← Book details Akidata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 82

Sashe 57

Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aka duba aka ga Yusuf ze iya bawa Widad jini, saboda rukunin jininsa ake cewa universal donor wato O-, sedai an samu jinin Yusuf da malaria, likitan yace 

"baze yuwu asa mata jinin ba"

Shikuma Yusuf yace be yadda da kowa ba, jininsa za'a saka.

Saleh yace  "kaga doctor, koma menene a jinin nasa saka mata, can taƙarke musu dan zamanmu anan akwai hatsari"

Aka bawa Yusuf Abinci, amma ya kasa ci se É—an kaÉ—an saboda hankalinsa na kan Widad, ana É—ibar Jinin Yusuf jiri ya É—ebe shi ya yanke jiki ya faÉ—i, haka aka É—auke shi aka bashi gado.

Akayi treating É—in raunkan jikin Yusuf, aka masa allaurai dan samun relief.

Aka sakawa Widad jinin Yusuf, tare da sauran Allurai, Yusuf na farfaÉ—owa ya fara tambayar ina Widad.

Likitan yace "wai dan Allah meye alaƙarsa da wannan yarinyar haka?"

Saleh yace "ƙanwarsa ce shiyasa ya damu da ita, 'yan fashi ne suka harbeta akan hanyar su ta tafiya, ita kaɗai yake da ita shiyasa"

Yusuf ya koma inda Widad take yasa ta a gaba, ya ƙura mata ido ko ƙyaftawa bayayi, tunda aka cire bullet ɗin nan har yanzu bata farka ba.

A hankali ta buɗe idonta, ta yunƙura zata miƙe Yusuf ya riƙeta yace "bi a hankali fa jikinki babu ƙwari"

Ta kalli Yusuf tace  "A ina muke nan?"

"I think we are save now insha Allah, yanzu zamu koma gida" ya bata amsa

Saleh ya shigo ɗakin yace  "waye yace maka zaku koma gida ne"?

Widad ta kalli Saleh ta ƙura masa ido, kamar taga baƙuwar halitta.

Yusuf yace "meyasa ba zamu koma gida ba yanzu?"

"saboda idan kuka koma, da kai da ita da mahafinta duk sesun kasheku"

Yusuf yace  "meyasa?"

"Zan gaya maka komai, Amma daga nan mafaka zan baku, inda zaku ɓuya ba zasu san inda kuke ba na gama shirya komai daga nan tafiya kawai zamuyi"

Saleh ya miƙowa Yusuf wata babbar jarkar youghurt yace "gashi nan kuci nasan ba wani Abincin kirki a cikinu, sannan ka canza riga ita kuma a sama ta hijjabi"

Yusuf ya karɓi youghurt ɗin ya buɗe ya miƙa mata, amma ta ɗauke kai, Yusuf ya girgiza youghurt ɗin ya ɗaga kai ya sha, sannan ya sake miƙa mata.

Se a lokacin ta karɓa, ta dinga sha saboda azabar yunwar da take ji, sedai tana gama sha ta dinga amai saboda kwanakin da tayi babu Abinci a cikinta.

Saleh yace  "Yusuf yakamata mu bar gurin nan da gaggawa in kaiku inda zaku fake, zamanmu anan hatsari ne na gaske"

Yusuf yace  "Amma jikinta har yanzu bata da lafiya, ya za'ayi mu tafi a haka?"

Saleh yace "zamu karɓi magungunan da zaku cigaba da Amfani da shi, amma dole mu bar gurin nan"

Haka likitan ya tattara magungunan Yusuf dana Widad ya basu, suka hau mota Saleh ya cigaba da nausawa dasu seda suka sake shafe wata tafiyar, Widad kam magungunan data sha basu saketa ba dan haka duka tafiyar nan bacci take, seda sukazo wata mararraba sannan Saleh yayi parking, wata tsohuwar motace akori kura ('yar ƙurƙura) gaba ɗaya ta sha jiki ta fatattake, hatta fentin jikinta ya koɗe duk ta mole, anyi parking ɗintabakin hanya.

Wani mutum ne ya fito daga a kori kurar, suka gaisa da Saleh, Saleh ya bashi mukullin motar da suka je da ita, suka kwance lambar motar dake jiki da wata.

