Sashe 2
Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Sae guraren qarfe biyar mahaifin ta ya dawo yayinda fuskar shi take cike da damuwa.
Rayyanat taje a natse cikin murna tana tarbon mahaifin ta inda ta kai hannu ta d'auke fartanyar da ke kan kafad'ar sa ta kuma d'obo ruwa ta bashi,
bai sha ruwan ba sae hannun sa ya tara ya wanke ya zauna a sukwane tare da dafe kan shi.
Rayyanat da ko kad'an bata son ganin mahaifin ta cikin damuwa nan take idanun ta suka ciko da qwallah ta durqusa a gaban shi tare da jaye hannayen sa da ya dafe kansa.
Muryar ta na rawar kuka tace "me yake faruwa ne Baffa dan Allah ka sanar da ni"
A hankali mahaifin ta ya d'ago idanuwan sa da sukayi jajir ya goge en guntayen hawayen da ke gefen su yace"Rayyanat na kasance bani da wani buri a rayuwa sae don ganin na faranta miki hakan yasa tun lokacin da mahaifiyar ki ta rasu ta barki kina jinjira naqi nayi aure don kawai kar ki shiga quncin rayuwa domin bansan matar da zan auro wace iri bace shiyasa na haqura da aure gavad'aya sbd zan iya zamowa auri sake idan har na had'u da matan da ke quntata miki ni kuma bana son kasance wa haka kuma gashi bani da wasu en uwa da zan kaiki a gurin su shiyasa na za6i na raine ki da hannu na,yayinda na zame miki tamkar uwa na kuma so na kasance uban da ba wani abu da zaki nema ki rasa amma talauci bai bar na miki haka ba kiyi haquri Rayyanat da na kasance uban da kullum sae kin nema kin rasa ba yin kaina bane wannan jarabtar ubangiji ce wacce a kullum nake roqon Allah ya kawo muna qarshen ta muna masu lashe jarabawar ba tare da mun sa6a masa ba.
Rayyanat nasan ke 'yace ta gari zaki fahimci abinda nake nufi da kuma abinda zan fad'a a yanzu.
Rayyanat a yau zamu kwashe komatsan mu mu koma daji da zama can gurin gonar mai gari da nake masa noma....Baffa me yasa zamu koma inda ba kowa ?dole ne Rayyanat sanin kan ki ne wannan gidan ba nawa bane kuma bani da wani gida na kaina haya muke kuma sanin kanki ne duk wata na kanyi qoqarin ganin na biya kud'in haya koda kuwa su kad'ai ne suka rage mana na abinci amma a yau Bala yaje har gurin mai gari yakai qara ta kan cewa bana biyan shi kud'in haya wai har ma yana bina na wata biyu naqi na biya shi, duk da cewa nayi ma mai gari bayanin cewa ba gaskiya ya fad'a ba amma mai gari ya zare kud'in noman da nake binsa na wata d'aya ya bawa Bala na zamo bani da ko sisi kuma Bala ya nemi na bar masa gida wai yana so zai saka wad'an da ke biyan sa duk wata.
Ba irin haqurin da ban bashi ba amma yaqi shiyasa mai gari yace idan har zan iya ya bani dama naje can kusa da gonar shi na haqa bukka mu riqa zaman mu a can tunda ba wasu namun dajin da ke cutarwa a gurin.
Cikin kuka Rayyanat tace"Allah yasa haka shi yafi Alhairi Baffa"Amin Rayyanat bari naje cikin gari naga ko zan sami wani aikin da zanyi a biyani mu samu abinda muka ci kafin mu kwanta"
Kallon mahaifin ta tayi kafin take share hawayen da ke kan fuskar ta tace"Baffa akwai rogo da Sarat ta kawo min ka bari kaci tukun ko zaka fita"
Aa Rayyanat ki dai ci in yaso idan Allah yasa nayi nasara sae mu qara cin abinda ya samu,, Baffa rogon fa mai yawa ne kuma tun safe na ajiye shi sae kazo muci tare,,,girgiza kansa yayi yayinda yake qara jin son er shi sbd yasan halin Rayyanat komai qanqantar abu bata yarda taci ita kad'ai sae tare da shi.
Nan ya dafa kanta yace"Allah yayi miki albarka Rayyanat ya kuma sanya nasara da albarka a cikin al'amurranki ya kuma sauya miki wannan rayuwa da muke ciki ma'ana nan gaba kad'an ki kasance cikin wadata da walwala had'e jin dad'i mai d'orewa har izuwa qarshen rayuwar ki"Amin Baffa na gode.
Nan ta d'auko musu rogo suka ci bayan sun kammala ta d'auko ledar da Anwar ya bata ta bawa Baffan ta ba tare da tace da shi komai ba yace"Rayyanat daga ina wannan ledar ta fito? Cikin jin kunya ta duqar da kanta ta kasa cewa komai wanda hakan yasa nan take ya fahimci inda ledar ta fito yace"Anwar ko sun tafi kenan? Eh sun tafi tun d'azu ,,to Allah ya kiyaye hanya ,,Amin Baffa,,tace"Baffa kayi haquri ban kar6a ba sae don ya had'a ni da Allah"ba komai kuma ai ba a maida hannun kyauta baya.
