← Book details Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 112

Sashe 68

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan awa d'aya da faruwar haka ne,inna Abba,Nasir, Aamil da kuma Amir zaune suke zugum a d'akin da akayi admitting d'in Ryynt wacce har an fito da ita sae jiran farfad'owarta suke yayinda mohd ke gefenta zaune cikin damuwa yana kallon fuskarta d'auke da goshinta da akayi rolling da bandage.
Yana cikin kallonta ne ta shiga motsi a hnkli had'e da fara ware hannunta da ke jimqe riqe a hannun man dashi kansa bai lura hannun nata a jimqe yake ba sae da yaji tana yunqurin ware hannun nn ya saki hannun a hnkli yana kallon hannun nata da take ci gaba da warewa har ta ware sa gabad'aya nn yaga ashe abin hannun sa ne riqe a hannun nata, ya d'ago yana kallonta ita kuwa sae kallon abun hannun take wanda sak irin wanda ta tsinta ne a tare da kud'in da aka jefawa baffanta,
a hnkli
ta d'ago ido sukayi 4 eyes ita da man wacce take idanuwanta suka ciko tap da qwalla har ma suka soma gangarowa gefen fuskarta.
Cikin tausayi mohd ya kai hannu zai share mata hawayen ,tayi saurin tashi zaune had'e da fad'in"wlh kar ka ta6a ni!mugu dama kai nake zargi kuma sae gashi kuwa tabbas kai d'in ne wlh ina gaya ma bazan barka ba sae na d'auki fansar abinda kayiwa Baffana ko da kuwa zan rasa raina.
Tana kaiwa nn ta had'e kai da guiwa had'e da fashewa da wani irin kuka mohd ya shiga kallonta cikin rashin fhmtar abinda tace,
haka ma su inna dake zagaye dasu wani iri suka ji zancen nata.
Abba yace"mohd me take cewa ne da kayi tsaye kawai kana kallonta"
Abba ya qarashe maganar ne yayinda Rynt ta d'ago da sauri tana kallon su d'aya bayan d'aya dan kwata kwata bata lura cewa akwai mutane a d'akin ba ta d'auka ko su kad'ai ne ita da mohd.
Tana cikin kallon su ne ta tsinkayo muryar mohd yana cewa"Abba nima ban fhmci inda zancen nata ya nufa ba asali ma tsoro nake idan ba wata matsala ce ta samu a qwaqwalwarta ba dmn zancen nata yayi kama da hkn.
Nan kawai suka ji inna ta fashe da kuka tana fad'in innalillahi wa inna ilaihi raji'una na shiga uku yau Rynh wace irin qaddara ce ta same ki da safiyar nn haka.
Rynt dake kallon mohd rai 6ace kan mgnr da taji yayi,
tayi saurin kallon inna tace"Allah inna ba abinda ya sameni lafiyata qalau ya fad'a ne kawae dan wlh ya duk san abinda nake magana akai"
Mohd yace"Rynt ni kuma wlh ban san abinda kike magana akai ba yi min bayani ta yanda zan fi fhmta kinji"
Wani irin kallon takaici tamai yayinda shi kuma yake kallonta with innocent face d'inshi.
Abba dake kallon su yace"kaga mohd nsn hlnka sarai ka iya maida mutane shashasha tun d'azu da muka zo muke tambayar ku dalilin faruwar wnn accident d'in nata amma kunqi gaya mana sae ce mana da kukayi qaddara ce yanzu kuma tazo da wani zancen kace kai baka sani ba bayan ba makawa kasani don nsn hln Rynt bata da banzar tabi'ar yin qarya"
Mohd ya kalli Abba yace"wlh na rantse Abba ni ban san me take magana akai ba"
Cikin muryar kuka mai d'auke da takaici Rynt tace"wlh ka sa....bata qarasa fad'a ba sae ihu da ta fasa tare da saurin dafe cikin ta,
a rud'e mohd ya matsa gab da ita zai riqota,ta sauka kan gadon ba shiri har tana qoqarin fad'uwa sae inna ce tayi saurin tarbo ta zuwa jikinta inda cikin tsananin 6acin rai inna ta kalli mohd da ya nufo su tace"kar ka kuskura kace zaka matso nn shashasha marar mutunci.
Cikin nuna damuwa mohd ya kalli Abba yace"dan Allah Abba a barni na dubata idan ba wata matsala bace cikin ya samu"
Abba yace"ko matsalar ce ai kai ka jawo shashasha kawai.
Nan mohd yaje zuwa sake magana Abba ya watsa masa mugun kallo kafin yake maida dubansa gun inna wacce taja Ryynt suka zauna kan bed yaje gab dasu cikin kulawa yace da Ryynt "a kira likita tazo ta dubaki ?
Ryynt wacce dama motsin cikin ne kawae ya sata ihu,
ta girgiza kanta tace"a'a Abba ba wata matsala bace dama"
Inna tace" Aa fa Rynh kin tabbatar"
ta gyad'a mata kai had'e da kallon man shaye da toka nn kawae ta fashe da wani sabon kuka sbd jin tayi komai ya dawo mata sabo har tana mamakin rashin imani irin nasa ta yanda ya kashe mata mahaifi wanda ya rage mata qwaya d'aya tal a duniya.
Nan fa taci gaba da kuka sosai inna na bata hqr amma bata iya daina kukan ba sae ma qaruwa da yake.

