Sashe 9
Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Abbas kenan anyi na farko, baza'ayi na biyu dani ba, bana son yi mata wulaƙanci ne amma taƙi ganewa, Soyayya kam sedai inga anayi, bazan sake ba, in Allah yayi zanyi Aure shikenan, Amma na gama Soyayya"
Abbas ya jinjina kai yace "shikenan Allah ya kyauta, na kiraka tun jiya bata shiga ya labarin mutuniyar ne?"
Shafa Aljihun sa Yusuf yayi, sannan ya jingina da jikin kujera yace
"Aini tun jiya dana dawo na kashe waya ta, bana son a dameni ne sam"
Abbas yace "kayi mata aikine jiya?"
"Eh munfi ta, na kaita wani gida, inaga gidan É—an uwan mahaifinta ne ko makamancin haka"
Abbas yace "babu dai wata matsala ko?"
"Babu wata matsala, ba tayi min dai wulaƙanci ba, Amma fa naga izza wadda ban taɓa ganin makamanciyarta ba, dan cikin isa da gadara take wa kowa magana, bata shakkar kowa bata girmama kowa, kai ko Dariya banga tayi ba Jiyan nan, magana ma aiki ce a gurin ta"
Abbas yace "taɓ, aishi yasa nace bazan iya ba, saboda na samu labarin yarinyar, shikenan ka dai kula sosai akan abunda muke son ganowa"
Jinjina kai Yusuf yayi, tare da cewa "Insha Allah, komai ze tafi dai dai"
***********
Ƙarfe goma na safe Yusuf ya bar gurin aikin, ya koma gida seda yayi wa Umman sa cefane, ya kai mata markaɗe ya kama mata Ayyukan gida sannan ya sauya kaya, ya nufi gidan Alhaji Nasir.
Yau da yaje ya tarar da Isa mai gadi dashi da wani, Suka gaisa, Isa yayi farat yace
"Yusuf ga Nura shine direban megidan nan, lokacin da kazo yaje garin su ne, amma gashi ya dawo, shike kai Alhaji unguwa"
Yusuf ya miƙa wa Nura hannu suka gaisa.
Isa ya nisa yace "Yusuf kayi gangancin tafiya jiya, nan ta fito a birkice jiya kaman mara hankali tazo nan tana neman ka wai ka fita da ita, baka ga shigar jikin ta ba, daga tambayar ta a haka zaka fita da ita ta mareni, wallahi har yanzu ko ƙuda bana so ya taɓa fuskata dan ba ƙaramin shiga marin nan yayi min ba"
Zaro ido Yusuf yayi yace "mari kuma?"
"Wallahi Yusuf mari na tayi"
Nura yace "aiba abun mamaki bane, dama wani lokacin haka take birkice wa, kun san abunka dame rangwamen Ƙwaƙwalwa, aini tunda naji zata dawo naji aikin gidan nan ya fita daga kaina, Allah ya temakeni aka samo mata nata direban"
Kallon su Yusuf yake dan be fuskanci inda zancen nasu ya dosa ba.
Isa yayi ƙasa da muryar sa yacewa Yusuf
"wani lokacin birkicewa take kaman hauka hauka, shiyasa kaga bata son mutane suje inda take, tana da larurar ƙwaƙwalwa shiyasa....
Yusuf ya katse shi ta hanyar cewa
"Shikenan shikenan, Allah ya bata lafiya be kamata a dinga yayatawa ba, Addu'a ya dace ayi mata, faÉ—ar bashi da Amfani sam"
Widad ce ta fito ƙaton falon gidan, ta tarar da matar gidan da yaran ta Suna ta ciye ciye suna hira, tana fitowa suka yi tsit suka shiga taitayin su, suka dena hirar.
Ta dube su É—aya bayan É—aya, kamar me nazari, sannan ta yatsuna fuska tace
"Amal jeki kira min wancan matsiyacin talakan direban, yau in fara gwada masa wacece ni"
Sam Amal ba taji daɗin kalaman da Widad tayi amfani da su akan Yusuf ba, Amma babu yadda ta iya ta miƙe ta tafi kiran sa.
