← Book details Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 112

Sashe 63

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

🔮🔮🔮🔮
*```Page 61```*
Tsaye kawae yayi yana kallonta har ta gama kwashe naman ta zuba wani snn ta kalle shi tace"nifa kasan ba gane ku nakeyi ba waye kai?
Aamil da still kallonta yake ya lumshe idonsa a hknli ya kuma ware su akanta snn yace"Aamil ne"
Tace"oh yi hqr ai na d'auka ko wancan d'ayan ne"
Yayi murmushi snn yace"ba komai je ki qarasa baccin naki idan naman ya soyu se na kwashe maki ko"
Murmushi tayi had'e da girgiza kai snn tace"ai baccin ma ya tafi"
Yace"eyyah sorry ashe da ban tashe ki ba"
Tace"ai ba komai dama karatu nake da niya idan na kammala suyar"
Yace"wae ke kam ba kya hutu ne Rynt"
Ta kalle sa tace"uhm jarabawa fa zamu fara gobe"
Yace"hkne fa gobe ne monday ko?
Ta gyad'a masa kai had'e da fad'in eh"yayinda ta d'auki abun tsama tana juya suyar da naman ya soyu ta kwashe suka koma falo Aamil yace ta d'auko littafanta ya taya ta dubawa.
Ba musu taje d'aki ta dau'ko littafinta da za'ayi masu jarrabawar sa gobe.
Sukayi zaune a nn tsakiyar falon yana mata tambayoyi tana bashi amsa cikin natsuwa shi kuma sae kallonta yake tayi dan gabad'aya ta tafi da hnklinshi ganin komai ya tamvaye ta kai tsaye take bashi amsa da kuma bayani gamsasshe wanda har ya gama mata tambayoyi akan all topics d'in da ke cikin littafin en kurarra kad'an tayi ya gyra mata.
Ya bata littafinta d'auke da murmushi a fuskar sa yace"na yaba da qoqarin ki sosai Rynt ina roqon Allah yasa kifi haka "
Cikin nuna jin dad'i tace"Amin nagode"
Kafin Aamil ke cewa to d'auko wani littafin sae mu duba ko"
Kallon sa tayi cikin yanayi na shagwa6a da sam bata san tayi ba tace"Allah bacci nakeji sosai"
Sae dai ya d'an jima yana kallonta kan yanayin shagwa6ar da tayi snn yace"ok jeki kiyi baccin"
Tace"to"snn ta tashi ta tafi d'aki.
A nn Aamil ya furzadda iskan bakin sa a hnkli tare da jingina bayansa a jikin doguwar kujera yana mae bin qofar Rynt da kallo dan ko kad'an bai so ta tashi ba.
Inna da nasir ne suka shigo ya miqe had'e da amsa sallamarsu snn yaba nasir hannu suka gaisa ya kalli inna yace"wae inna dama ba kya nn ne?
Inna tace"yo naji shashasha da to a gurin wa kazo da har baka san bana nn ba"
Sae da yayi murmushi snn yace"inna gurin wa zan zo kuwa banda ke kawae dae da ban ganki ba na d'auka ko kina ciki kina bacci"
Tace"au ai ka tambayi Rynh kaji inda nake ko kuma baka ga Ryynh d'in bane itama"
yace"na ganta har ma mu kayi karatu yanzu ma ta shiga daga ciki zatayi bacci.
Inna tace"wato kama ga Rynh sae baka tambaye ta inda nake ba dan ba ina uwarka ba ko"
Er dariya Aamil da nasir su kayi snn Aamil yace"ko d'aya inna ba hk bane kin sani"
Tace"to ya kabaro mutan gida?
Yace"suna lfy ,ai ilham har so tayi nazo da ita sae gashi koda zan fito tayi bacci"
Inna tace"ayyo ai sae kazo min da ita gobe idan zaka zo ko"
Yace"to inna"kafin yake cewa ni zan tafi"
inna tace"au ko gaisawa ba muyi ba har zaka tafi"
Yace"inna akwai d'an wani aiki da nake son naje gida nayi ne amma inshaAllah zan dawo anjima"
Tace"to a dawo lafiya"
Nan suka fita shida nasir wanda shima sae da yayiwa inna sallama kafin suke fita.

Washe gari man ne da Amir a bakin mkrntar su Rynt fake cikin mota sae ga Rynt ta fito gate wacce kai tsaye ta nufi motar drivernta da yazo d'aukar ta yayin da Amir ya kalli man dake kallon Rynt har ta shiga motar suka tafi bae ce komai ba sae jan tashi motar yayi yabi bayan su har suka iso gidan inna,
Rynt da drivernta sam basu lura cewa ana bibiyar su a baya ba.
Wacce koda ta fito motar hnklinta na gun Aamil da ta hango shigar sa gidan riqe da hannun er sa ilham ta kwasa aguje ta shiga gidan tana kiran ilham.

