← Book details Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 112

Sashe 49

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Rynt kuwa sae karatun ta tasa ma gaba wacce ko yanzu zaune take a d'akinta ta tasa agwalima gaba tana sha yayinda take duba littafan mkrntar ta na boko dana islamiyya ,
kasancewar yanzu ta gyara d'akinta ta dawo ciki da zama sae bacci ke kaita d'akin inna.
Tana cikin duba littanfanta ne taji inna na qwala mata kira taje ta sami inna a falo inna taba ta waya tace"nasiru ne wae ki gaya mae abubuwanda aka ce ku siyo a makrnta.
Nan ta kar6i wyr ta snr dashi snn taba inna wayarta ta koma d'aki taci gaba da duba littafanta.
Ba ita ta tattara littafan ta ajiye ba sae da ta soma jin bacci duk da cewa dare bai wani yi sosai ba don qarfe tara ne a lokacin.
Bathroom ta shiga tayi wanka ta fito tayi shirin bacci cikin riga da wando ta zuba qaton hijabinta ta fito riqe da agwalimar ta guda biyu a hannu.
Nan ta had'u da Nasir ya fito d'akin inna zaije d'akinta hannun sa riqe da farar leda mai hoton littafai da kuma al'amin bookshop a rubuce ta gaida shi ya amsa tare da miqa mata ledar yace "duba kiga littafan ne "
Ta duba tace "eh sune nagode"
Har ya juya zai fita sae kuma ya juyo ya kalleta tayi saurin sadda kanta qasa yace"ki qara hqr kwana biyu kinji ni shiru har yanzu ban sami kaina bane"
Tace"ba komai yaya ai ka barshi kawae sae ka sami lokaci"
Yace"to sae da safe"
Snn ya fita ita kuma taje ta ajiye littafan a d'akinta taje d'akin inna.
Da shigarta ta bud'e fridge ta saka agwalimar ta a ciki.

Washe gari an sauke Rynt a makaranta sae dube dube take ta inda zata hango mami sbd kwana biyun nn duk suna had'uwa da safe idan an sauke su.
Tana cikin dube dube ne sae ga mami ta shigo gate d'in mkrntar da gudu Rynt ta saki murmushi taje ta tarbota tana mae fad'in"wnn gudu haka mami ba kya tsoron kije ki fad'i"
Tace"Anti sauri nake kar baki ganni ba ki tafi don na hango lokacinda aka sauke ki mu kuma muna baya da nisa har ma nayi ta kiranki baki ji ba,
to kince da nisa ya zan jiki mami,
Mami bata ce komai ba sae lunch box d'inta ta ajiye qasa snn ta ciro school bag d'inta dake bayanta ta bud'e ta ciro er wata container rubber mai marfi taba Rynt tace"umma tace na kawo maki"
Rynt ta kar6a takai hannu a hnkli ta bud'e.
Wacce tana bud'ewa qamshi mai dad'i ya daki hancinta nn taga
awara ce wacce taji cabbage da albasa bayan sauce d'in hantar rago da aka zuba akai mai had'e da kayan lambunda aka yanka su slice by slice ta yanda kallo d'aya zakayiwa awarar ka sami kanka da tsinkewar yawu.
Cikin nuna jin dad'i ta rufe snn ta kalli mami tace "kice ma mama nagode sosai kinji"
Mami tace"yauwa anti nifa har yanzu bamu je kasuwa ba bare naga raqumi ya shiga akurki,idan ma nayiwa umma magana se dariya kawae take min,ta qarashe mgnr ne shaye da toka.
Rynt tayi murmushi tace"umma da kanta take miki dariya"
Tace"eh mana"
To yi hqr jeki kar a fara maku assembly"
Daga hk kuwa sukayi wa juna bye bye suka wuce.

10:00pm
Man ne zaune kan bed ya rufe laptop d'inshi ya d'aura kan bedside drawer ya kwanta sae ga malika ta shigo d'akin taje ta kwanta kusa dashi had'e da kai hannu tana shafa sajen fuskar shi har izuwa qirjin shi,
kallonta yayi tare da janye hannunta daga kan jikinshi ya kashe wuta had'e da juya bayan shi,nn yaji ta matso gab dashi ta rungume shi ta baya
yace"pls malika bana son damuwa kin sani,ki matsa kusa dani bana son jinki a bayana.
Kmr kazar da qwai ya fashewa ta jaye jikinta daga nashi.

