← Book details Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 112

Sashe 67

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Inna ta washe baki tace"to ko kaifa d'an albarka"
Shidae Aamil komai bai ce ba sae fita da yayi ya had'u da Abba ya fito d'akin Rynt ya sadda kansa kawae ya wuce zuwa d'akin Rynt Abba kuwa ya shiga d'akin inna,wanda sae da ya nemi guri ya zauna snn ya kalli inna dake zaune kan gefen gado wacce ke kallon sa tana fad'in"da kmr magana ka tsaya yi da Rynh ko?
Abba yace"eh inna hkne na tambaye ta ra'ayin ta ne kan had'a aurenta da Aamil sae bata iya cewa komai ba tamin shiru, daga baya da nace ko bata ra'ayin auren ne, tace ita a gsky tafi so tayi karatu, nace indai karatu ne kar ta damu dmn Aamil mai barinta ne ta qarasa karatun ta cikin jin dad'i da kwanciyar hnkli amma idan tafi son sae ta kammala karatun to,
sae ta min shiru kuma bata ce komai ba shine na fito na barta dmn na fhmci shawara take a ranta kmr wacce na fhmci yanzu tsoron aure take ganin irin wahalar da tasha a gun mohd shine take ganin kmr duk inda taje hkne.
Inna tace"dole ne fa tayi wnn tunanin amma ni mai fhmtar da ita ne sannu sannu har ta fahimci cewa ba duka a aka taru aka zama d'aya ba.
Abba yace"to shikenn inna ni zan tafi Allah sa a dace"
Tace"Amin d'an albarka Allah kiyaye hanya a gaida gida yace"to"snn ya fita.

Aamil kuwa a lokacin da ya nufi d'akin Rynt sae da yayi sallama Rynt ta amsa mar snn ya shiga ya sameta zaune gefen gado kanta qasa yace"Rynt dan Allah kiyi haquri sam ban gane ki ba bare na fhmci cewa ke mtr man ce shiyasa kika ji wani irin zance a bakin Abba da yake farin ciki da shi amma ni tunda na fhmci wace ce ke banida farin cikin da ya wuce ki koma d'akin ki, kiyi haquri ki manta komai kije ku gina sabuwar rayuwa keda man dmn nafhmci dgske yake son maida ke sbd irin damuwar da naga ya shiga a yau ban ta6a ganin sa a cikin irin ta,kuma ko don qaruwar da ke tsakanin ku ya kamata ace kinyi haquri kin koma kinji"
Muryar can ciki tace"to"
Dan kawai ta samu ta huta dashi dmn ita sam bata son jin ana zancen qaruwar da suka samu tsakanin ta da man abinda ko yaushe ftr ta taga an cire cikin ta huta amma sae wani zancen sa ake mata.
Aamil dake kallonta yace"naje na gaya ma Abba kin amince zaki koma gidan mohd d'in?
Tayi saurin kallon sa had'e da girgiza kai snn tace"sae nayi shawara tukun"
Yace "shikenn idan kin gama yanke shawarar sae ki gaya min"
Ta gyad'a masa kai kawae shi kuma ya fita ya bar d'akin.

6angaren su mohd kuwa a lokacin da Amir yaja shi suka fita da qyar ya samu mohd ya shiga mota wae a cewar yau in shi in Aamil dole a kwashi gawar d'ayan su don ba zai ta6a yarda ya auri Rynt ba sae dai ko idan da gawar Aamil za'a d'aura auren to zae gani.
Shine Amir ya samu da qyar da lallami ya kaisa gida ya dawo kan hnya sae mamakin Aamil yake da kuma mamakin Abba da ya yarda zai ba Aamil Rynt ya aura.