Inna ta kalli mohd dake tsaye a sukuikuice yana ta kallon ryynt,
Cikin 6acin rae tace"ja'irin yaro wae me ka mata ne kasa er mutane sae kuka take tayi ne iye!
Yace"inna nifa na gaya muku ban san me na mata ba"
Abba yace"kaga wlh kar ka maida mutane shashashu kan me to zata zauna tana irin wnn kukan hk "
Mohd yaje zuwa magana Abba bai barshi ba sae fad'a da yaci gaba da yimae sosai.
A nn ran mohd ya soma 6aci yace"haba Abba wae ya za'a yarda da shirmen zancenta ne nikam kawai a barni na duba ta tukun idan ba wata matsala ce ta samu a qwaqwalwarta ba idan kuma har dgske take cewa lafiyar ta qalau ai sae tayi bayani ta yanda kowa zai fi fahimta ba wae ta wani cumuimuye magana azo anata ganin laifi na a kan abinda sam banida masaniya akanshi.
Rynt dake kuka ta miqe tsaya tana kallon sa da idanuwan ta dake d'auke da tsanar sa qarara wacce taso ace ta bar abin daga ita sae shi amma ya soma kaita qololuwa ta yanda bazata iya barin abun ba har sae ta fallasa sirrin,duk da cewa tasan idan ta snr dasu ba lallai bane su barta ta d'auki fansar abinda tayi niyya amma tunda tana da evidence ko ta hanyar hukuma ne sae ta nemi fansar ta.
Nan ta kauda fuskar ta ba tare da tace dashi komai ba sae duban ta da ta maida gun Abba da inna kafin ta iya ce musu komai sae hawaye taji suna silalowa a hnkli kan kumatun ta inda cikin sanyin murya mai d'auke da rawar kuka tace"Abba ,inna, ina roqon ku da kuyi haquri da jin abinda zai fito bakina da kuma jin ainihin dalilin da yasa na zauna ina rayuwa tare da ku,nn wasu hawaye suka sake gangarowa akan fuskarta snn taci gaba da cewa"inna a gsky ina rayuwa daku ne kawai dmn d'aukar fansar abinda mohd ya min wato na kashe min baffana na da yayi"
ta qarashe mgnr ne had'e da fashewa da kuka yayinda mutanen d'akin suka ji zancen nata kmr saukar guduma a kunnen su inda cikin gwalo ido mai d'auke da tsananin mamaki kowa ke kallon mohd yayinda shi kuma mohd ya dasqare guri d'aya ya saki baki yana kallon Ryynt cikin fiddo ido mai d'auke da mamaki,
wanda kowa a gurin ya kasa cewa komai sae Abba ne yayi qarfin hln cewa"innalillahi wa inna ilaihi raji'un mohd me zanji!
Cikin rud'un da Mohd yake d'auke dashi yayi saurin girgiza kansa yace"No Abba wlh kwata kwata zancen ta ba gsky aciki kawai nafi yarda cewa accident d'in nn ya bawa qwaqwal war ta matsala, abarni na dubata dan Allah Abba"
Abba ya kalli Rynt wanda kafin yace komai ta riga sa da cewa"Aa Abba abinda nake so shine dan Allah muje gida gabad'ya mu dmn na nuna muku shaida ta ta yanda zaku fi fhmtar cewa da hnkli na nake zancen nn"
Ta qarashe mgnr had'e da kai hannu ta share hawayen da ke kan fuskarta.
Abba kuwa bai musa mata ba suka d'unguma gabad'ayan su har su Aamil sae zuwa gidan inna.
Bayan sun isa ne Ryynt taje sae d'akinta ta d'auko kud'i da abin hannu irin na man tazo zata bawa Abba wanda kafin ya kar6a Aamil ya miqe xumbur cikin tsananin tashin hnkli yana kallon abun hannun da kuma kud'in.

Billy giro😊
[10:00PM, 5/2/2017] Billy giro😊: 🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮
Chapter 68 · 0% Book details