Billy Giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[10:00PM, 5/2/2017] Billy giro😊: ```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```

🔮🔮🔮🔮
*page* *```50```*
Washe gari guraren qarfe goma na safe mohd ne ya fito daga bathroom sanye da white bathrobe wanda kai tsaye gun wardrobe ya nufa ya ciro black suit ya ajiye kan bed yayinda malika ke kwance akan bed d'in tana ta sharar bacci.
Bayan ya gama shirin sa tsaf ya d'auki makullin motar sa ya fita,ya bud'e motar sa zai shiga knn sae ga driver yazo byn sun gama gaisawa ne yake cewa "yalla6ai lafiya kwana biyu naga mami da yayarta basa fitowa zuwa mkrnta ko anyi hutu ne banida labari?
Ba tare da yako kalle sa ba yace"sunyi tafiya ne"
Daga hk kuma ya shigewar sa mota yaja ya tafi.

Yana shiga office wayar sa ta shiga ruri ya ciro wyr a aljihu ya d'aga tare da fad'in"Aamil ya akayi ne"
Daga d'ayan 6angaren yace"man muna son zamu shigo 9ja ne but no actual time,bcs akwai wani aikin da Amir keson qarasawa da sae idan ya kammala shi ne snn ko zamu zo,but idan mun zo d'in wnn karon ba a gida zamu sauka ba a gidajen mu zamu sauka shine muke son kasa a fara gyara mana gidajen sbd may be gyaran zai d'an d'auki lokaci kan irin yanda aka jima ba'a shiga gidajen ba,if ma gidajen na buqatar canjin komai pls duk kasa canza a mana.
Man yace"ok naji ka gaida Amir bye"
Daga hk ya katse wayar yaje ya zauna kan kujerar sa mai shillo tare da kai hannu kan landline ya latsa lambobi ya kira, ba jimawa sae ga wata er kyakkyawar farar yarinya ta shigo da bazata wuce 22 yrs ba d'auke da teacup n saucer a hannunta taje kan desk ta ajiye masa snn ta juya ta fita.
Mohd dake latse latse da laptop d'insa yakai hannu a hnkli kan teacup d'inda ke kan saucer ya d'auka had'e da kai bakinsa yana shan tean da ke ciki yayinda yake ci gaba da latse latse da d'ayan hannunsa.

Malika kuwa tunda ya barta ba ita ta farka ba sae 12 wacce da tashin ta ta fad'a bathroom tayi wanka ta fito taje d'akinta ta shirya kafin take sa cleaner ya gyrawa mohd d'akin shi.
Bayan ta gama shiri ne tazo downstairs tayi breakfast taje kan 3seater ta kwanta sae chat take.
Sae jin tayi an fizge wyr tayi saurin tashi zaune had'e da kallon wanda ya fizge wyr.
Qawar ta Fa'iza ce ta gani tana mata dariya itama dariyar ta mata snn tace"yau kuma bazata kika min"
Tace"wlh kedai kan hanya muke nida hubby zamu je gidan su shine nace ya d'an biyo dani nn mu gaisa mun kwana biyu bamu had'u ba tun asibiti"
Malika tace"aini fushi ma nake yi dake wae ace tun asibiti ba waya ba text ba chat"
Sae da Fa'iza ta nemi guri ta zauna kusa da ita snn tace"wlh banji dad'i bane kwanakin nn shiyasa banida lokacin waya don kashe ta ma nayi sae yau na kunna"

Malika tace"eyyah to ya jikin?
Allah naji sauqi sosai ya man da haqurin rashin babyn shi da yake fama?
Malika tayi er dariya snn tace"in gaya miki har yanzu ya kasa haqura ya cire abun a ranshi har ma baya son damuwa kwata kwata he is so lonely.
Fa'iza tace"lallai yana son baby sosai sae ki hanzarta ki samar mai wani "
Tace"Hm ba yanzu ba sae mun gama baje soyayyar mu tukun"
Fa'iza tace"ta bayan fa da akayi?
Aikin san wnn soma ta6i ne ga kuma wnn abar wacce duk da nasan ba kulata yake ba amma idan na tuna cewa wae mtr my man ce sae na nemi farin cikina kaf na rasa but now nsn cewa ni kad'ai ce nayi waje da matsiyaciyar banida wata damuwa sae hln damuwa da my man d'ina yake ciki a yanzu wanda ko shi na d'an kwanaki ne zai ajiye shi mu dawo normal.
Fa'iz tace"hkne kam kinga bari na tashi naje nabar hubby shi kad'ai a mota"
Nan malika ta tashi taje har mota ta rakata suka gaisa da mijin fa'iza snn ta dawo.
Chapter 49 · 0% Book details