← Book details Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 112

Sashe 75

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari mohd ya riga Ryynt tashi yaje bathroom ya d'auro arwala yazo ya sameta ta farka amma bata tashi daga kwancen da take ba sae hannun ta da take d'an moving dashi kan bed ,
ya durqusa gab da ita had'e da riqo hannunta yana mai kallonta cike da tausayi bata kalle sa ba sae hannun ta da ta janye taje zuwa share qwallar da suka zubo mata ya riqe hannun ya kai nasa hannu ya share mata qwallar had'e da fad'in "yi hqr tashi kije kiyi arwala kizo muyi sallah kinji"
Shaye da toka ta kalle sa kawae ba tare da ta iya ce masa komai ba don kanta ke mata masifar ciwo a gurin ga zuciyar ta dake ta faman tashi,ba'a fi minti d'aya ba ta miqe lokaci d'aya ta tafi da gudu zuwa bathroom tana kwara amai ta samu da qyar aman ya tsaya mata mohd dake riqe da ita shi ya taimaka mata ta wanke bakinta ta d'auro arwala snn suka je sukayi sallah ko shi a daddafe tayi sllr wacce tana idarwa sae kwanciya tayi kan darduma mohd dake addu'a kallonta kawae yayi yaci gaba da addu'ar sa da ya gama ya tashi yaje ya bud'e fridge ya d'auko gasasshiyar kaza yaje ya mata warming sae gashi ya dawo d'auke da fresh milk a cup da kuma naman kazar da ya saka a cikin plate.
Yazo ya durqusa gab da ita yana kiran sunanta a hnkli bata tanka shi ba don har bacci ya kwashe ta a lokacin shi kuwa bae kula da hakan ba sae zama da yayi tare da janyo ta zuwa jikin sa ya cire mata hijab nn ta soma kuka dan sae a lokacin ta farka ya kira sunanta a natse yana ta6a jikinta da yaji ya soma yin zafi bai ji dad'in zafin jikin ba dan sae yaji damuwa a ransa.
Ryynt dake kan jikin sa sae qoqarin zamewa take ta kwanta kan darduma bai barta ba sae qara kwantar da ita yayi kan qirjinsa ya d'ebo naman kaza zae bata tayi saurin girgixa kanta alamar bata so ya ajiye naman ya shiga rarrashinta kan tasha ko fresh milk ce nn ma taqi kan dole ya barta ta koma kan darduma tayi kwanciyar ta bata jima ba bacci ya koma d'aukar ta.
Baccin qwarai tayi dan ba ita ta farka ba har sae da akayi sllr zuhur ta tashi a daddafe dan har lokacin bata jin dad'in jikinta taje tayi wanka ta fito ta nemi er doguwar riga ta saka snn ta sanya hijab tayi sallah a nn gurin tayi kwanciyar tana d'an jin tashin zuciya nn ta lumshe idanunta a hnkli
sae ga man ya shigo d'akin tana jinsa tayi kmr bata san da shigowar sa ba shi kuma yayi tsaye yana kallon ta d'auke da kular abincin da ya kar6o a gurin su Amir dan duk cikin gida d'aya suke kowa dae da nasa 6angare.
Kan dining yaje ya ajiye abincin snn ya d'auki breakfast d'inta dake ajiye tun d'azun ya fita dashi dan yasan yanzu kam lokacin cinsa ya wuce sae dae kuma lunch.
Bai wani jima ba ya dawo ya same ta kmr yanda ya barta wanda duk a tunanin sa bacci take.
Ita kuwa tana nn kwance cikin jin jiki har akayi sllr la'asar,yayinda man ke zaune sae kula yake da duk wani motsi nata.
Ganin anyi sllr la'asar ne yasa yaje yayo sllr ya dawo ya sameta itama tayi sllr tana zaune kan darduma ta had'e kai da guiwa tana fama da kanta dake mata masifar ciwo.
Yazo gab da ita ya durqusa ya shiga kiran sunanta a natse tayi kmr bata ji sa ba don ko magana bata son a mata.
Nan ya tashi ya d'ebo mata abinci ya kawo gabanta ya ajiye yace cikin muryar rarrashi "yi haquri kici abinci dan Allah kinga tun safe komai baki ci ba kinji"
Rynt kam qamshin abincin soma damunta ma yayi nn take taji cikinta ya hautsine ta soma yunqurin amae bai bar ta tashi ba ya riqe ta dan yasan ko taje wahala kawae zata yi dan ba wani abu taci ba,nn ya kwantar da ita kan qirjinsa yakai hannu yana shafa bayanta yayinda ta cusa fuskarta gabad'ya cikin qirjinsa tana shaqar qamshin turarensa da ya soma kwantar mata da zuciya daga haka ne bacci ya kwashe ta sae kallon ta yake cike da tausayi dan yasan dole tana jin yunwa gashi jikinta har yanxu yana d'auke da zafi.

Yana nn zaune abinshi rungume da ita sae bacci take ya soma jin zafin jikin nata sae qaruwa yake musamman kan goshinta nn ya d'auke ta yaje ya kwantar kan bed ya jawo wayar sa ya kira Amir ya gaya masa irin magungunan da yake buqata.
Ba jimawa yaji knocking yaje ya bud'e qofa,
Amir dake tsaye a bakin qofar yace"inace dae jikin da sauqi koh?
Mohd yace"to jikin nata sae zafi yake tayi tun safe har yanzun wlh gashi tana fama da yunwa don tun safe komai bata ci ba yanzu da na kawo mata abinci ko qamshin sa ma bata son ji bare ta iya cin sa.

