← Book details Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 112

Sashe 4

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

```Na Billy giro😊```

11/12/2016

🔮```5```🔮
Suna shiga gidan kakar ta tarbe su da murna kamar har
Rayyanat d'in ta sani dmn akwai ta da son mutane sosai.
Bayan sun zauna ta kawo musu ruwa snn ita ma ta zauna suka qara gaisawa tace"daga ina haka muka samo baquwa nasir?, Nasir yace "wlh kaka pretty ce ta kad'e ta a bisa qaddara shine bayan ta kaita asibiti da kwana biyu aka sallamota to har yanzu dai bata fad'i ita wace ce ba dmn duk na tambayeta sae tayi tamin kuka ,
kawai dai ta sanar dani sunanta Rayyanat ,naso ta zauna can gidana har ta qarasa jin sauqi amma kinsan halin pretty shine naga kawai na kawota gurinki dmn zata ma fi jin dad'in zama a nn.
Kakar da ta bude baki tun fara mgnr sa tace "ikon Allah, wani irin tuki take har xata buge yar mutane snn kuma ta ki Bari ta xauna gidanta har ta warke, ni dae yaran Kabiru suna bn mmki da irin halinsu" Nasir dae yyi shiru bae ce komae ba, ganin sae fada kaka ke tayi kmr xata ari baki yasa yace "ynxu dae kaka kiyi hkuri hka, sae ta xauna gun ki har Allah ya sa a samo yan uwanta" kaka tace "yo in bata xauna nn ba ina xata xauna da" Nasir yyi murmushi yace "gskya ne kaka" Rayyanat kam sae kallon tsohuwar take nn da nn taji ta kwanta mata taji kuma xata iya xama da ita.

Kakar ta tashi ta shiga kitchen ta d'ebo abinci ta kawo mata tace "ki saki jinkinki fa ki d'auka nan tamkar gidan ku ne kinji, ita kuma xata xo ta sameni har gida, tukin ma daga ynxu sa xanyi Khabiru ya hanata tunda abun nata har da buge mutum, kwanaki ma hka ta buge dan mutane" Nasir dae bae ce komae ba,
Rayyant ta sunkuyar da kanta tana mai share qwallah had'e da ajiye d'an ledar da ke hannunta.
Kakar tace "kawo ledar na shigar miki da ita idan kin kammala sae ki watsa ruwa ko kyaji d'an damar jikin ki, ki kwanta ki huta"
Bayan takai ledar ta dawo tana mai duban Nasir tace"ina ce ka siya mata magungunan da zata ci gaba da sha? Nasir yace Eh akwai magunguna a cikin ledar ta idan ta gama cin abinci sae tasha kafin tayi wanka dmn lokacin shan magunan ma yayi.
Yana gama fad'ar haka ya tashi yace"inna ni zan tafi sae anjima idan na dawo " inna ta washe baki tace "To Allah yyi maka albarka" ya amsa da Ameen yana murmushi ya nufi kofa xae fita, juyowa yyi yace "am yau man bai shigo bane inna? Inna tace " waye kuma hka?" Nasir yyi dariya yace "Mai gidan ki mana" ta tabe baki tace "Tun da safe ya shigo da dan rashin mutun cin sa, amma na taka masa burki, to har ynxu dae bn gansa ba" Nasir yyi dariya yace "to shknn" inna tace"ko da wani abu ne?" Aa ba komae naga ko yaushe na xo yana nane da ke ne,"

Har gurin motar sa ta rakashi ta dube shi da kulawa tace"Nasir gaskiya yarinyar nn da akwai alamomi ban tausayi a tare da ita jifa tunda kuka shigo bata da aiki sae na share qwallah,ai ma inna kad'an kika gani baran idan aka tambayeta inda ta fito, shiyasa yanzu nafi son sae taji sauqi tukun ko zan sake tuntu6ar ta.
To Allah yasa ta kirki ce kamar yanda nake ji a raina ni dae ta kwanta min wllh, Nasir yace Amin inna.
Daga haka ya shiga motorsa ya wuce, inna kuwa ta koma daga ciki.

Nasir kuwa yana zuwa gida ya samu gidan a hargitse duk pretty ta farfashe abubuwa ta kuma tafiyarta gidan su kamar yanda tace.

6angaren pretty sae kuka take sosai a jikin wata mata da nake sa ran ummanta ce ita kuwa sae masifa take inda take fita ba nn take shiga ba na ganin har dare Nasir yaqi zuwa ya sasanta shida pretty.
Wani gaye ne ya shigo d'akin Alhmdlh ya had'u ta koina baya da makusa tamkar balarabe fari tas dashi,yana d'auke da d'an siririn saje kan fuskarsa .
D'ayan hannunsa yana riqe da suit baqa kalar wandon da ke jikin sa,yayinda rgr jikinsa ta kasance fara mai ratsin layi layi.
D'ayan hannunsa kuma yana sanye a cikin aljhun wandonsa.
tsaye kawai yayi yana kallon su ba shi da niyyar cewa komai .
Mamar ce ta fara ganin shi ,ya gaishe ta ta amsa inda cikin nuna damuwa sosai tace"man kaji abinda Nasir yayi wa qanwar ka pretty.

Nan mamar ta zayyana mai abinda pretty ta fad'a mata.
Bai ce da mamar komai ba ya kalli kanwar tasa fuskar sa ba yabo ba fallasa yace "garin ya akayi kika kad'e ta? Kmr xata yi kuka tace yaya ina lokacinda zamu tarbo su umma har ka tsaya wani gidan mai ka bada sadaka? Yyi shiru yana kallonta, hkn yasa ta turo baki tace yaya ni fa ba laifi na bne yarinyar ce Jaka, ina ga daga kauye ta fito, wani mugun kallo ya shiga yi mata, ta dauke kai tana murguda baki, ya gyada kai yace "daga yau kar ki kuskura ki kara jan mota" ta xaro ido tana kallonsa tace "sbda me, ko mijina fa bae hanani va yaya" tsawa ya daka mata yace "nace kar ki kuma jan mota"
Daga haka ya fita ba tare da ya tsaya jin me zata ce ba .

Tafiya yake a hnkli har ya isa 6anfarensa.
D'akin sa wani irin d'aki ne mai masifar kyau da tsari komai fari tas sae qawar da akayi da golden ga tsarin d'akin ba wani tarkace kamar tsarin d'akin turawa.
Frigde ya bud'e ya ciro gorar ruwa ya bud'e ya tsiyaya ruwan a glass cup yasha snn yaje ya cire kayan jikin sa ya sanya white bathrobe ya nufi bathroom.

Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[2:38PM, 5/2/2017] Billy giro😊: 🔮```BAZAN BARSHI BA```🔮

```Na Billy giro😊```

11/12/2016

🔮```6```🔮
Ya jima sosai kafin yake fitowa yana gama shiri yaji ana masa knocking yaje ya bud'e qofa idanunsà suka sauka kan qanwar sa pretty dake tsaye riqe da trayn abinci fuskar ta fam kamar zata fashe don fushi tace"amma dai yaya zancen na daina tuqi da wasa kake min ko?mugun kallo ya watsa mata ya juyarwarsa ya koma daga ciki,ta shiga ta ajiye trayn sea qunquni take ita ba wanda ya isa ya hanata tuqin mota kan wata jaka can er qauye marar asali ma,
Bai kulata ba har ta qaraci surutunta ta fita.
Chapter 4 · 0% Book details