowa duk ta wahala sae kuka take.
Cikin damuwa sosai mohd ya dafa Amir yace"Amir dan Allah muje na ganta"
Amir yace"ka ganta fa kace?
Eh mana Amir to so kake tayi ta fmn wahala ne baka tsaya ka duba ta ba ka wani zo kana gaya min .
Calm down laulayi ne fa ka sani baya da magani,
Don baya da magani sae a bar yarinya tana wahala gsky ni shiga zanyi koma me zai faru sae dae ya faru! yana gama fad'ar hkn ya tafi fuuu! zai shiga gidan.....
Amir ya riqe sa yace"kaga dakata ai ba wae haka kawae za'a barta ba inna tace idan tasha agwalima abun zai mata sauqi so agwalimar ce aka rasa bcs babu ita a gidn kuma ta kirà nasir ta snr dashi bata same sa ba.
Ni kuma ba sanin inda ake saeda agwalimar nayi ba shiyasa na fito dmn na snr da kai.
Man yace" kaga yi sauri da Allah shiga mota muje koma a ina ne ai ma samota.
Nan suka shiga mota mohd yaja suka tafi sae bin gari suke guraren da ake sae da fruits amma basu samu ba sae can kan hanya suka had'u da mai agwalima man ya tsaida mota suka fito sae gun mai agwalima,
Man yace"malam nawa gabad'aya agwalimar taka take ne "
Da sauri Amir ya kalli man yace"kai kana haukane muda baza mu wuce siyen ta d'ari biyu ko uku ba kake zancen gabad'aya ai sae ta lalace bata kai ga shanye ta ba ma"
Mohd yace"taya zata lalace bayan a fridge za'a zuba kaga malam juye min agwalimar ka kaf a leda ka fad'i kud'in ka na baka"
Dariya Amir yayi yace"haba man aikin hnkli dae"
Snn yace da mai agwalima"malam yi hqr sa mana ta d'ari biyar kawae ta isa"
Nan mai Agwalima ya shiga qirga agwalima yana sakawa a leda yayinda man ya kalli Amir cike da niyar magana Amir ya riga sa da cewa"kar fa ka manta tana can tana fmn yunqurin amai idan muka qara 6ata lokacin mu a nn zata wahala da yawa ne"
Nan man ya fasa maganar da yayi niyya ya maida duban sa gun mai agwalima da ya gama saka ta d'ari biyar a leda ya bawa man ya kar6a yayinda Amir ya ciro dubu d'aya a aljihu ya bawa mae agwalima yace ya riqe canjin kawae,
nn mai agwalima ya washe baki yana musu godiya su kuma suka shiga mota suka bar gurin sae gidan inna.
Wanda da isar su Amir ya fito da sauri riqe da ledar agwalimar ya shiga gidan.
Kusan minti goma da shigar sa ne ya fito ya sami man sae kai komo yake a qofar gidan yana ganin Amir yace"ya ake ciki ne ta daina yunqurin aman? Eh har ma ta shiga bathroom zata d'an watsa ruwa"
A nn man ya fitar da ajiyar zuciya yace"olryt amma dae zamu dawo anjima don na samu naga yanda jikin nata yayi ko"
Amir yace"shikenan Allah kaimu".
Daga haka suka shiga mota suka bar layin.

Ana fitowa masallaci sallr isha'i sae gasu sun dawo gidan ,Amir ne ya shiga wanda bayan en mintina kad'an da shigar sa gidan ne man yaga flash d'insa a nn ya shiga gidan ya nufi d'akin Ryynt kai tsaye ya sameta kwance kan darduma ta idar da sallah idanunta a rufe kmr mae bacci.
Nn yaje ya durqusa gab da ita tare da d'aura hannun sa a kan gefen fuskarta,ta bud'e idonta a tsorace tare da saurin tashi zaune tana kallon shi ya sake mata d'an guntun murmushi ita kuwa lokaci d'aya tasha masa toka dan ta fhmci mohd ne sbd qamshin turaren sa da taji.
Fuskar ta a murtuqe ta miqe zata bar d'akin mohd ya jawota zuwa jikin sa bata yi yunqurin qwatar kanta ba sae goshin ta da tayi saurin kai hannu ta dafe sbd kanta da taji yayi mugun sara mata.
Cikin damuwa mohd ke kallonta dan ya fhmci irin ciwon kan da take d'auke dashi nn ya tafi da ita kan bed suka zauna ya kwantar da kanta a qirjin sa had'e da kai hannu yana murza mata goshin nata a hnkli, Rynt kuwa se hancinta ta shiga cusawa a hnkli cikin rigar sa sbd wani irin qamshin dad'i da taji turaren sa na mata.
Man bae hana ta ba sae kallonta da yake har ta shigar da hancinta gabad'aya cikin suit jacket d'in shi.

