← Book details Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 112

Sashe 65

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rynt kuwa tana cikin baccinta mae dad'i taji inna tana qwala mata kira ta tashi firgigit tana kallon inna da ta shigo d'akin snn ta kalli inda take kwance tana d'an dube dube a d'akin inna tace"me kike nema ne?
Tace "ba komai"
Inna tace "to tashi muje d'aki ki kwanta ko"
Ba musu Rynt ta tashi had'e da d'aukar wayarta da kuma littafinta da suke da jarrbawar sa gobe don tana son da dare idan ta farka tayi karatu.
Nan suka rufo d'akin suka fito wacce da shigar su d'akin inna ko hijabin jikinta bata iya cirewa ba ta fad'a kan bed ta ci gaba da baccinta.
Ba ita ta farka ba sae
11:40pm ta tashi a hnkli had'e da bisimillah tana miqa taje bathroom bata jima ba ta fito ta koma kan gado ta zauna tare da jawo littafinta ta kunna fitilar wayar ta tana karatu.
Tana tsaka da karatun ne wayar ta ta shiga qara tayi saurin sakata a silent tana kallon numbar da ke yawo akai, d'auke da mamaki a fuskarta na ganin baquwar numbar da bata sani ba kuma da daren nn.
Kiran na gab da tsinkewa ne tayi saurin d'aga kiran dan a take ta shiga tunanin ko Sarah ce.
Sae dai duk da hkn bai sa da ta d'aga wayar tayi magana ba se shiru tayi tana sauraren muryar da zata ji.
A natse taji ance "kin tashi?
Bata ce komai ba sae shan toka da tayi dan lokaci d'aya ta gane muryar mohd ce yayinda ta shiga tunanin a ina ya sami numbar ta,
ya katse ta da cewa"kina jina mijinki ne mohd ina son zanyi magana ta fhmta dake ne kinji"
Kmr yana ganin ta ta qara murtuqe fuska,murya can ciki tace"nifa ynx karatu nakeyi bani da wnn lokacin"
Yace"kun fara exam ne?
A qufule tace"eh"
Yace"olryt gobe zan kira ki idan kin dawo daga school"
Komai bata ce dashi ba ta katse kiran taci gaba da karatun ta.

Washe gari da yamma Rynt na zaune a falo ita da Aamil yana mata tambayoyi akan littafin da zasu yi exam next day.
Wayar Rynt dake ajiye gefe ta shiga qara Rynt ta kalli wayar kawae ta kauda fuskarta don ta fhmci numbar mohd ce Aamil dake kallonta yace"ya baki d'aga kiran ba?
Tace"ba komai kawae bana son in katse karatun da muke yine"
Bae ce komai ba suka ci gaba da aikin su har kiran ya tsinke aka koma kira Rynt ta kalli wayar had'e da kai hannu zata d'auki wayar se kawae wayar ta nuna battery low ta mutu hkn ya mata dad'i dan dama niyyarta tana d'aukar wayar katse kiran zatayi ta kuma kashe wayar gabad'aya.
Aamil da har ya soma jin haushin mae kiran dan hk kawae ransa ya basa cewa namiji.
Ya kalli Rynt kmr wanda zae ce wani abu sae kuma ya fasa suka ci gaba da yin karatun su kawae.

Bayan sun gama karatun ne ta saka wayarta a chaji da dare tana shirin bacci wayar ta ta shiga ruri tana ganin mohd ne mae kiran ta buga tsaki ta d'aga wayar had'e da fad'in"wae me?
Mohd yace"kan me d'azun na kiraki baki d'aga ba da qarshe ma dan kin rainani kika kashe wayar ko"
Komai bata ce ba sae tsaki da tayi ta kuma cillar da wayar kan bed taje taci gaba da shirin baccinta shi kuma se magana yake tayi ba amsa har sae da ya gaji ya tsinke wayar.
Sae da ta gama shirinta tsaf snn ta d'auki wayarta ta fito ta rufe d'akin ta tafi d'akin inna.
Washe gari da safe ta fito daga wanka knn mohd ya kirata kallon wayar kawae tayi ta kauda kai taje ta jawo Vaseline tana shafawa , tana ji har yayi kusan 3 missed calls bata d'aga ba wacce tana gama shirinta ta kashe wayar ta jawo drawer ta saka wayar a ciki snn ta d'auki school bag d'inta ta bar d'akin taje d'akin inna tasha fura a gaggauce ta fita.

Mohd kuwa rashin d'aukar wayar Rynt ba qaramin 6ata masa rae yayi ba shiyasa tun daga rnr bae sake d'aukar wayarsa da sunan kiranta ba har kuwa aka kwashe kusan sati d'aya sae harakar gabansa yake haka ma Rynt wacce yanxu wata irin shaquwa ce ta ban mamaki ta shiga tsakanin ta da Aamil wanda yanzu shi ke kaita school ya kuma je ya d'auko ta wani lokacin ma har d'aukar ta ya ta6a yi suka je shopping da dare ya kwaso mata kaya niqi niqi tamkar bai ta6a sanin meye zafin kud'i ba inna dae sae kallon su take dan duk a tunaninta Aamil tausayawa Rynt ne kawae yake.