Tunda Amal ta fito ta hangi Yusuf yana hira da su Nura, yayi kyau sosai komai nasa gwanin sha'awa, kamar ba direba ba.
Amal Ta ƙaraso inda suke bata kula su Isa dake ƙoƙarin gaishe ta ba, ta dubi Yusuf tace
"barka da rana Yusuf"
Fuskarsa ba yabo ba fallasa yace
"Yawwa barka, ina uwa É—akina?"
Bata jin daɗin yadda koda yaushe yake taƙaita magana da ita, Amma ta basar tace
"itace tace in kira ka ma"
Yusuf ya miƙe yace "shikenan muje"
Yabi bayan Amal, tsananin kwarjinin Yusuf ne yasa Amal sam ta kasa kuma ce masa komai, se ƙamshin turare yake fitarwa me daɗin ƙamshi kaman ba direba ba.
A falon suka tarar da hakimar ta harɗe da alewa me tsinke a bakin ta, tana danna waya tareda kaɗa ƙafafuwan ta.
Kamar kullum yanzu ma kanta babu ɗan kwali, ta baje gashin ta, Amma yau anyi sa'a skirt ne dogo a jikin ta da wata 'yar ƙaramar riga shara shara.
Tunda Yusuf ya shigo ɗakin ƙamshin turaren sa ya daki hancin ta taji ya saukar mata da wata muguwar kasala, a duk lokacin da Yusuf zezo gidan nan taji wannan ƙamshin turaren a jikin sa se kasala ta saukar mata.
Kallo ɗaya Yusuf yayi mata yaji ƙirjin sa ya buga da ƙarfi, da sauri ya ɗauke idon sa daga kanta, Sam fuskar ta babu alamar afuwa.
Ya kalli matar gidan yace
"barka da yamma Hajiya"
"Yawwa barka sannu ya aikin?"
"Alhamdilillah"
Ya juya ga Widad yace "sannu da hutawa ranki ya daÉ—e"
Dama be zaci zata amsa ba, dan haka be kuma cewa komai ba se sunkuyar da kansa ƙasa da yayi.
Ya shafe mintuna Arba'in a durƙushe a gaban ta ba tare da tace komai ba, shi kuma ko kansa be ɗaga ba.
Amal ji take tamkar ita ce a durƙushe a gurin, gaba ɗaya taji kaman ta cewa Yusuf ya tashi yayi tafiyar sa.
Ba zato ba tsammani ya tsinkayi maganar ta
"Waye ya baka iznin tafiya jiya?"
"ba kowa Ranki ya daÉ—e"
Seda ta kuma jan wasu mintunan sannan tace
"meyasa ka tafi?"
Ba tare da ya É—ago kansa ba yace
"na zata na gama aikina na jiyane shiyasa, Amma hakan ba zata sake faruwa ba Insha Allah, kiyi haƙu....
Cikin tsawa tace
"Shut up, what the hell are you trying to say? Do you sign my conditions based on Assumption? Don't you read what is in that paper? Why are you trying to applogise? Talaka baze canza hali ba, baku da Alƙawari baku san ƙa'idar Aiki ba, se an jima ku buɗe baki kuna zagin shugabanni da masu kuɗi, waye kai da zaka karyamin doka? Me kake taƙama dashi da zaka nemi ka raina min hankali? Ɗan uban waye kai? Ko ban gaya maka lokacin aiki nawane ba? Har da zaka fara da rainamin hankali"
Tunda Widad ta fara zazzaga rashin mutuncin ta Yusuf be ɗaga kai ba, dukda yadda zuciyar sa ke harbawa jijiyoyin kansa suka miƙe saboda ɓacin rai, Amma ya dake.
Amal kaman ta É—ora hannu akai tayi ihu, ji take tamkar ita Widad ke ciwa mutunci, ita kuwa matar gidan da Ramlah ko a jikin su dan babu wanda Widad ta bari a rashin mutunci.
