← Book details Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 112

Sashe 33

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Fa'iza tace"hm laila, ni mijina ma da sae ya min kuka nake barin shi....nn wyr malika tayi qara ta kalli fa'iza tace"kinga tafiyata my man ya dawo ,
tace"to yayi sae nazo a gaida shi tace"to snn ta d'aga wyr ta fita.

Rynt kuwa koda qarfe hud'u tayi ta gama shirin ta tsaf sae jiran mae lesson take amma shiru har aka qara minti goma sae ga man ya shigo d'akin yace da Rynt"zo ga mai lesson d'in naki yazo"ta taso zata fita ya kalle ta shaye da toka yace"bana son raini
fuskar ki zai karantar ko ke!
da zaki wani je masa fuska sake ba niqabi"
Tace"wae nikam meyasa kake son takurani ne kace komai sae nasa niqab"
Yace"kika dae takura kanki ai na gaya miki tunda kikayi gigin amincewa aurena baxa ki ta6a jin dad'i ba,rayuwarki da mami ne yasa nake d'an sauqaqa miki ba wae don wani abu ba!
Don hk ki tabbatar kin saka niqab kafin ki tafi idan ba hk ba kin haramta da lesson d'in gabad'aya!
Nn ya tafi ya varta tsaye ta ta6e baki tace"auren naka in banda qaddara me ma zai sa na amince ko yanzu cikar burina kad'ai nake jira na fecewa aurenka"
Taje ta ciro niqab ta saka snn ta fita.

Man na zaune ake mata lesson d'in hkn yasa yaga yanda Rynt keda saurin fahimta duk da cewa hnklin sa ba duka yana kansu ba sbd wani aiki da yake a laptop.
Sae da ana kusa fara kirayen kirayen sllr magrib mai lesson d'in ya tafi.
Ita kuma ta tashi zata tafi kenan man ya tsaida ta yace"gaya min kalmar da na koyadda ke a d'azun "sae da ta kauda kanta gefe snn tace"retype"ya d'an d'ago ya kalleta snn yace jeki.

Bayan sati d'aya da faruwar haka fhmtar Rynt sae qaruwa take akan lesson d'inda ake mata don yanzu ta fara fhmtr wasu kalmomi na turanci da ake fassara mata su zuwa hausa,hkn kuma akan nuna mata yanda ake ftr da sautin kowane harafi da kuma sauran abubuwa da dama.
Mohd kuwa duk za'ayi mata lesson sae yazo yayi zaune a falo sae ya fake da wani aiki ne yake kan laptop hkn bai hana Rynt ta kasa sakewa ba a gurin lesson d'in sbd sosai take son ta fahimci komai ko don yanda a class take jin ana fad'in wasu kalmomi da dama na turanci da bata san su ba.
Gefen islamiyya kam Alhmdlh bata da wata matsala gurin, kuma still tana ci gaba da maida hankalinta sosai akai.

Ko yanzu ma lesson ake mata man na zaune yana aiki da laptop d'inshi .
Yatsun sa na kan laptop amma sae kallon Rynt yake sbd yanda ta bada dukkanin hnklinta akan lesson d'inda ake mata da kuma wasu tambayoyi da yaji an mata ta bada amsa kai tsaye.
Can Rynt taji a jikinta ana kallonta hkn yasa ta d'ago sae kawai ta sami idanuwanta a cikin nashi still bai daina kallonta ba sae itace ta maida hnklinta ga lesson yayinda kyawawan yatsun ta ke riqe da marker ta fara rubutu akan whiteboard d'inda ke gabanta zata had'a sentence akan wata kalma da lesson teacher d'in ya bata ta rubutu sentence akai dmn yaga idan ta fahmci ainihin inda ake saka kalmar a cikin magana,kmr yanda ya mata bayani.
Shiyasa man ya kasa d'auke idonsa dmn yaga shin zata iya.
Tsaf kuwa Rynt ta had'a sentence ba wani gargada ko shirme a ciki, qoqarinta man ya gani ba don komai ba sae don sanin ba wani gud foundation ta samu ba amma gashi tayi trying much better akan lesson d'inda ake mata da ba'a wani jima da farashi ba.
Numfashi ya ftr a hnkli had'e da maida duban shi gun laptop yayinda su kuma suka ci gaba da lesson d'insu.

Washe gari da qarfe kusan uku malika ce zaune a falo ita kad'ai tana jujjuya wasu ruwan gora dake hannunta nn wayarta tayi qara ta d'aga wyr tare da tashi ta nufi fridge d'in falon ta saka gorar a ciki snn ta nufi d'aki ta d'auko mayafinta ta fita.

Ba jimawa sae ga Rynt ta fito falon riqe da magani a hannunta zata sha sbd kanta da taji yana d'an mata ciwo gashi to 4 mai lesson d'inta zai zo.
Tana bud'e frigde d'in sae ga man ya shigo gidan ya nufi fridge d'in ya buga tsaki ganin gorar ruwa qwara d'aya wanda tun jiya ya kamata ace ya siyo ruwa a gidan amma sae gashi yau ya fita ya manta.
Ya kalli Rynt tare da fad'in "ke kin gyara min d'akina kuwa? Tace" bana jin dad'i ne amma yanzu zan tafi idan nasha magani "
Yace"kin fara ko? tace"nifa ba hk bane kuma kasan bana iya gyara d'akin naka ba kowa a ciki, mami ce ke tsaya min kuma bacci take tun d'azu amma idan zaka tsaya min zan gyara maka ynz"
Bai ce mata komai ba sae gorar ruwa ya jawo ya tsiyaya mata ruwan a cup ya bata snn shima ya tsiyaya ma kansa yasha.

Malika na cikin mota ita da qawarta fa'iza tana driven zasu tafi kasuwa sae fira suke malika ta katse firar da cewa"oh my goodness!fa'iza na manta na saka gorar ruwana a fridge d'in falo a maimakon nakai d'akina"fa'iza tace "to meye matsalar ko gidan naku tsiyar ruwa ake yi ne"
Cikin ba'a fa'iza ta fad'i mgnr ,malika tayi murmushi tace"ba haka bane desire tablet ne a cikin su kuma mai qarfin ne da sae dare nake shan shi idan zamu kwanta nida my man.
Fa'iza tace"to ai sae ki bari idan kin koma kya cire"
Malika tace" Eh dama ai"

Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[10:00PM, 5/2/2017] Billy giro😊: [ 1/27/2017]

🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮
Chapter 33 · 0% Book details