← Book details Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 112

Sashe 6

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ko minti ashirin bai yi da fita ba sae ga Man ya shigo gidan sae dai shi ba kallo ya samu suna yi ba tausa ya samu Rayyanat tana yima inna.
Rayyanat na ganin shi sae duk ta nemi natsuwar ta ta rasa, haka ta dake ta gaida shi ta kuma yi saurin tashi tabar gurin.
Bai ma amsa gaisuwar ba sae inna ya gaida ya ajiye ledar da ya shigo da ita kusa da inna snn ya zauna,inna ta tashi zaune tana washe haqora tace"me kuma kazo min dashi yau? Sae da ya jingina bayansa kan 2 seater d'inda yake zaune snn yace"gasasshiyar hantar rago ce na siyo miki kan hanya"
Kai Allah dai shi yi maka albarka kamar kasan nayi kewarta wlh,ai inna har fruit naso siya miki se na manta,,ayyo ai d'azun da rana Nasir ya shigo min dasu munsha har mun gode Allah har ga saura a fridge ko na d'auko ma zaka sha?Aa inna, to abinci kam zaka ci dai ko? shima haka dmn a qoshe nake, yau tawaye kamin kenan ,Aa naci abinci ne a gidan wani abokin mu da yayi sabon aure muka je, oh ni kakata talatu kai yanzu ka gwammace kayi ta zuwa gidan abokanai ba a zuwa naka ,
wai nikam yaushe zaka fara ra'ayin aure ne muhamnadu,hm inna ai aure lokaci
ne dashi kin sani in lokaci yayi zanyi har ma a wayi gari watarana kina zaune zagaye da en jikokin ki, nn inna ta washe baki tace"Allah nuna mana lokaci muna masu rai da lafiya"Amin inna.

Washe gari Rayyanat ta gama taya hurera duk ayukkan da take tazo tayi kwance qasan tiles tana jiran fitowar inna daga gurin wanka nn bacci yayi awon gaba da ita.

Pretty ce ta shigo gidan tayi tsaye tana kallon Rayyanat dake bacci tace"yau zaki ci ubanki yarinya"
Nan taje ta bud'e fridge har ta d'auko gorar ruwan sanyi sae kuma ta girgiza kai ta mayar ta nufi kici tana murmushin mugunta ta d'auko flask d'in ruwan zafi tazo kai tsaye ta bud'e tana kwara ma Rayyanat su a jiki ,
ihu Rayyanat ta saki ta tashi a firgice tana lalubar bayanta inda taji saukar ruwan zafi.
Mari pretty takai mata tace"er iska ai yau sae kin bar gidan nn wlh tunda bana ubanki bane!
Taja Rayyanat kamar wata kayan banza ta ingizata waje da qarfi sae kawai Rayyanat taji ta fad'a jikin mutum hkn yasa taji saukar wani irin gigitaccen marinda ya soma fitar da ita hayyacinta.

Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[2:38PM, 5/2/2017] Billy giro😊: 🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮

```Na Billy giro😊```

17/12/2016

🔮```8```🔮
La'ilaha ilallahu Muhammadu rasulillahi sallallahu Alaihi wa sallam!
Cewar inna wacce ta fito daga gurin wanka tace"Muhammad me rayyanah ta muku ne da zaku mata taron dangi tun ina bayi naji ihunta Fatima na faman sirfa mata masifa yanzu gashi na samu ka tafka mata uban mari haka!inna ta qarasa magana cikin muryar kuka irin na tsafi d'in nan.
Nan take man damuwar sa ta bayyana ya shiga bawa inna haquri bata kula shi ba sae kuka take taja Rayyanat suka koma cikin d'aki.
Pretty ta kalli man dake qoqarin bin su inna tace"to wai meye abun damuwa kabar su mana tunda kasan halin inna dama saurin kuka ne da ita in ba don shi ba meye abin kuka wa wannan er qauyen,harara ya dalla mata yace ai duk ta dalilin kine banga uban me ya kawo ki gidan nn ba....kamar ya yaya...zan mare ki wlh idan baki 6ace min da gani ba!
Turo baki tayi tana faman gunguni har ta fita gidan.
Man kuwa shiga d'akin yayi amma a iya falo ya tsaya inna ta fito tana shar6ar hawaye zata d'auki wayarta dake kan TV stand yace"inna yi haquri Allah sam na d'auka rashin hnklinta ne yasa ta fad'o min a jiki ban san cewa pretty ce ta ingixo ta ba,amma Muhammadu ai ka saurara mata ko! yanzu gashi bayan fasa mata baki da kayi duk bayanta ya kwaye... Kamar ya inna nifa marinta kawai nayi... Yo kai ba kasan ruwan zafi pretty ta watsa mata a baya ba,shiga ka duba ta kaga ai nasan dole sae an yanke wnn ftr ,ta qarasa maganar cikin kuka snn tace"ka shiga mana ka duba min yarinyar mutane kazo kayi tsaye se kallona kake!
Ba musu ya shiga ya sami Rayyanat ruf da ciki se kuka take abin tausayi zip d'in rigar ta a bud'e fatar bayanta har yyi ja, kauda fuskar sa yayi tare da sauke ajiyar zuciya snn ya kalli inna dake tsaye kusa dashi tana matsar kwalla yace "inna ina ganin ta sosa bayanta ne a lokacin da aka watsa mata ruwan, kuma wnn da gani ma ba wani ruwa me xafi bne, Rayyanat da bata ji shigowarsa dakin ba sae maganar sa taji tayi saurin tashi xata rufe zip d'in rgrta, inna ta karaso da sauri
tace "A'a Rayyanah kar ki rufe ai shi likita ne zai duba miki bayanki in kuma baxae iya ba sae ya kira mana ubansa ya xo ya kai mu asibiti," Rayyanat ta girgiza kai ba tare da ta kallesu ba alamar bata so, inna tace "A'a ki yi haquri ya duba ki kinji jikata"
Man da takaici ya ishe shi yace "inna bari kawai zan turo a duba ta" yana kai wa nn ya fice daga dakin kmr xae tashi sama.

Sae da ya kira wani abokinsa likita snn ya bar gidan ya nufi gidan kanwarsa pretty.
Yana isa gidan Nasir ya samu kan dining sama sama suka gaisa yace masa "ina pretty" kafin ya basa amsa sae ga prettyn ta sauko, bata damu da ganin fuskar yayanta ba annuri ba ta daure fuska ssae tace "gani yaya lafiya dai ko"
Yyi mata wani mugun kallo yace "me wnn yarinyar ta miki da zaki xuba mata ruwan xafi a jiki," shiru pretty tayi tana kallon shi kamar bata san me ya faru ba har lkcn fuskarta a tamke, ya daka mata tsawa yace "ya kika min shiru kina kallona ina maki mgna?" Ta tabe baki tace
"To nifa yaya ban gane zancen da kake ba bare na iya ce maka wani abu," nn ya fahimci ta fita ne bada ixinin nasir ba shine take wani nuna kamar bata san da zancen ba.
mari ya kai mata don bata da nisa daga inda yake yace "yanzu kin fahimci zancen nawa!ko kuma sae na qara miki wani," da sauri taja baya tana kuka don ganin da gaske yake, tace "to shine zaka wani mareni wlh sae na gaya ma umma!
daga haka ta tafi da gudu tana kuka ta haura sama.
Duk da Man ya fahimci Nasir yana buqatar jin bayani bai tsaya yi masa ba ya tafiyar sa hakan yasa nasir ya tafi ya haura sama gun matarsa da shima ya fahimci gidan inna taje bai sani ba.

Da shigarsa ta taso ta rungume shi tana kuka tace "ka gani dai ko honey ban masa komai ba yazo ya mareni," mugun kallo yyi mata yace "bana son qarya pretty nasan halin Man ba zai zo haka kawai ya mareki ba ,ba makawa gidan inna kika je gun Rayyanat kika aiwatar da nufinki ko?" shiru tayi alamar can taje d'in, nn ya shiga yi mata fad'a sosai daga qarshe yace duk ta qara fita bada izinin sa ba sae ya sanar da Abbanta, fushi ta shiga yi dashi bai kula ta ba ya tafiyarsa yaci abinci ya fice daga gidan.

Gidan inna ya nufa yaje yaga aikin da pretty tayiwa Rayyanat lokacin ma har likita ya xo ya dubata, bata wani kone ba sae dae fatar jikinta da yyi ja ssae.
Sosai ya bata haquri daga ita har inna da abun yabi ya dama har tana cewa a kira mata kabiru, Nasir dae ya dinga bata haquri yace shi zai yi maganin abun amma fafau inna tace ita fa sae taje shima zai kaita gidan da kanshi.

Haka ko akayi dmn tare suka fita shida inna suka bar Rayyanat ita da hurera.

Wani makeken gida suka nufa kyace gidan shugaban qasa ne kan tsari da kyawo irin nashi, kuma ba wani gida bane face gidan su Nasir d'in da kuma su pretty wato qanwar man sbd gabad'ayan su family's ne en wa da qani ne,
Baban su Man shine babba snn mahaifin Nasir bayan shi kuma akwai wani Alhj sa'eed wato qanin mahaifin Nasir inda shi kuma yana da qanwa mai aure a garin kd dukkan su 'yayan inna ne shine maxan suka had'e kansu suna zama gida d'aya sae dai kowa da nasa 6angare.
Suna shiga gidan
inna ta nufi 6angaren su pretty sae ga wata yarinya tazo da murna ta tarbe ta tana fad'in "he inna nida nake batun zuwa gurinki shine kika zo, inna ta washe baki tace "tukuna saukar yaushe Ameera? Yau yau d'in nan aka bamu hutu inna ,to ina er uwar taki saliha? "Tana 6angaren su tare ma ne zamu tafi gurin ki nasan yanzu haka ta shirya tana can tana jirana wlh, inna tace "ayyo to ai yanzu komawa zanyi sae mu tafi tare je kira min Abbanku kabiru yazo ina da magana dashi, tace "to inna zauna na kira miki shi"inna ta zauna ita kuma ta haura sama.
Chapter 6 · 0% Book details