← Book details Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 112

Sashe 31

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Rynt kuwa gurin assembly students sae tsegumin ta suke ganin ta sanye da niqab kowa sae fad'in albarkacin bakinsa yake masamman da suka shiga class daga mai fad'in"ita wnn fa daga ina muka had'u da ita, sae me cewa qara'i sa niqab a secondary school ban ta6a gani ba, wata tace"hm koda kud'i wlh ba abinda zai sa na laqa wnn abun a fuska ta, wata tace inaga fa mtr aure ce don bazata sa niqab hk kawai ba, tace"wace mtr auren er qarama hk da ita kuma a ina kika ta6a ganin mtr aure a secondary school ai ko aure aka mata bata qare secondary school ba to sae dai kawai azo a zana mata waec n neco ,kawai dai inaga ma wani ciwo take d'auke dashi daya lalata mata duk rabin fuska shine akayi dabara da hkn.
Duk zancen nn Rynt na jin su sae duk haushin man ya turniqeta don ganin take duk shine yaja mata wnn srtn gashi ta tsani irin haka,ai kuwa kai tsaye tasa hannu ta cire niqab d'in,masu gulmar ta suka ce"lah ashe yrnyr lafiyarta qalau ra'ayi ne kawai,yayinda wata ta kusa da seat d'in Rynt ta matso a hnkli tace da Rynt"sister meyasa kika cire niqabin nn kinyi kyau wlh bare gashi klr wandon uniform kuma yadin sa mai laushi da santsi baki ga yanda yayi kyau akan hijabin ki fari ba wlh da kin mayar zaifi ,tayi magana ne yayinda ta kar6i niqabin a hannun Rynt tana dubawa sbd ita dgske take yayi kyau,tace"ki myr kinji sister"Rynt tayi d'an guntun murmushi tace"ai zan mayar"ta fad'i hk ne kawai don ta huta da srtn yrnyr.
Yrnyr tace"ok"
Daga nn sukayi shiru sae ga wani uncle ya shigo riqe da register a hannun shi duk suka tashi tsaye suka gaida shi sae da ya amsa snn ya basu ixinin zama shima yaje ya zauna ya fara kiran sunayen su d'ayan bayan d'aya har ya kawo gun sunan Rynt da ya ji sunan ya soma masa wuyar fad'a sbd ba bahaushe bane shiyasa wasu abubuwa ke masa wuyar fad'a,wanda a lokacin da Rynt ta amsa sae da ya kalle ta dan ganin mai sunan.

Sae five aka tada su sbd makarntar had'e take da islamiyya.

Suna a tsaye ita da mami suna jiran tahowar man,nn Rynt ta ciro niqabinta ta d'aura sbd gudun masifar man, d'aura niqabin keda wuya sae ga motar man ta kunno kai.

Da kanshi ya fito motar mami taje aguje ta rungume masa qafafu ,d'aukar ta yayi tare da kallon Rynt ta gaida shi ya amsa snn suka je cikin mota.
Kan hanya mami ta kalli man da ke gefen hagunta yana driven sbd a gaban mota take zaune Rynt kuwa na baya.
Tace yaya"Allah mkrntr nn da dad'i wata anti ta shigo ajinmu sae waqa take mana muna ta rawa kuma kasan me yaya? yace sae kin fad'a,tace"duk uncle d'inda da ya shigo ko aunty da waqa muke gaida shi na maka kaji,yace"yimin inji"
Tace"kaga anti na shigowa zamu tashi tsaye ne "nn ta tashi tsaye snn tace"sae mu fara da cewa.
_"Good morning aunty!we are very happy to see u!God bless u as u come today! Paa! pa papapa paaa!_
Muna tafawa itama tana tafawa snn sae tace "how are u? Muce we are fine aunty .
Man yayi murmushi yace"to shikenan zauna ki huta"turo baki tayi tace "yaya ban fa gama baka labari ba"sae da ya shafi fuskarta snn yace"to mami zauna sae kici gaba da gaya min"
Bata zaunan ba sae cewa tayi"bayan mun zauna sae ta mana waqa mai dad'i muna ta rawa abin mu kuma itama tana kama mana,na maka kaji ita ma?eh inaji, ta fara da
_"1,2 bought my shoes! 3,4 knock at d door!5,6 pick up sticks! 7,8 let them straight !9,10 a big fat hen!11,12 shoot ur gun! du! du!dudu! duu! I said shoot ur gun du!du!dudu! duuu!"_