Billy giro😊
[10:00PM, 5/2/2017] Billy giro😊: ```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```

_wuhuu!Really! Really!!Really!!! appreciate! my dearest family, Aunty zygiro,Nanà giro, Shamsiya giro,Hafsat giro,Apeeya giro n Rayyanat giro wnn page in naku ne and these hearts goes to u ❤❤❤❤❤❤_

🔮🔮🔮🔮
*```Page 62```*
Sun jima a haka d'akin tsit kmr ba kowa mohd ya katse shirun yayin da ya shafo bayanta yace"ina son zanyi magana dake kinji"
Nn yaji shiru ba amsa yakae hannu ya d'ago fuskarta yaga ashe tayi bacci abinta.
ya lumshe idonsa a hnkli yana kallon yanda ta koma maida fuskarta a qirjinsa ta lafe sosai kmr wacce zata sha mamma.
Nan kawae ya d'aura hannun sa kan cikinta yana ta kallonta lokaci mai tsawo se can ya tashi ya kwantar da ita kan bed ya kama hanya zai bar d'akin sae kawae yaji qarar waya nn ya tsaya da d'an mamaki yana kallon wayar Rynt dake fmn ruri kan bedside drawer a hnkli ya qarasa gun bedside drawer d'in ya d'auki wayar yana mae kallon Rynt snn ya kalli mae kiran wato Sarah bayan kiran ya tsinke ne ya danna wasu lambobi ya kira nn wayar sa dake cikin aljihu ta shiga ruri ya katse kiran ta jikin wayar Rynt snn ya maida wayar ya ajiye kafin yake ciro tasa wayar a cikin aljihu yayi saving number d'in Rynt ya fito falo zai bar gidan yana mai jiyo sautin firar inna da Amir .

Bayan ya fita ne Amir dake ta fmn ci gaba da jan inna da fira yaji shigowar text a wayar sa koda ya duba mohd ne ,
sae da ya d'an qara lokaci snn yayiwa inna sallama ya fito ya sami mohd jingine a jikin mota yace"Hope ta amince"
Mohd yace"no ko mgnr ma ban samu nayi da ita ba tayi bacci but i got her number zan kirata sae muyi magana a waya"
Amir yace"to shikenn ai haka ma yafi"
Daga haka suka shiga mota suka bar gurin.

Mohd na komawa gida ya rage kayan jikin sa ya fad'a bathroom wanda sae da ya kwashe kusan awa d'aya kafin yake fitowa sanye da white bathrobe ya nufi fridge ya bud'e ya ciro fresh milk ya tsiyaya a cup yaje ya zauna kan sofa ya jingina bayan sa tare da d'aura qafafunsa kan footstool ya fara shan fresh milk cike da tunanin idan Rynt bata amince da zancen sa ba wace hanyar kuma zai bi.
Yana cikin hakane malika ta fad'o d'akin ya kalle ta kawae ya kauda kai taje gab dashi ta zauna had'e da riqo hannunsa tana kallon sa snn tace"my man umma ce bata jin dad'i shine nake son naje na dubo ta"
Hannunsa ya zare daga nata yana kallonta shaye da toka.
Ta wani maràiraice fuska tace"ba wani jimawa zanyi ba dan ko 10 bazan kai ba pls kaji?
"Ba inda zaki je"
Pls my.....bata iya qarasawa ba sbd wani irin mugun kallo da ya mata had'e da nuna mata qofar fita d'akin.
Rae 6ace ta tashi ta fita d'akin taje d'akinta.
Wacce da shigarta ta jawo wayarta ta kira ana d'aga wayar ne tace"wlh d'an banzan bai bar ni ba ka bari kawae gobe idan ya tafi aiki zan zo na same ka.......tana kaiwa nn ta katse wayar ba shiri tana kallon man dake tsaye a bakin qofar d'akin ,
ya qaraso gurinta yana mata kallon tuhuma snn yace"da uban wa kike waya!?
Malika dake kallon sa a tsorace ta samu da qyar tace"umma ce fa......bana son raini meyasa to da kika ganni kika katse wyr a tsorace iye!
Banga shigowar ka bane sae ganin ka da nayi shiyasa na tsorata.
Cikin kallon tuhumar da yake binta dashi ya kai hannu ya fizge wayar hannunta ya shiga call logs ,sweetheart2 shine last call nata ya kalle ta kawae ya cillar da wayar kan bed ya fita sbd sweetheart shine sunan da tayi saving number d'in mamarta dashi ,
sweetheart2 kuma numbar gayen da ta gama yawa da shine,shine man ya d'auka ko wata number mamar ta sake yi shiyasa ya fita kawae ya barta.
Malika kuwa man yana fita ta dafe qirji had'e da fitar da wani irin numfashi na ganin bae gano ta ba.
Chapter 64 · 0% Book details