← Book details Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 112

Sashe 5

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari sallah kawai tayi tace da ummarta"ni xan koma"
Umma ta saki baki tana kallonta snn tace"amma pretty ni nasara ke wace irin mace ce wlh kowace mace na ganin ta samarwa kanta enci amma banda ke ,wane irin abu ne da baza ki bari sae nasir yazo da kansa ba ko zaki koma ,wlh kwata kwata kin 6ata kanki da sonda kike yiwa nasir kmr ba nice na haife ki ba....nifa umma ba haka bane naji kina waya da Abba yana kan hanya shiyasa zan tafi kar yazo ya sameni ya min fad'a kuma kinsan jiya da dare nasir yazo har yayi ta kiran wayata naqi na d'aga,to shi baqon gidan nn ne da bazai shigo ba sae ke zaki fita ki same shi ai inace yaje 6angaren uwar sa amma yaqi zowa nn,ai umma barshi don ni bama gidan sa nayi ba wlh gidan inna zan tafi,to idan inna ta tambayeki lafiya fa? Ai inna ce zan kwashe da ita dai dai ba kamar Abba ba ,to ai sae ki tashi kiyi niyya dmn gab yake da isowa garin nn.
Sauri sauri taje tayi wanka ta shirya sae neman makullin motar ta take duk ta jigata kamar zata yi kuka ta kalli ummarta da ta shigo tace"umma ina makullin mota ta? Yayanki yazo ya kar6a....haba umma meyasa kika bashi, kije ki roqe sa mana ai zai baki ,Allah umma kinsan da kamar wuya kidai roqa min shi ya bani, Aa ba ruwana can tsakanin ku ne kije ki gwada sa'ar ki idan ya baki to.
Wani abu yace miki da zai kar6i makullin motar ne?ba abinda yace min kawai dai ya kar6a ya tafi.
Cikin 6acin rai ta fito tayi kici6is da yayanta da kuma mijinta Nasir a nn harabar gidan kallo d'aya tayiwa Nasir ta kauda kai ta kalli yayanta tare da marairiace fuska tana roqon ya bata makullin motar ta,kallon nasir yayi yace"sae kaja matar taka ku tafi"
Ya sa qafa zai wuce tayi saurin shan gabanshi tace"pls yaya kayi haquri ka bani"
tsawa ya daka mata yace"wai ina wasa dake ne da kike tunanin zan kar6e abu na baki!
Le6ace baki tayi zuwa kuka tace"yaya ba fa laifi na bane na gaya ma"
Wayar sa da tayi ringing ya d'aga ya bar gurin ,kuka ta fashe dashi nasir yazo yaja hannunta ta fizge hannun taje ta shiga mota shima ya zagaya ya shiga yaja motar tana ganin ya hau titin zuwa gidan su ta dalla mai harara tace"nifa ba gidan ka zan tafi ba don ka sani gidan inna zanje gara tun wuri ka sauya hanya don ko munje gida ba shiga zanyi ba wlh ,kuma sae naci uban wnn er iskar yarinyar da ka kaiwa inna wacce a dalilinta aka hana ni jan mota sae naga ta yanda ma zata zauna gidan inna d'in dole ta barshi tunda ba gidan kakarta bane ko wani nata.
Nasir yayi shiru yana kallon pretty shidai ko kad'an baya son masifar nn tata gashi aikin kenan idan aka ta6o ta.
Hannun ta ya riqo tare da kai mata sumba snn yace"da kika yi shiru sae kika min kyau kamar ace ko yaushe haka kike ba ruwanki da fad'a"
Hm ba wani dad'in baki da zaka min nifa sae ka kaini gidan inna ,kallon ta yayi yana tunanin wayon da zai mata dmn yasan duk taje gidan inna ba qaramar rigima za'ayi ba,yace"gidan inna kwantar da hankalinki zan kaiki amma sae kin raka ni gida nayi wanka tukun,ta6e baki tayi tana kallonshi snn tace"wankan me zakayi da baza ka kaini gidan inna ba har sae na raka ka,banyi wanka ba da safen nn ina gama sallar asuba naje gida dmn nazo dake, kuma yunwa nake ji sosai kinsan kin tafi kin bar ni ba abinci kuma yau da safe ma haka,shine nake son ki had'a min breakfast kafin na fito wanka kinji,
ya fad'i haka ne cikin marairaicewa had'e da tsare ta da ido dmn yasan da ya mata haka bata iya masa gardama,
ta kauda fuskarta gefe kamar baza ta amince ba sae kuma tace "naji"