"kasan tsanani baƙin cikin da na shiga zama na a gidan nan bayan an ɓata min rai, daka nan ka fita dani da ban shiga damuwar dana shiga ba, tun jiya nake fama da damuwa saboda sakacinka, nayi kwanan baƙin ciki da ɓacin rai, this is my last warning to you, idan makamancin haka ya kuma faruwa, sena nuna maka wace ce Widad"
Risinawa ya kuma yi da kai
"zan kiyaye ba zana kuma ba insha Allah"
Jefo masa key tayi fuskar sa tare da faÉ—in
"Car Number 8, to bulama's residence"
Yaji zafin yadda ta jefa masa key a fuska, da maganganu marasa daɗi da tayi masa, amma yasa hannu ya ɗauka, kaman wanda ƙwai ya fashewa a ciki ya nufi hanyar fita.
Fakar idon Widad Amal tayi ta biyo bayan Yusuf, wajen ƙofar fita ta cin masa, yana ta sauri fuskarsa babu Annuri, Amal ta kira sunan sa, dan tsayawa yayi ya waigo yana kallon ta
"Dan Allah kayi haƙuri da abunda Widad tayi maka, haka halin ta yake muma duk haƙuri muke da ita, dan Allah kayi hakuri"
Ga mamakin ta se taga murmushi akan fuskarsa yace
"aini banji haushi ba, tabbas laifi nane da banbi komai a ƙa'ida ba, bayan nasan hakan ya saɓawa Yarjejeniyar dana sakawa hannu, kuma nasan yana daga AƘIDAR uwa ɗakina girmama Alƙawari, ya kamata in nemi Afuwa ne ba jin haushi ba"
ÆŠan zare ido Amal tayi "yanzu duk abunda tayi maka kana nufin ba kaji haushin hakan ba?"
Jinjina mata kai yayi alamar eh tareda faÉ—in,
"bari in hanzarta in fito da motar karta fito ta sameni anan ranta ya kuma ɓaci" yayi gaba abun sa yayin da shi kaɗai yasan me yake ji a ransa.
Yaje ya fito da motar da ce masa, ya buÉ—e ya shiga ya zauna ya kifa kansa akan sitiyari, tabbas badan duk cikin aikin sa yake wannan abun ba to da ko Gidan su Widad gold ake sarrafawa baze kuma aiki a gidan ba.
Jin ƙamshin turaren ta yasa shi saurin ɗagowa, ta buɗe gaban motar ta zauna, tace "jeka falo inda na zauna ka ɗakko min wayata"
Ikon Allah wayar ma bazata fito da ita ba seya É—akko mata? Bece komai ba ya fita daga motar ya koma cikin gidan, yana zuwa ya tarar falon ba kowa wayar tana kan center table, ya É—akko ya fito ya kawo mata.
Tasa hannu ta karɓa ba tare da ta kalle shi ba tace "A ina kaga wayar"
"Akan center table"
Murmushin gefen baki tayi tace "let's go"
Kamar yadda tace gidan Bulama ya kai ta, ya samu guri yayi parking ya fito ya buɗe mata ƙofa ta fito, ƙafarta sanye da takalmi me tsini sosai shigar nan tata baka ce musulma ce ba, kayan sun kamata tsam a jikin ta a hankali ta furta "do not accept any gift from anyone"
GyaÉ—a mata kai yayi yace "Insha Allah"
"Follow me"
Haka yabi bayan ta, cikin hanzari take tafiyar yau.
Yau kai tsaye bata nemi iso ba cikin gidan ta nufa, Yusuf na bin bayan ta.
A babban falon dake gidan suka ga wata budurwa da wannan matashin da suka tarar jiya, da wata babbar mace da alama itace matar gidan.
Maimakon Widad tayi Sallama se tace "Hi how are you doing guys?"
Matar tace "Widad dama kina garin nan amma ko ganin ki ba'ayi"
Budurwar tace "Wallahi Mum Ramadan yace tazo jiya amma taƙi shigowa" Yusuf dai bece komai ba saboda jan kunnen da tayi masa jiya.
Ramadan ya kalli Widad yace "you look so Cute in this outfit Dear"
Ba ta amsa musu maganganun su ba tace "Is Daddy Around?"