Amir ya nisa tare da fad'in"bari naje to nasa my wife ta mata farfesun kifi ko zata iya cin sa"

Mohd yace"olryt tnks"
snn ya kar6i ledar magungunan da Amir ya miqa masa ya maida qofa ya rufe yaje ya ajiye ledar magungunan kan bedside drawer ya zauna jiki sanyaye kusa da Ryynt yana kallonta cikin tsabar tausayinta da yake ji don kallo d'aya zakayi mata kasan cewa tana jin jiki.
Bata wani jima da baccin ba ta farka sae juyi take tana neman fad'owa kan gadon mohd da ya fito daga bathroom yaxo da gudu ya tarbota,
ta dafe kanta dake mata masifar ciwo har bata son bud'e idonta sae hawaye kawae dake fitowa a idanun nata.
Fuskar sa d'auke da tausayi yakai hannu yana share mata hawaye snn ya jawo farfesun kifin da mtr Amir ta kawo mata tana bacci.
yana bud'e kular farfesun kifin knn,
taji tashin zuciya sosai bakinta ya cika tap da yawu ta tashi aguje ta nufi bathroom tana kwara amae mai wahalar gske dmn amman kumallo ne kawae,
tana gama amman ta samu da qyar ta wanke bakinta sbd wani irin jiri da ke d'ibar ta ga ciwon kai kuma.
Mohd ya riqo ta zae taimaka mata su fito bathroom d'in ta zame jikinta a hnkli ta zauna qasan tiles d'in bathroom d'in ta had'e kai da guiwa sae numfashi take fitarwa a wahale.
Mohd dake durqushe gabanta yana kallonta kmr ya cire ciwon yake ji ya maida jikin sa.
Cikin damuwa kmr zae yi kuka yace"Ryynt yi hqr tashi muje ki d'an ci wani abu sae kisha magani kinji"
Da qyar murya can ciki tace"um um bazan iya cin wnn farfesun kifin ba ka fita dashi dan Allah"
Mohd yace"shike nn idan na fitar me kike son a kawo maki kici to"
Cikin muryar kuka tace"nima ban sani ba kawai kaje ka fita da farfesun kifin tukun"
Nan ya kalleta snn ya tashi yaje ya d'auki farfesun kifin ya fita dashi wanda ya d'an jima kafin yake dawowa d'auke da ledar snacks a hannun sa yaga still bata fito daga bathroom ba yaje ya sameta kwance qasan tiles har ta koma yin wani bacci kuma,
ya d'auko ta ya fito da ita ya kwantar kan bed.
Yayi zaune gefen gadon had'e da dafe kansa don ko kad'an bae so ta koma yin baccin ba har sae ta d'an samu abinda taci ta kuma sha magani tukun.

Ba ita ta tashi daga baccin ba sae bayan isha'i ta tashi cikin kukan wahala dan wata irin yunwar masifa take ji ga jikinta da mugun zafi har ita kanta bata son ta6a jikin nata.
Mohd dake zaune tun d'azu zaman jiran farkawarta ya janyo ta a hnkli zuwa jikin sa yana share mata qwallah had'e da rarrashinta,
ta qara narkewa sosai a qirjinsa murya can ciki tace"zanci abinci"
Jikin sa na rawa ya jawo kular abincin su da aka kawo musu na dare ya d'ibar mata abincin a plate ya d'ebo a spoon zae kai bakinta ta kalli abincin kawae ta kauda kai,snn ta kalle sa qwalla tap a idonta kmr zasu zubo tace"kayi hqr dan Allah ni bazan iya cin wnn abincin ba idan da abun sha ka bani"
Jiki sanyaye ya maida abinci ya ajiye snn ya jawo pillow ya kwantar da ita don ya fhmci ko zama bata iya yi.
Ya tashi yaje ya bud'e fridge ya tsiyayo mata fresh milk ya kawo mata had'e da snacks d'in da ya siyo mata a d'azun ya shiga bata da kanshi ta d'anci ba sosai ba sae fresh milk da ta d'an sha rabin d'an qaramin cup tace zatayi sallah ya bata magunguna tasha snn ya ja hannunta zuwa bathroom ya taimaka mata har wanka tayi snn tayi arwala suka fito .
Tayi sallolin da ke kanta wacce da qyar taga ta kammala sallolin sbd har lokacin kanta kamar zae tsage take ji amma ta fara jin qarfin jiki dae dae gwargwado sae dae a kwance tayi addu'a dmn in ta kwanta ciwon kan na d'an
mata sauqi.
Mohd yazo ya sameta gurin ta kammala addu'a ya riqo hannunta tare da fad'in"zo muje to na kaiki kan bed ki kwanta koh"
Komai bata iya ce masa ba har ya tallabeta cak sae kallon sa take tayi har yaje da ita kan bed ya kwantar.

Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[10:00PM, 5/2/2017] Billy giro😊: 🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮
Chapter 75 · 0% Book details