← Book details Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 112

Sashe 62

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

5:00pm
Rynt ce zaune a falo ta tasa littafanta gaba tana dubawa sae ga Aamil ya shigo had'e da sallama ta amsa sallamar yayin da ta d'ago ta kalle shi bata kawo kowà ba sae shi Aamil d'in don ta fhmci yanzu kusan ko yaushe shine ke zowa.
Nn ta gaida shi fuskarta ba yabo ba fallasa ya amsa mata cikin sakin fuska snn yace inna fa.
Tace"inna tana maqota amma tace bazata jima ba zata dawo"
Yace"OK"snn ya zauna yana mae kallon Rynt da ta maida hnklinta gun duba littafanta yace"kuna da test ne?
Tace"um um ina dubawa ne kawae"
Yace"gud haka nada kyau ,but yaushe zaku fara exam ne?
Rynt tace"wani sati mai zowa inshaAllah"
Yace"olryt next week knn ,inga littafin"
Ba musu ta bashi ya kar6a yana dubawa nn yaga rubutun nata mai kyau dashi.
Yace" zaki koya min rubutun nn naki mae kyau"
Ya fad'i hkne d'auke da murmushi a fuskar sa yana kallon ta"
Kallon sa tayi ta kauda kanta d'auke da d'an guntun murmushi ba tare da tace komai ba,shima d'in dae bai ce komai ba sae sauka yayi kan kujerar da yake, ya zauna nn qasa inda yake fuskantar ta ya lanqawshe qafafu kmr yanda take zaune itama snn ya d'aura littafi a nn tsakiyar su ya kalle ta yace "a ina kika tsaya da karatun naki?
Tace"topic d'in yau ne kawae kuma shima tun a school na fara dubashi kuma shine kazo ka tarar ina dubawa"
Yace"shikenan zan tambaye ki abinda kika fhmta akan kowanne topic dake ciki"
Ta gyad'a masa kai yayin da shi kuma yaje ga topic d'in farko ya fara mata tambayoyi tana bashi amsa shi kuwa ya kafe idon shi akanta se kallon d'an qaramin bakinta yake dake ta koro bayani filla filla kmr malami na koyar da d'alibi.
Sallamar inna ce ta katse su nn Aamil ya fitar da numfashi a hnkli ya kalli inna tare da amsa mata sallamar snn ya gaidata.
Washe da baki ta amsa had'e da tambayar sa mutan gida
Yace"duk suna lafiya kuma suna gaida ke"
Tace"madallah ina amsawa"
Kafin take kallon yanda suke zaune da kuma littafin da ke hannun Aamil tace"Au yau kaine ka maye gurbin mai darasin nata knn "
Nan Aamil yayi saurin duba agogon hannun sa yace"af inna ai na
manta cewa lokacin lesson d'in nata yayi wata qil ma har yazo yayita sallama ba muji ba"
Inna tace"Aa ai yau ba zai zo ba sbd rnr yau an ke6e mata ita ne dan ta samu ta huta"
Aamil ya kalli Rynt yace"to inna ai karatu kuma na samu tanayi ba hutun ba"
Inna tace "yo ai ita Rynh ko yaushe haka take kullum cikin karatu take uwa ta jika takardar ta shanye"
Aamil dake kallon inna ya maida duban sa gun Rynt yana murmushi yace "Rynt is gud kid'an riqa hutawa kinji ko"
Gyad'a masa kai tayi shi kuma ya bata littafin ta tare da fad'in"to jeki ajiye gobe idan na dawo ma qarasa ko"
Tace"tohm" had'e da kar6ar littafin ta had'a da sauran snn ta tashi ta nufi d'aki yayin da Aamil ya bita da ido har ta shige d'aki yace "inna wae ina kika samo yarinyar nn ne wlh se naji ta kwanta min a rai sosai, ga ta da hnkli"
Jin shiru yasa ya maida duban sa gun inda inna ke tsaye yaga ashe ta d'aga bata nn.
Mikewa yyi a hnkli ya dauki makullin motar ya fita daga falon. Bayan 'yan mintina inna ta dawo falon rike da kofin fura tana cewa "gashi nn sauran na Ryynt ne...." Bude ido tayi tace "Au har ya tafi ko me?" Kwala ma Ryynt kira tayi ta fito inna tace "ina wnn yaron ba dae ya tafi ba" Ryynt tace "ban sani ba inna ina ciki" inna ta tsuke fuska tace "to in gidan uwarsa yaje xae tafi bae mata sallama ba dan bnxan yaro kawae, inda Muhd ya fi su knn" Rayyanat dae murmushi kawae tayi bata ce komae ba ta juya ta koma daki.
Karfe takwas da kusan rabi Ryynt na xaune falo suna kallo da baaba hurera inna kuma na daki tana sallah aka bude kofar falon hade da sallama, Amir ne ya shigo ya karaso cikin falon murmushi dauke a fuskarsa, baaba Hurera ya gaidar snn ya xauna yana kallon Ryynt, ta dan sake fuska had'e da gaishesa dan ta d'auka ko Aamil ne da ta d'an fara sabawa dàshi ,ya amsà gaisuwar yana màe ci gàba dà kàllonta yayin da Baaba hurera tace "Yau kaine a gidan namu shugaba"
