← Book details Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 112

Sashe 87

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Taje ta riqo hannun sa ya juyo yana kallon ta tace"MK ina zuwa kuma baka ci abinci ba?
Yace"zanje inda za'a bani ba tare da na roqa ba"
A nn tayi saurin sadda kanta qasa d'auke da hawayen da suka cika mata ido don sae taji wani irin kishi duk da taga yanda suka kwashe shida malika a airpot.
Murya can ciki tace"yi haquri muje na baka"
Yace"tafi kawae kici inda kike son ci d'in ni ki barni na tafi abuna"
Hawayen da suka cika mata ido ne suka silalo a hnkli ta share hawayen jiki sanyaye ta juya zata bar gurin,
Jiki sanyaye mohd ya riqo ta yace"meye na kuka kuma Ryynt inace kinfi ra'ayin kici abincin a tare da su shiyasa nace ki tafi"
Ryynt tace"Allah ba wani nn fushi kayi "
Ya janyo ta zuwa jikin sa yace"to yi haquri kuma ni ba fushi nayi ba dama na gwada ki ne kawai inga ko kina son mijinki da gaske sae naga ashe ke dad'i miji ce da ba kya son ganin fushin sa.
Da wasa ta sha toka tace"me kake nufi?
Ya d'aura mata kiss kan lips yace"abinda kika fahimta shi nake nufi"
A shagwa6e ta maqale kafad'a tana doka qafafun ta qasa tace"wlh Aa ni ba dad'i miji bace"
Ya lakato hancinta tare da fad'in"ba wani nn na gano ki ae"
Kuka ta fashe dashi ta shiga kai masa duka irinta ta shagwa6a tana fad'in"wlh Aa ni ba dad'i miji bace"
A nn Mohd ya shiga kare dukan sae dariya yake ita kuma sae ci gaba da dukan sa take tana fad'in ita ba dad'i miji bace shidai ne haka ba ita ba nn ya kama yatsan ta ya gantsara mata d'an qaramin cizo ya gudu ya barta sae kukan shagwa6a take tana yarfi da hannu yaje kan darduma ya zauna tabi shi ta kama yatsan sa ta rama ya shiga yarfi da hannu sae dariya take masa dan da gaske ta cije shi, ganin zae kama hannun ta ya rama ta tashi da sauri ya biyota dai dai inna ta fito taje bayan inna ta la6e sae gwalo take masa tañà dariya.

Sorry 4 dis one

Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[10:05PM, 5/2/2017] Billy giro😊: ```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```

🔮🔮🔮🔮
*page 79*
Nan mohd ya shiga qoqarin ganin ya janyota inna bata barshi ba sae fad'in take wae muhammadu lafiyarka?
Yace"Inna cizo na fa tayi"
Ryynt tace"wlh inna shine ya fara ni kuma na rama"
Ta qarashe mgnr tare da yi masa gwalo bata ankara ba sae ganin tayi ya jawota tace"wayyo Allah yi haquri inna zae rama dan Allah ce yayi haquri bazan sake ba wlh"
Inna taje zuwa qwace ta mohd yace"inna wlh ba abinda zan mata abinci zamu ci"
Ryynt tace"inna ba wani nn ramawa zae yi"
Ta fad'i hkne yayin da take yunqurin komawa ga inna amma bata iya ba dan man sae d'aukar ta yayi cak tana wuntsil wuntsil da qafafu har yaje da ita kan darduma nn inna tayi murmushi had'e da girgiza kanta ta tafi ta basu guri dan ta fhmci mohd ba kunya ne da shi ba.
Ryynt kuwa cikin fushi ta kalle sa tace"wae meyasa kake min abubuwan da kake sa ina jin kunya dan Allah ban so ka daina"
Ta qarashe mgnr cikin muryar kuka mohd ya d'aura mata kiss kan lips yace"to naji yi hqr muci abinci"
Ta tashi tare da fad'in"banci"
Mohd ya riqo ta ta buge masa hannu yayi saurin kama hannun nasa had'e da fad'in "Ash!
ya yaye hannun rigar sa wata irin babbar yankuwa ta bayyana yayinda hannun farar rigar sa ta ciki duk ta lalace da jini.
Da sauri Ryynt ta koma ta zauna ta riqo hannun sa tana kallon gurin ta kalle sa idon ta tap da qwallah tace"mk me ya same ka haka?
Bae ce mata komai ba sae kallon yankuwar yake yana tuna lokacinda yaja malika zae kaita d'aki ne wuqar hannunta ta yanke sa garin fizge fizgen ta.
Ya kalli Ryynt wacce duk ta rud'e tana basa haquri had'e da tambayar me ya same shi .
ya shafo fuskarta yace"d'an wani tsautsayi ne ya same ni d'azun da na fita amma kar ki damu kinji"
Ryynt da hawaye suka silalo kan fuskarta ta kalle sa tace"wnn ne d'an jifa yanda yankuwar tayi babba sosai warkewar ta ma zae yi wuya"
Ta qarshe mgnr ne cike da son fashewa da kuka.
Mohd da saurin kukanta ke bashi mamaki gashi baya son ganin kukan nata ko kad'an ya janyo ta zuwa jikin sa yace"don't cry mana Ryynt jikina baya da matsala take naji sauqi kar ki damu kinji"
Ryynt ta d'ago tare da share hawayen ta ta tashi tare da fad'in "to ina zuwa"
Ya maida ta yace"no yi zamanki bana so inna ta sani"
Tace"ba gaya mata zanyi ba first aid case zan d'auko"
Yace"yi zamanki kawae idan na fita zanyi dressing d'in gurin don idan inna taga kin d'auko first aid kit d'in dole zata nemi dalili"
Ryynt ta gyad'a masa kai tana kallon yankuwar da ya maida hannun rigar sa ya rufe.
Ya sakar mata murmushi yace"to muci abinci koh"
Fuskar ta cikin damuwa ta bud'e plate suka fara cin abincin tana bashi yana bata har suka kammala cin abincin.
mohd ya tashi zuwa sllr magrib.
Ita kuma ryynt sharp sharp ta kwashe kwanikan abincin ta kai kitchen snn ta tafi d'akinta ta sami su saliha tuni sun kammala cin abincin su,
Saliha na bathroom gurin yin arwala mami kuwa sae fmn game take da game tap d'in ta.
Ryynt ta kar6e game tap d'in ta kashe tace"mami ana yin kirayen kirayen sallah kina yin game ki daina ba kyau kinji"
Mami ta washe baki tace"to Aunty na daina amma yaushe zamu koma gidan yaya"
Ryynt tace" idan kun koma gida ki gaya ma umma a had'a maki kayanki idan zan koma sae mu koma kinji"
Mami ta daka tsalle ta rungume Ryynt tace"da gaske Aunty?
Ryynt tayi murmushi tare da gyad'a mata kai.
Sae ga saliha ta fito daga bathroom Ryynt ta tashi ta shiga.

Sae da suka ida sllr magrib da d'an jimawa Nasir yazo ya kwashe su ya maida su gida.
Ryynt kuwa d'akin inna taje sae firar bayan rabuwa suke cike da nishad'i.
Chapter 87 · 0% Book details