← Book details Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 112

Sashe 103

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Ryynt kuwa har washe gari ba kanta sae wahala da take ta faman yi ita bata haifu ba ga jinin yaqi tsayi duk da irin taimakon da nurses keta bata kuwa.
Guraren qarfe goma sae ga mohd ya diro asibitin da kallo d'aya zakayi masa kasan hankalin sa a tashe yake.
Ya sami inna da Nasir still su kad'ai ne a asibitin ba wani wanda yazo dan ba'a sanar da kowa ba tukun sae anga yanda abun ya kasance.
Yace dasu"ya ake ciki ne dan Allah ina Ryynt d'in take in ganta?
Kafin suce komai sae ga wata likita ta fito tana ganin mohd tace"yauwa Dr ur wife tana cikin wani yanayi gabad'aya ta galabaita sam bata iya pushing any more da kamar sae an mata aiki"
A rud'e Mohd yace"muje in ganta"
Nan suka tafi kai tsaye se d'akin da Ryynt take wacce ke kwance kan gadon haifuwa abin tausayi duk ta wahala mohd ya nufi gurinta kmr zae yi kuka yana kallon yanda take bleeding a fusace ya kalli nurses d'inda da ke kan Ryynt yace"wane irin abune haka kun bar min ita sae bleeding take kuma kun kasa fitar min da babies d'ina so kuke su mutu ne ko yaya!
Likitar da suka shigo tare da shi tace"Sory Dr wlh it's not our fault haka aka kawo mana ita kuma munyi iya qoqarin mu amma abu ya faskara kawae abinda na fahimta ba time d'in haifuwar ta bane da akwai maganin da tasha da ya mata qarfi har ya tashi naqudar shiyasa ta wahala har ma abinda ke ciki duk ya galaibata baya iya yunqurin fitowa"
Kwalla tap a idonsa ya kalli ryynt wacce ke kallon sa ta kama hannun sa ta riqe gam a cikin nata cikin muryar kuka tace"Mk zan mutu"
Da sauri ya girgiza kansa yana mae share mata zufar goshinta da d'ayan hannun sa yace"Baza ki mutu ba my Ryynt ki nisa inshaa Allah yanzun zaki haifu kinji"
Ryynt da ko numfashin kirki bata iya yi muryar ta na rawa tace"Mk bazan iya ba mutuwa ma zanyi na sani"
Girgiza kansa yayi had'e da saurin kai hannu yana share mata hawayen da ke sauka kan fuskarta yace"um um my ryynt inshaa Allah baza ki mutu ba ki daina fad'ar haka dan Allah"
Tace"uhm uhm mk nayi qanqanta da haifuwa ka sani kuma wnn qaton cikin bansan ma ya zan iya haifo abinda ke ciki ba"
Yace"my Ryynt Allah zae taimake ki kawae rufe idonki ki nisa kinji dan Allah"
Ba musu ta rufe idanunta a hnkli tayi iya qoqarin ta na ganin ta nisa amma ta kasa sae kuka ta fashe masa dashi muryar ta na rawa tace"bazan iya ba mk dan Allah kiramin inna in ganta dan Allah"
Nan mohd yasa aka kira mata inna tazo Ryynt ta kama hannun inna sae kuka take tana roqon inna ta yafe mata mutuwa zatayi inna ta shiga rarrashinta tana mata addu'a tana tofa mata man kuwa duk yabi ya rud'e komai ya kasa yi sae shafar goshin Ryynt yake yana ta rarrashin ta wacce ta soma salati tana qoqarin miqewa sbd wata irin azaba da ta soma ji ta koma da qarfi ta saki hannun inna ta kama hannun mohd sae kuka take tana roqon ya yafe mata ga kuma salatin da take ta faman yi a bakinta yayinda take ta faman qoqarin miqewa man yana maida ta sae addu'a yake ta mata dan ya fahimci haifuwar tazo mata gab.
Da qarfin tsiya Ryynt ta qara riqe masa hannu sbd wani irin nishi mae qarfi da yazo mata a nn man yayi qoqarin cire hannun sa daga nata yaje da sauri yana bata taimako ta hanyar sa hannun sa ya soma ciro 'ya'yan sa d'aya bayan d'aya santala santala dasu biyu maza mace d'aya kuma kowanen su cikin qoshin lafiya.

Plz sorry 4 diz one

Billy giro😊
[10:07PM, 5/2/2017] Billy giro😊: ```🔮BAZAN BARSHI BA🔮```

🔮🔮🔮
*page 89*
A take nurses suka kar6i yaran dmn zuwa gyara su.
Cikin tsananin murna inna ta fita ta snr da Nasir abinda aka haifa.
Mohd kuwa ya kama Ryynt sae kissing d'inta yake yana mata sannu ita kuwa sae kallon sa kawae take qwalla tap a idonta.
Mohd da kanshi ya gyarawa Ryynt jikinta snn aka tafi da ita d'akin hutawa.
Nasir kuwa a lokacinda inna ta snr dashi ba qaramin farin ciki yaji ba wanda a nn take ya ciro wayar sa ya kira family house ya snr dasu.
Snn suka tafi d'akin da aka kae Ryynt sae barka suke mata shida inna suna mata sannu ,da aka shirya yaran aka kawo musu inna ta kar6i yaran d'aya bayan d'aya sae rawa take tana murna tana godewa ubangiji.
Haka ma Nasir bae yi rawa ba dae ya kar6i yaran cikin tsananin murna yana ta kallon su snn ya bawa mohd wanda bakin sa har kunne sae kallon kya wawan yaran sa yake da sak mazan shi suka biyo macen kuwa kamar an tsaga kara ita da Ryynt sae dae hasken duk na mohd ne.
Cike da so mohd ke kallon Ryynt yana nuna mata 'ya'yan su Ryyñt ta kalle su kawae bata ce komai ba shi kuma yayi zaune yana wa yaran sa addu'a.
A nn cikin asibitin mohd yasa aka had'awa Ryynt tea mae kauri tasha.
Basu bar asibitin ba sae ga mahaifiyar mohd tazo it da umman saliha.
Murna a gurin su ba'a cewa komai musamman mahaifiyar mohd da wani tsabar son Ryynt ya qara shiga ranta da duk motsi idan Ryynt tayi sae tace ya akayi ne Ryynt ba abinda ke maki ciwo dae ko, ko kina buqatar wani abu ne a kawo maki.
Ryynt kuwa kae kawae take girgiza mata d'auke da jin dad'in yau itace ke samun kulawa haka sosai a gun mahaifiyar mohd duk da cewa tuni ta fara samun kulawa a gurinta amma yau kulawar ta daban ce da kowa na cikin d'akin sae da yaji dad'in hakan musamman mohd wanda sae kiran wayar sa ake ana masa barka dan ba family ba har en uwa da abokan arziki duk an sanar dasu.

Sae da Ryynt ta sami hutu aka kuma tabbatar she is ok ba wata matsala snn suka nufi gida.
Gidan man suka nufa kmr yanda ya buqata snn ko za'a tafi gidan inna daga baya.
Suna shiga gidan da gud'a inna ta fito mota tana taka rawa dan farin cikin da take ciki ya ma wuce misali kuma irin tsafin nn ne da basa iya 6oye farin cikin su a koina.
Chapter 103 · 0% Book details