sae a snn ryynt ta gane Amir ne don sunan da baaba hurera ke kiransa knn, yyi murmushi yana shafa kai yace "nine baaba, innar fa"Baaba Hurera tace "tana ciki tana sallah" shiru yyi bae ce komae ba yana dan satan kallon ryynt da ta maida dubanta ga kallon da take, mikewa baabà hurera tayi tace "bari in kawo maka abinsha ko" kmr jira yake yace "to baaba" ta mike ta nufi kitchen, sakkowa kasa yyi da sauri yana kallon ryynt yace "Rayyanat ina son muyi wata magana da ke don Allah, ko idan xan tafi xa ki dan fito na jiraki" hade rai tayi tace "nifa sanyi nake ji" shiru yyi yana kallonta snn yace "ae ba wani ddewa xa muyi ba" fitowar inna daga daki ne ya sanya shi yin shiru ya maida dubansa ga tv kmr me kallo, inna tayi michi michi da ido tace "waye wnn nake gani kmr Muhd a falona" Amir yyi yar dariya yace "A'a nine inna" tace "ayyo wace gulmar ce to naga kamar kana yi" dariya yyi ya mike yana kallon ryynt yace "ni kinga tafiyata ma inna tun daxu na shigo gaishe ki" bae jira cewarta ba ya fice daga falon.
Yayin da inna tace"to Allah kiyaye"snn ta nufi kitchen.
Rynt kuwa ba dan ran ta ya so ba ta tashi da sauri tabi Amir ta samu har ya fita gate, dan tsaki ta ja ta bi bayansa, jingine ta samesa jikin motarsa ta karasa tace "gani" bata rufe baki ba aka bude motar, kamshin turarensa kawae ya bugi hancinta ta juya a tsorace xata bar gurin ya fizgota, kuka ta saki tana kallon Amir tace "amma ka cuceni wllh," Amir ya girgixa mata kai yace "ki tsaya ki sauraremu Ryynt, mgnr fahimta muka xo ayi"cikin kuka tace " bana bukata, ni ku rabu dani kawae kar in maku ihu ko ana dole ne"
Nn ta gatsara wa mohd cixo ya cikata ba shiri tayi cikin gida a guje, Amir ya fuzar da iska yace "sae da nace maka kadda ka fito man ban san me ya fito da kai ba mtsw c wat you've caused now" Muhd ya dafe kansa yace "I just can't control my self ne" Amir yyi tsaki ya shige mota, Muhd ma ya bude motar a sanyaye ya shiga Amir ya tada suka bar layin. Ryynt na shigowa falo ta had'u da inna ta fito daga kitchen tace "Aa ina kika fito ne Rynh? ryynt dake kkrin boye hawayen fuskarta tace "na d'an fita ne kawai" snn ta nufi daki da sauri don xuwa yin kukan dake cinta ko xata ji ddi, wani mugun tsanar Muhd na mata yawo a xuciya.
Washegari ya kasance lahadi Ryynt na kitchen tana soye soyen kajin da Abba ya aiko masu da shi safiyar ranan Baaba hurera na can bakin famfo tana wanki, inna kuma ta tafi anguwa awanni biyu da suka wuce, gajiya ryynt tayi da soye soyen don wani mugun bacci kawae take ji gashi bata dad'e da farawa ba, tana kwashe Wanda ya soyu ta xuba wani ta xauna kan yar kujerar dake kitchen din ta jingina jikin bango ko minti biyu bata kara ba bacci me shegen nauyi ya dauketa, kiranta taji ana yi a nutse cikin bacci ta farka a tsorace lkci daya ta mike tsaye shi ma ya mike, kallonsa take har lkcn a tsorace tana son gane waye, ya sakar mata murmushi da ya bayyana fararen hakoransa, juyawa tayi da sauri tana kallon gas ta ganshi a kashe ta karasa gun da sauri don ganin suyan da take ta ga saura kadan ya qone, karasawa yyi kusa da ita yace "don me baki bari kin tashi daga bacci ba kika yi aikin," bata basa amsa ba sae ma gaishesa da tayi ta soma kkrin kwashe naman dake cikin mai.

Dan Allah kuyi hqr da na bar ku kuna ta zuba ido wato kwata kwata sabo da posting d'in dare ya mantar dani yanda nayi daku.
Gashi kuma yau na d'an samu kaina busy but am really sorry pls n pls 🙏🏻
Luv u all❤

Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[10:00PM, 5/2/2017] Billy giro😊: ```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```
Chapter 62 · 0% Book details