Dariya ce ta qwacewa Rynt wacce tun d'azun take fmn danne ta amma ta kasa.
Sbd yanda mami ke rawar waqar abin dariya ne sosai.
Ta jikin mirror man ya hango Rynt dake fmn dariya sbd fuskarta ba niqab da shigar ta motar ta cire ta kad'a jaka.
Rynt ta tsagaita da dariyar ta yayinda mami ke cewa"Anti ai kuma yau kunyi ta rawa da waqa ko? Tace"Aa mami ai mu ba yara bane kmr ku"to Anti ai auntyn mu ma babbace amma takeyin rawa"eh ita malamar yara ce shiyasa, to anti meyasa kullum sae naga anti amarya nasa kid'a tana ta rawa bayan ita ba malamar yara bace?
Nn Rynt tayi rashin sa'ar had'a ido da man ta jikin mirror sae kawai ta kauda idonta tayi kmr ma bata ganshi ba tace da mami"wae mami ba islamiyya aka tashi ba yanzun nn amma sae zancen boko kike mana da tun qarfe biyu aka wuce gun" tace"yauwa anti a lokacin islamiyya ko, wani malami yace yana sona qanwa tunda na iya alfun ba'un har qarshe kuma ba kuskure ko d'aya ,nace masa ai antina ce kullum take koya min a gida har ma nace ko shi idan yana so yazo zaki koya masa,ko anti zaki koya mai in yazo ko?Rynt tace"uhm mami ai shi malami ne yafi ni iyawa sae dai ma ya koya min, to anti ai da na gaya mai a mkrntar kike yace yana so zai ganki sbd yaji dad'in yanda aka bani kulawa har ma nafi en ajinmu iya karatun qur'ani.
Mohd yace"mami ba kya gajiya da surutu ne wae nikam, a ajiye zancen nn haka kinji, kuma ki daina fad'ar abinda ba'a tambaye ki ba kinji,tace" to yaya zan tambayeka gobe idan zaka kawo mu school zaka saya min chocolate kan hanya sbd wanda ka saya min a kwanaki ya qare gashi yau da mukaje breakfast ina ta gani agun en ajin mu suna ci har da biscuit amma ni banda"
Yace"ai mami na siyo miki komai suna but na manta dasu ne.
Yauwa yaya na gode yanzu in muka isa gida sae a ftr ko? Yace "eh"nn ta kama waqar ta.
_pawpaw is a kind of fruit,sweet like sugar yellow like fanta every body like pawpaw ,pawpaw!_
_A lion !a lion!a lion has a tail he has a big head and a very small waist._

Haka tayi ta en waqoqinta sbd dama ta iya duk wasu waqoqi da take ji a bakin en gidan su.
Man dai da Rynt ba mai magana a cikin har suka isa gida.

Tun daga rnr man bai qara kaisu school ba driver ke kaisu yana d'aukosu.
Rynt kud'in break fast yake bata mami kuwa kuku ke had'a mata breakfast asa a lunch box.
Haka kuma tun daga rnr Rynt bata qara yadda taje da niqab a school ba sae dai idan zasu je takan sa da sun isa mkrnt se ta cire idan kuma zasu koma gida ta saka.
Yanzu har sunyi kusan sati biyu da fara zuwa makaranta amma har yanzu mohd bai nemowa Rynt mai lesson ba.

Rnr wata juma'a da qarfe 12:05pm man ne tsaye a parking lot ya bud'e gambun mota zai shiga sae ga su Rynt an dawo dasu daga school.
Ko tsayuwa motar su bata gama yi ba Rynt ta bud'e gambu ta fito mota ta tafi aguje cikin kuka ta shiga gidan.

Man dake qoqarin shiga mota sae fasawa yayi ya rufe gambun mota snn yabi Rynt cikin gida.
Chapter 31 · 0% Book details