Karfe takwas da minti goma na dare Rayyanat na kitchen tana yi ma inna goge goge bayan ta gama wanke kwanukan da suka ci abincin ta ji an bude katon gate din gidan alamar mota xae shigo knn, duk lkcn da taji karan bude gate din sae gabanta ya fadi don ba sabawa tayi ba, bayan kusan minti bakwae inna ta shigo kitchen din ta gwalo ido tace "lahh bar maki aikin Hurera tayi" Rayyanat tace "A'a ni na karba inna" inna ta washe baki tace "ayyo!sannu da aiki jikata, ynxu duk ke kika gyara kitchen din nn hka" Rayyanat tayi murmushi ta sunkuyar da kanta bata dae ce komae ba, inna tace "to miko min wancan kulan abincin in kai ma mai gidana ya xo" Rayyanat ta dauko ta mika mata da ladabi inna ta fita tana cewa "yau ko dan kankanan da lemo bae siyo min ba ya kwaso kafafuwa ya xo xae cinye min abinci uwa shi ke siyo min" bayan minti goma da fitan inna Rayyanat ta gama abinda take a kitchen din baka taba cewa daga kauye take komae nata tsaf tsaf take yi, da kyar ta iya fitowa daga kitchen din a sanyaye tuno babanta da ta yi, hkn yasa kwalla ya cika idonta, tayi saurin sharewa bata tarda kowa falon ba sae hurera yar dattijuwar matar da ke goge tiles din falon ta kalleta tana murmushi tace "sannu Rayyanah, ki tafi can daya falon inna na can, amma ga furar ta nn da na dama mata ki dauka ki tafi mata da shi, Rayyanat ta gyada mata kai kawae ta dauki furan da ke rufe kan centre table ta nufi falon da Baaba Hurera ke nuna mata, inna na xaune kan tabarma ta tankwashe kafa ta kapa ma tv ido tana kallo uwa tasan abinda ake yi, shi kam yana xaune kan three seater rike da remote waya na kare kunnansa alamar waya yake, kallonsa kawae Rayyanat take a sace kuma a tsorace sae dae har lkcn bae juyo ba, inna ta juya da sauri ganinta a tsaye tace " A'a karaso mana Rayyanah" Sae a snn ya juya yana kallon da warce kakar tasa ke mgna, Rayyanat ta sake kwanon furar hannunta ba tare da ta shirya ba, inna ta mike da sauri tana salati, ya katse kiran da yake shi ma ya mike yana yatsine fuska yace "ina kika samo mai aikin nn kuma Inna, idan xa ku dauki masu aiki ku dinga bincike da kyau don Allah ku dena dauko yara irin hka masu kananan kwakwalwa, bnda hka meye xata shigo falon mutane ta sake masu kwanon fura a kasa kmr wata me tabin hnkli" juyawa Rayyanat tayi da gudu ta fice daga falon a rude.

Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[2:38PM, 5/2/2017] Billy giro😊: 🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮

```Na Billy giro😊```

16/12/2016

🔮```7```🔮
Oh Allah yoni hajara!kai muhammadu ai wnn yarinyar iyakar hnkli da natsuwa tsautsayi ne kawai da in yazo ba mai tare shi.
Inna ina hnkli a nn da shigowarta ta 6arar da fura kmr wacce bata saba ganin mutane ba,kudai 'ya'yan kabiru haka kuke abu kad'an ya isheku masifa,
inna yau maigidan naki kike gaya ma haka, yo ai ko waye kai tunda ka ta6a er albarkar nn dole na maka magana yarinya tsakanin jiya iyau lafiya muke zaune sae gashi kazo zama d'aya ka rikita ta har ta tafi da kuka,nidai inna da wnn mitar kira hurera tazo ta goge gurin nn ,kuma dan Allah kidaina kwaso iren iren yaran nn sam ba abin yarda bane da har kike saurin bama yarda zama d'aya,wai er had'uwar jiya zuwa yau ce kike kora min bayani kamar kun shekara, masifa inna ta shiga yi dashi,Man ya bita da kallo yana murmushi har ta fita.

Taje ta samu Rayyanat a d'aki sae kuka take rusawa,
tayi zaune tana rarrashinta har ta samu tayi shiru.
Rayyanat ta tashi tana share hawaye tace"inna bari naje na kwashe furar"a'a ai nasa hurera ta kwashe, kika sata inna nifa na 6arar,kar ki damu indai hurera ce bata da wnn,bari na tashi naje nabar maigidana shi kad'ai ,tace"to inna"inna na fita Rayyanat ta kifa kai taci gaba da kukanta.

Da dare Nasir yazo ya samu sun kammala cin abinci sunyi zaune suna kallo ya gaida inna snn ya samu guri ya zauna ,Rayyanat ta sadda kanta qasa tana miqa gaisuwa ya amsa gaisuwar snn yace"ya jiki ?tace"Alhmdlh yace"kina dai shan maganin ki akan lokaci ko? Gyd'a masa kai kawai tayi tana wasa da en yatsunta.
Ya maida dubansa gun inna da ta miqe qafafu tana kallon Indian film kamar wacce kejin wani abu dmn duk ta tattara natsuwarta a can.

Sae da abin ya bashi dariya sae dai bai yarda yayi ba dmn yasan masifa zata aje mai in tasan dalili dryr dmn kallo d'an gidan ta ne ba mai shiga tsakanin su.
Yace"inna hln mai gidan naki ya koya miki indiyan ci ne naga kin maida hankali sae sauraren su kike?yo ina fa na iya Rayyanah na saka ma shine nayi zaune nima ina kallon abin tausayi naga sae wulaqanci yarinyar kesha a gun mijinta,dariya yayi yace"to ke inna ya akayi kika san mijinta ne? Yo kai Nasir banda idanu ne ko ko banda fahimta,gashi har gado d'aya naga suna kwanciya ai wnn sae miji da mata,dariya kawai yayi ya ajiye zancen dmn ya kalli film d'in ba miji da mata bane budurwa ce da saurayi ya mata ciki shine yake wulaqanta ta.

Hannu yakai ya shafi sumar kanshi yace"inna zan tafi "ah ah kaiko da wuri haka ,inna aski zanje sae dai gobe idan na sake shigowa ,to Allah kiyaye ,
sae da yace"Amin snn ya fita.
Chapter 5 · 0% Book details