Ba shiri man dake cikin mota ya bud'e gambu motar zai fito Amir ya riqe shi yace"ya kake hkne wae"
Cikin damuwa man ya kalle sa yace"kai baka ga yanda ta kwasa aguje bane bayan ba ita kad'ai bace ka sani"
Yace"its all ur fault da ka mata ciki bayan kasan qaramar yarinya ce"
Rai 6ace yace"abinda zaka ce knn"
Amir yayi er dariya yace"yanzu dae meyasa muka biyota tun daga school har nn nida na d'auka ko da ta fito d'in nn zaka je ka sameta ne kuyi magana amma sae naga kana kallo har wae taje ta shiga mota driver yaja suka tafi baka ce komai ba sae wani biyo su da mukayi"
Man yace"Amir dama fa ina so na ganta ne kawae"
Amir yace"to ya zancen mgnr da muke son muyi da ita ne?
Zan same ta anjima muyi maganar,
A ina knn ?a nn gidan mana ,ta yaya tunda dae kasan yanzu bazata qara yarda ta fito ba,hkne zan sameta ne a d'akinta ,kana nufin cikin gidan zaka shiga knn? Eh ai ba yau na saba ba,hm amma kasan dae idan inna ta ganka baza ku kwashe ta dae dae ba ko, inshaAllah ma bazata ganni ba.
Allah yasa cewar Amir man yace"Amin had'e da jan motar suka bar gurin.
Rynt kuwa tana qwalawa ilham kira suka jiyo da ita har Aamil nn ilham taje da gudu jikin Rynt ta rungume ta yayinda Aamil yayi tsaye d'auke da murmushi yana mamakin yaushe suka san juna ne da har suka saba haka.
Rynt d'auke da ilham ta qaraso gurin shi ta gaida shi ya amsa tare da fad'in ya exam?
Cikin sakin fuska tace"Alhmdlh"
Snn suka qarasa daga ciki yana mai fad'in "yaushe kuka san juna ke da ilham ne?
Tace"ranar ne fa kawae da suka kawo wa inna yini"
Aamil yayi murmushi had'e da jinjina kai don ya tuna rnr har wasa ya gansu sunayi.
A nn Rynt ta fice d'aki da ilham yayinda shi kuma ya nufi d'akin inna yana mai jiyo Rynt dake tambayar ilham Sadiq fa? (cewa da d'an Amir).

Da dare mohd ne ya shigo gidan wanda kai tsaye d'akin Rynt ya nufa koda ya mird'a handle yaji sa gam a rufe ya dafe kai cikin damuwa had'e da kallon qofar inna ya nufi qofar a hnkli cikin sand'a ya leqa.
Da sauri ya shiga d'akin ganin inna bata ciki sae Rynt dake kwance kan bed riqe da littafi a hannunta ta kare fuskarta.
Koda ya qarasa shiga d'akin yaji saukar ruwa a batroom alamar inna na ciki tana wanka yaje gab da Rynt had'e da d'auke littafin da ke kan fuskarta nn yaga ashe bacci take ,
ajiye littafin yayi gefe yana ta kallon fuskarta sae can ya maida duban sa a kan cikinta tare da d'aura hannun sa akai yana shafawa a hnkli Rynt ta motsa had'e da juya kwanciyar ta nn kawae yaji inna ta bud'e bathroom zata fito ya tashi da sauri zai bar d'akin sae kawae makullin motar sa ya fad'i a nn tsakiyar d'akin bae iya d'aukar makullin ba ya fita sbd a lokacin har inna ta fito tana fad'in"waye ne?
"Nine"cewar Amir wanda ya duqa tare da d'aukar makullin ,
inna tace"yau kuma zuwan dare aka min?
Cikin sakin fuska Amir yace" na shigo ne kawae mu gaisa na tafi dan kan hanya nake"
Inna ta washe baki tace"to sannu d'an albarka ai ka kyauta ya Maryam da sadiqu duk suna lfy dae ko.
Yace"lafiya qalau suke"
Tace"madallah" kafin yake cewa" to inna a kwana lafiya zan tafi sae gobe idan na shigo inshaAllah"
Tace"to a gaida gida Allah kai lafiya"
Yace"Amin kafin yake fita.

A wajen gate ya sami man jingine a jikin motar sa ya qarasa gab dashi yana kallon sa yace"u see yanzu da banzo ba fa ya knn kaida kace d'akinta zaka sameta shine ka wani je ka sameta har d'akin inna"
Man dake kallon Amir cikin damuwa yace"Amir ban same ta d'akin ta bane shiyasa"
Da baka same ta can d'in ba ai se ka haqura har gobe ba wae kaje d'akin inna ba,Amir wane irin haquri ka kuwa san irin yanayin da nake ciki ko kuwa don ba kai bane.
A natse Amir ya kai hannu ya dafa shi yace"man duk da bani bane na fhmci irin yanayin da kake ciki sosai amma zan fi so kabi komai a sannu har ka cimma yin nasarar shawo kanta.
Hakane amma dae kasan bazan iya haqura ba sae na dawo gobe ko,ai ba wae nace kar ka dawo gobe bane a sannu nace kabi komai ta yanda har ka samu ka shawo kanta ba a sami wata matsala ba but anjima da yamma zan rako ka muzo kai sae ka tsaya a qofar gida ni kuma se na shiga dmn naje na samu na janye hnklin inna da fira zuwa d'akinta so a nn zan maka flash sae ka shigo kaje d'akin Ryynt sae kuyi magana.
Man ya sauke ajiyar zuciya yace"shike nn"
Nan Amir ya bashi makullin motar sa man ya kar6a ya shiga motar yayinda Amir yaje ga tashi motar ya shiga suka bar qofar gidan.
Chapter 63 · 0% Book details