Saleh Ya kalli Yusuf yace "Yusuf ku fito wannan motar zamu hau mu ƙarasa"

Yusuf yace "nifa Saleh ban gane wannan abubuwan ba, kodai kaima kana da wani ƙudurin ne akanmu"

"Yusuf wallahi ba wani abu da nake shiryawa don in cutar daku, sedai ƙoƙarin ceton rayuwar ku"

Yusuf ya fito hannun sa ɗauke da Widad suka shiga 'yar ƙurƙuran nan, Saleh yaja motar.
(Yau Widad ce a cikin irin wannan motar🙄)

Tashin hankali ba' a samasa rana, duk wannan uwar tafiyar da suka sha Nafila ce akan wadda suke yi yanzu, wata irin ruɓaɓɓiyar hanya suka bi, banda ƙura babu abunda yake tashi wata irin lalatacciyar hanyace, duk kwazazzabai da turɓaya ga uban ramuka, wani ramin in suka shiga da ƙyar suke fita ga ƙurƙuran nan se wani irin ƙugi injinta yake yi, gashi sun matsu a motar, duk yayin da suka shiga rami haka suke bige kafaɗu da ƙarfen motar.

Wannan kwaraf kwaraf É—in ne yasa Widad ta farka, a hankali ta kalli Yusuf tace

"A ina muke?"

Yusuf yace "Sannu ya jikin naki?"

Bata bashi amsa ba ta kuma cewa  "A ina muke ne?"

"Mun kuɓuta ne, Saleh ze bamu mafaka"

ÆŠan lumshe ido tayi sannan tace "Na gaji jikina ciwo yake, hannuna zafi kaina ze fashe, Wayyo Allah Daddy na"

Yusuf yace "kiyi haƙuri insha Allah komai ze daidaita, zakiji sauƙi mun taho da magunguna"

Shiru tayi ta sake kwantar da jikinta a ƙirjin Yusuf, hawaye na bin gefen idonta.

Tun Yusuf yana sa ran tafiyar ta ƙare har yayi shiru ya zubawa sarautar Allah ido.

A hankali Yusuf ya fara ganin gidaje  tsilla tsilla a gurin, gine gine na tsurar ƙasa haka Gidajen suke, wasuma ko katanga babu a haka suke, yayi mamakin wannan irin ƙasurgumin ƙauye haka da yadda mutane ke rayuwa a cikinsa, suka baro duk bakin hanya suka shigo wannan surƙuƙin guri sukayi ginin Gidaje.

A hankali suna cigaba da tafiya, yaga ƙauyene sosai me ɗauke da gidaje da mutane a ciki, sedai sunyi hannun riga da duk wani abun more rayuwa da jin daɗi, kama daga Makaranta, Asibiti, ko wani abu me kama da borehole tunda suka shiga ƙauyen Yusuf be ganshi ba.

A ƙofar wani babban gidan ƙasa, an shafawa ƙofar gidan farar ƙasa, alama dai mamallakin gidan yana riƙe da wata sarauta ne a ƙauyen.

Saleh yace "Yusuf ina zuwa"

Ya sauka daga motar ya shiga cikin gidan, Yusuf yana ta ƙarewa gurin kallo yana tunanin anya Widad zata iya rayuwa a cikin gurin nan?

A hankali yaji tace  "Ka yadda da Saleh, kana da tabbacin shima ba cutar damu zeba?"

"Ko ban yadda dashi ba, Allah baze bashi damae cutar damu ba, nidai fatana inga kinji sauƙi gaba ɗaya"

Ajiyar zuciya tayi, tai shiru ba tace komai ba can Saleh ya fito shida wani dattijon Mutum, kansa É—auke sa rawani.

Suka ƙaraso gaban akori kurar, dattijon yace "sannu dai ɗan samari"

Yusuf yace yawwa Baba, barka da yamma

"Yawwa barka" mutumin ya kalli Saleh yace  "sune wannan?"

"Eh sune wanda na gaya maka, ina son su zauna a gidanka na wani lokaci, kafin komai ya lafa su koma"

"Amma kana ganin babu wata matsala Saleh, nifa bana son abunda zezo ya É—agawa Al'ummar garina hankali, kasan ku mutan binni se a hankali"

Saleh yace "Haba dai, wane irin matsala taimako zakayi, baka ga yadda suke a galabaice ba, babu wata matsala insha Allah"

"Shikenan, shigo dasu se a kaisu É—akin daka gyara musun"

Yanzu ma Widad ba zata iya tafiya ba, Yusuf ne ya É—auke ta zuwa cikin gidan.