Nan Abban ta yace ta bud'e kayan koda ta bud'e kala biyu ne masu kyau less da atamfa kuma da hijab kala biyu wato kalar kayan sae takalmi taki d'aya da kuma tokar wanka mai had'e da set d'in turare sae wata envelope da aka d'ora akai wacce ta bawa Baffan ta tace shi zai bud'e sbd tana ganin kamar kud'i ne a ciki koda mafahaifin ta ya bud'e en dubu dubu ne sabbi dal har dubu biyar sae wani tsadadden zoben azurfa black an white da wata er guntuwar takarda soke a cikin zoben.
kasa had'a ido tayi da Baffan ta yayinda yake miqa mata kayan bata kar6i kud'i ba sae zobe ta kar6a had'e da takarda tace"Baffa ai a gurin ka kud'in ya kamata su kasance da kuma wad'anan tufafin"Rayyanat ki ajiye komai a gurin ki sbd kinga fita zanyi naje naga gurin da ya kamata mu haqa bukka na fara aikin kafin gobe sbd tun da safe yake so mu bar gidan"
Baffa muje na taya ka ba musu yace "to adana kayan muje"
kwalla taje ta bud'e ta saka kayan suka fita.
Da suka fita basu suka dawo ba sae yamma liqis.
Da dare Rayyanat bata iya bacci ba sae da ta d'auko wannan takardar ta fara karantawa kamar haka
*_"Rayyanat ina so ki saka wannan zoben a yanzu kuma kimin alqawari baza ki ta6a cire shi ba har abada domin cire wannan zoben tamkar kin cire ni a cikin zuciyar ki ne_*
Murmushi ne ya bayyana a fuskar ta yayinda take sanya zoben inda ta rufe idon ta a hankali tace"
*_yaya Anwar nayi maka alqawari wannan zoben ba zai ta6a fita a yatsa ta ba sae dai idan mutuwa nayi aka cire shi_*
Daga haka ta kwanta sae kallon yanda zoben yayi matuqar kyau a yatsan ta take har ta shiga magana a ranta cewa
_"Da ace ko mutuwa nayi baza a raba ni da zoben nan ba da nafi kowa farin ciki"_
Yaya Anwar ina ma ace zoben nan mai 6acewa ne da na bashi umarnin ya 6ace a lokacin da na mutu har akaini makwanci na don dai kawai ya kasance ina tare da kai a duk inda nake ko da yake ko ba zoben nan kana tare da ni sbd kana cikin zuciya ta ba kuma zan ta6a iya fitar da kai ba kamar yanda hanta bata iya rabo da jini.
Tana maganar ne a fili cikin natsuwa tamkar anwar na kusa da ita.
Washe gari tun da asuba ta had'u da mummunan labari su Anwar sunyi had'arin mota kuma ba wanda ya rayu a cikin su kuka taci tamkar ranta zai fita Baffan ta kuwa sae bata baki yake yana aikin rarrashi.
Suna cikin haka ne Bala yazo cike da masifa yasa aka yi ta fitar da kayan su ana watsi da su wanda hakan ya qara sa Rayyanat cikin wani yanayi ganin yanda ake wulaqanta mahaifin ta da ke ta ba Bala haquri kan su daina watsar musu da kaya bai saurare shi ba sae da suka fitar da kayan kaf tare da jan hannun Rayyanat suka ingiza ta waje wacce ta kasa yin komai sae kuka .
Mahaifin ta ne ya kama ta ta tashi sbd fad'uwar da tayi garin ingiza ta da akayi har ma suka fasa mata baki.
Nan suka fara kwasar kayan su suna zubawa a cikin wani tsofon baro da mahaifin ta yayi yayin tallar ruwa a ciki wanda maya biyu sukayi suka gama kwasar kayan na su hakan yasa basu koma cikin gari ba sae qoqarin ganin sun qarasa bukkar da suke su samu su zuba kayan su.
Bayan sun kamalla ne mahaifin ta ya zauna yana qara bata baki kan tayi haquri da komai na duniya sae haquri kuma mai wuce wa ne amma Rayyanat tamkar mahaifin ta na qara mata qarfin kuka ne domin da zarar ta kalli zoben da ke kan yatsar ta sae ta sake fashewa da wani sabon kuka .
Haka Rayyanat tayi sati tana kukan rashin Anwar da Sarat duk tabi ta rame ta zamo tamkar ba ita ba,sae dai yanzu suna samun d'an abinda suka ci ta hanyar amfani da kud'in da anwar ya bawa Rayyanat.
Yau kusan wata biyu kenan da komawar su jeji tun Rayyanat na tsoron zaman jejin har ta saba sae dai har yañzu mutuwar anwar bata sake ta ba bcs duk lokaçin da ta kàlli zoben da ke kan yatsar ta sae ta zubar da qwallah.