Rnr litinin da yamma Man ne tafe cikin mota shida Amir yayinda Amir ke cewa"gsky man ka fiye gajen haquri dan kawae ka kirata taqi ta d'aga sae kawae ka fita harakarta "
Man yace"hm Amir knn ta yaya kake tunanin zan iya fita harakarta bayan ina sonta ina kuma son abinda ke cikinta,just na bata lokaci ne har ta gama nata ikon kafin nake fara nawa ikon.
Amir yace"ta yaya yarinyar da ko saurararka taqi tayi?
Shiru mohd yayi dan baya son kowa yasan abinda ke ransa na d'auke Rynt da zai yi ya tafi da ita waje.
Amir kuwa bae sake ce masa komai ba har suka iso gidan shi ya bud'e gambun motar zai fita Man yace"ka shirya anjima byn sllr isha'i zan zo na d'auke ka ka rakani muje gidan inna"
Gurin Rynt zaka je ne?
Ba tare da ya kalle sa ba yace"eh"
Amir ya fita had'e da fad'in"sae ka zo"snn ya rufe gambun motar ,
man kuwa yaja motar tasa ya tafi.

6angaren su Aamil kuwa Rynt ce ya d'auko daga school ya kawota gidan inna ya ajiye ta wacce kafin ta fita motar sae da ta kalle sa d'auke da murmushi a fuskarta tana mae godiya shi kuma cikin sakiñ fuska ya lumshe ido had'e da ware su a kanta snn yace"ki gaida inna zan shigo anjima "
tace"to"snn ta tafi sae shillo take da ledar agwalimar da ke hannun ta wacce ya saya mata.
Aamil kuwa a maimakon yaja motar sa ya tafi sae kallonta yake tayi cike da tunanin yau zae kawo qarshen haqurin sa dan anjima idan ya dawo kai tsaye zai je ya gaya wa inna abinda ke ransa na game da Rynt koma kawae zae je ya sami Abba ya gaya masa dan inna tasan cewa lallai da gaske yake.
Da tunanin hkne yaja motar sa ya tafi.

Rynt kuwa tana shiga gida tayi wanka taci abinci tayi zaune a d'akinta ta tasa agwalimar ta gaba tana sha a nn ta miqa hannu ta bud'e drawer dan nn inda take zaune da drawer ba nisa ta ciro wayarta ta kunna sae kawae taji shigowar text murmushi tayi ganin Aamil ne ya turo saqon wacce ta san ba komai bane face kati don kullum sae ya turo mata katin dubu d'aya, hkn kuwa na mata dad'i sosai don sae ta kira en uwa da abokan arziki suyita waya wato Sarah da kuma umman saliha wacce bayan sun gama waya da ita sae ta bawa mami,suyi ta waya da Rynt cike da nishad'i suna dariya.

Da dare bayan isha'i Rynt ta idar da sallah ta miqe had'e da linke darduma ta saka a wardrobe ta kai hannu zata cire hijab bata cire hijab d'in ba sae tsaye tayi tana kallon cikin ta da har ya d'an fara turo hijab ,
a hnkli ta d'aura hannunta kan cikin sae kuma tayi saurin d'auke hannun ba shiri sbd motsa mata da taji yayi cikin takaici mai d'auke da alamar zata yi kuka takai hannu tana doka cikin.
Mohd dake tsaye a bakin qofa yana kallonta ya qarasa gurin ta da sauri har yana hard'e qafa ya riqe hannuwanta duka biyu ya kalle ta rae 6ace yace"kinyi haukane idan kika kashe abinda ke ciki fa"
Shaye da toka ta ture shi tace"dan ya mutu sae me ko ce maka akayi dama barin sa zanyi!
A fusace ya fizgota zuwa jikin sa yace"wlh idan har na koma jin kince zaki cire cikin nn zanyi mugun sa6a miki"
Tace"wlh sae na cire cikin nn kayi abinda zakayi"
Rufe bakinta keda wuya taji saukar duka a bakin nata wanda zama d'aya ya 6are da jini ,
sosai ta fashe da kuka tana kallon jinin da ta shafo a hannun ta.
Man kuwa sae farin handkerchief d'insa ya zaro zae share mata d'an jinin da ke gefen bakinta, ta buge masa hannu tana masa muguwar harara tare da fad'in mugu Allah ya isana wlh.
Ta qarashe maganar ne cikin muryar kuka sosai ,komai man bai ce mata ba sae janta yayi tana fmn fizge fizge har yaje da ita kan bed suka zauna taje zuwa tashi ya maida ta had'e da rungumeta yakai bakinsa saitin kunnen ta yana gaya mata magana cikin natsuwa, a nn ta d'ago ta kalle shi tace"da gaske kake yi"
Yace"eh"yayin da ya maida ta kan qirjinsa ya kwantar,sae ga Aamil ya fad'o d'akin ya tsaya da mugun mamaki yana kallon man da ya d'ago fuskar Rynt zai had'e bakinsa da nata yaga bata hana shi ba sae ma lumshe idonta da tayi har man yakai ga saka harshen sa a cikin bakinta.
Aamil cikin rud'u da kuma mamakin da yake d'auke dashi ya shiga ja baya har ya fita d'akin ya nufi d'akin inna dmn jin shin wace ce Rynt❓

Dan Allah Kuyi haquri da fmn jirana da kukayi tayi jiya kuma sae gashi baku samu ba .
Then
Ku qara min afuwa dmn gobe bazan samu yi ba sbd tafiyar da zanyi.
Luv u all❤

Billy Giro 😊
[10:00PM, 5/2/2017] Billy giro😊: ```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```
Chapter 65 · 0% Book details