Duk da rabi tana hayyacin ta rabi bata hayyacin ta, tana mamakin mutane ne ke rayuwa a wannan gidan, roofing gidan kansa na Azarane, ta dinga kallon roofing tana tunanin menene wannan?
Yayin da wasu É—akunan roofing danga ne.

Tunda suka shigo gidan, mutan gidan maza da mata suka fito suka yi cirko cirko kamar zakaru suna binsu Yusuf da kallo kamar sunga baƙin halitta.

Wani ɗakine a can ƙarshen gidan, Saleh yasa mukulli ya buɗe ƙofar katakon dake ɗakin ya shiga yacewa Yusuf "bismillah"

Ba lefi ɗakin yana da girma amma ba sosai ba, yana da taga guda ɗaya wadda akayi ta da katako da kuma langa langa, ɗakin ginin ƙasa ne tsura, sedai anyiwa ƙasan floor, aka shimfiɗa buhu a ƙasa sannan aka kawo tabarma duk aka shimfiɗa.

Akwai matsaikaciyar katifa a shimfiɗe a ƙasa, da bargo guda biyu se fula guda ɗaya duk sababbi.

Gefe ga tulu, da wani ƙaramin kwandon kwanuka da 'yan kwanuka a ciki, gefe ga sababbun bokitai guda biyu, da sabuwar buta.

Akan katifar Yusuf ya kwantar da Widad, da duk inda ya motsa ta ciwo yake mata.

Dattijon yace  "wannan bata da lafiya ne haka?"

Saleh yace "Eh bata da lafiya, a hannun masu garkuwa fa na karɓo su, na maka bayanin komai, dan Allah Baba a kula dasu, duk abunda suke buƙata ayi musu"

"Shikenan, indai nine baka da matsala, ko baka kawo kowa ya zauna a gidan nan ba, gidan nan na jama'a ne, Allah ya basu lafiya"

Ya juya ya fita, yana kora yaran da suka yi dandazo a ƙofar ɗakin suna leƙen su Widad.

Idon Yusuf ne ya sauka akan akwatunan Widad data shirya domin tafiyar da zasuyi, da traveling bag É—insa da suka bari a motar da'aka sace su.

Yusuf ya zare ido yace "Nifa Saleh ina buƙatar kamin bayanin abubuwa, ya akayi ka samu jakunkunan mu na tafiya? Ya akayi kasan idan muke kaje ka tseratar damu?"

Saleh yace  "Nasan zakayi mamaki, kuma dole ku tambaya, Amma yanzu ina sauri saboda zan koma kano kar su gane wani abu a ƙasa su fara zargina, duk yadda aka shirya sace ku dani akayi shi, Tun bayan sace ku ni kuma na fara shirin yadda zaku tsira, amma ka sani koda wasa karka kuskura kayi gangancin barin ƙauyen nan in bani na fita daku ba, dan wallahi suka ganku sekun kasheku"

Yusuf yace "wai tsaya, wai inane nan ma tukuna?"

"Nan wani ƙauye ne a cikin garin Bauchi, Zan dinga zuwa ina duba ku, a waccan jakar na ajiye muku abubuwan da ba'a rasa ba da zaku buƙata kafin ku saba da irin rayuwar da suke yi, ga kuma kayanku can dana kawo nan, nan gidan ƙanin kakana ne dan haka insha Allah baku da wata matsala, idan ma dawo za kaji komai "

Saleh ya fita tsakar gida ya kalli wata dattijuwa yace "Gwaggo dan Allah Amana nan, a kula da baƙin nan dan manyane duk abunda suke buƙata ayi musu"

Gwaggo tace  "Lallai kam, baƙin suna da girma a gurinka, tunda sanadinsu gashi kana leƙo mu"

Wata mata a tsakar gidan tace "Eh aimu da yake cinyesu zamuyi shiyasa ba'a bamu amanar baƙin ba se ita"
Chapter 57 · 0% Book details