Guraren goma Amil ya tafi gidan Amir wanda yazo masa shaye da toka yana kallon sa Aamil ya sadda kansa qasa kawai ya shiga mai bayanin komai kan cewa shi bai san cewa Rynt mtr man bace shiyasa yajewa Abba da zancen yana son zai aureta ba wae dan yasan sun rabu ba.
Tun lokacinda Aamil ya fara zancen sa Amir ke kallon sa da mamaki se can yace"shine matsalar kai kwata kwata ba ruwanka da kowa bare ka san wnn waye ya kuma yake damu abinda kasa ma gaba kawae ka damu dashi wace irin rayuwa ce wnn kuma inace damu akayi bikin su kuma har gidan sa munje byn auren wanda muna zaune ta biyo ta wuce har ta gaida mu,haka ma a gidan inna mun had'u da ita ka sani,
Aamil yace"Amir wlh sam ban gane ta ba kawae dai d'ayar matar sa na sani malika da dama nsnta kafin auren.
Amir yace"to naji yanzu ya kake so ayi bayan duk kabi ka qara lallata komai"
Wàto Amir so nake ka raka ni muje gurin man na masa bayani na kuma basa haquri.
Amir ya girgiza kai snn yace"let tomorrow dan yanzu idan mukaje komai zai iya faruwa sbd ransa a 6ace yake sosai ba zai ta6a saurararka ba.
A sanyaye Aamil yace"shikenan Allah kaimu goben"
Amir yace"Amin"
Snn sukayi sallama kowa ya kama gabansa.

Washe gari da safe Rynt ce cikin shirin makarantar ta tsaf riqe da kofin tea a hannunta ta kasa sha don tun jiya har yau ta kasa sakewa sae tunani take tayi inna kuwa lalla6a ta shiga yi ta samu har tasha tean byn ta gama sae ga Aamil ya shigo gidan zai kaita school wanda ba don komai yake son ci gaba da kaita school ba sae don ya samu ya riqa bata magana har ta amince da komawar ta gidan man .
Inna na ganin Aamil ta washe baki suka gaisa cikin sakin fuska yayinda Rynt ta gaida shi ba yabo ba fallasa.
Snn suka fito suka kama hanyar makaranta.
Suna cikin tafiya ne sae kawai Aamil yaga motar man tasha gaban su kai tsaye har sae da yayi saurin cije birki ya tsaida motar ya fito yana kallon d'an uwan nasa da ya fito cikin mota a fusace,nn ya tafi zai qarasa gurinsa cike da niyar mai bayani man bai saurara masa ba sae kukan kura da yayi ya cakumi collar rigar sa had'e da kai sa ya manna sa jikin mota ya kuma shaqe mai wuya da hannunwansa duka biyu.
Aamil da bai ta6a tunanin abinda mohd zae masa ba knn sae qoqarin qwatar kansa ya shiga yi amma ya kasa nn Rynt ta fito mota a tsorace ta nufo su tayi tsaye a rud'e tana kallon yanda man ya shaqe Aamil da har idanuwan sa sun fara firfitowa,ai kuwa nn ta shiga ihu tana neman taimako.
Da qarshe ganin ba sarki sae Allah taje da kanta ta fizgo hannun mohd zata janye shi daga jikin Aamil bata iya janye shi ba sae abun hannu taji ta sa6ulo a hannun sa had'e da wani irin turi da mohd ya mata wanda bata an kara ba sae jin kanta tayi kamas! mota ta banke ta, nn ta saki wani irin ihun da yasa mohd ya jiyo cikin muguwar razana yayo kanta ya kwashe ta a rud'e ganin yanda jini ke fita a kanta yaje ya sakata a mota yaja motar aguje ya tafi ba tare da ya damu da sanin wanda ya kad'e ta ba da kuma Aamil da ya bari riqe da wuyan sa yana fmn tari.

Billy giro
[10:00PM, 5/2/2017] Billy giro😊: 🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮

🔮🔮🔮🔮
*```Page 64```*
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!
shine kake taji a bakin mutum biyu wato Nasir da Amir da sune suka fito cikin motar da aka kad'e Ryynt da ita wanda koda suka fito tuni man ya fice da Ryynt sai gun Aamil suka nufa da ke durqushe kan guiwoyinsa yana fmn ci gaba da tari.
A nn Nasir ya bud'e motar Aamil ya d'auko ruwan gora a mota ya ba Amir dake riqe da Aamil a cewar ya ba Aamil ruwan se su hanzarta zuwa asibiti dmn ganin halin da Ryynt ke ciki.
Bayan Aamil yasha ruwan ne suka d'aunguma gabad'ayan su se asibiti.
Wato Man specialist hospital inda kai tsaye A&E ward suka nufa suka samu an riga an shiga da ita zuwa dubata nn suka zauna zaman jiran a fito da ita, sae yi suke suna safa da marwa musamman Amir da shine ke tuqa motar koda abin ya faru.
Chapter 67 · 0% Book details