← Book details Akidata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 82

Sashe 72

Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Eh ita kazar"

"ta yaya zanjawa kaza kunne? Ko nima kazarce?"

Widad tace "to waya sani"

Gwaggo dake banÉ—aki kam dariyarta ta sha, dan yanzu sun saba kusan kullum da rigimar Widad da Hari suke karyawa.

Yusuf da wanine yace masa Widad ta iya neman magana cewa ze ƙaryane, amma yanzu yake ganin zahiri da ikon Allah, haka yaita bawa Hari haƙuri sannan yasa Widad a gaba zuwa ɗaki.

Ya ƙura mata ido sannan yace "da wanine ya cemin kin iya rikici haka cewa zanyi an miki ƙarya, amma gashi da idona ina ganin ikon Allah, kullum sekin nemi magana"

"da da bana yi ancemin mahaukaciya bana son mutane, yanzu kuma kace na fiye rigima"

Yusuf yace "yi haƙuri, amma adinga ragewa kinji queen, waini ya'akayi kika sake da mutan gidan nan, abun ya bani mamaki fa"

"Basu san ni wace ba, dan haka bana tunanin zasu cutar dani, dukda suma bawai yarda dasu nayi ba, amma inajin daÉ—in yadda suke kyautata min ne"

Yusuf yace "to nifa, an yarda dani?"

Kallon up and down Tayi masa tace "tukuna dai"

"shikenan ni na yadda dake ai, zoki zauna kusa dani muyi hira"

"Baza'ayi hirar ba, idan nazo kusa da kai taɓani zakayi"

Dariya Yusuf yayi, yace "taɓakinne bakya so inyi?"

"Eh bana so, kai kuma sekace dole seka taɓani"

"ba laifina bane, laifin zuciyata ne Gimbiyata"

"kai ka sani kai da zuciyar taka"

Tai maganar tare da kwanciya ta koma bacci, a hankali Yusuf ya dawo kusa da ita ya kwanta, tana yunƙurin juyi akan katifarta taji mutum, ta leƙo kanta daga bargo taga Yusuf.

"wai dan Allah meyasa kake min hakane, tasarmin daga kan katifa"

"Niba taɓaki zanyi ba, ina son inyi bacci ne zuwa ƙarfe goma in fita, Amma cinnaku se cizona suke wuyana ciwo yake saboda kwanciyar ƙasa, haba uwa ɗakina, atemaka a tausayamin mana"

Tura baki tayi tace "to matsa ni in fita tsakar gida in baka guri seka kwanta"

Zaro ido yayi yace "haka kawai inje ki fita ki jawomin magana, ki fita neman rigima, a'a yi zamanki anan"

"toni gaskiya bazan kwanta a kusa da kai ba"

Banza yayi mata ya gyara kwanciyarsa, tare da lumshe ido, yunƙurawa tayi zata fice ya fizgota ya zaunar da ita yace "yi haƙuri, bari in tashi in bar miki katifar, base kin fita kin janyomin magana ba, har mamaki nake yadda kika koyo rigima"

"nifa ba magana zan É—akko ba, ni kawai zomaye zan kalla"

"Idan kika tsokani Baba Hari, ba zan baki bredin ba"

"aikuwa kuka zanyi in ka hanani" ta miƙe tayi waje abunta.

Hankalin Hajiya Halima ya kasa kwanciya sam, saboda rufe mata É—a da'akayi, Amal ma duk abun ya dametta, suna ta zaryar station amma abu ya gagara, Yanzu ma Amal ce ta tafi É—akin Ramlah, ta tarar da ita a zaune tana waya, da Fahad.
Amal ta samu guri ta zauna, ta jira ta kammala sannan ta kalli Amal tace "lafiya kuwa? Kin shigomin É—aki kin sani a gaba kina ta kallona"

Amal tace "Ramlah waike baki damu bane dan Allah, kwanan Yayanmu Uku a hannun 'yan sanda, Mummy se zarya take anƙi sakinsa, amma kin shigo ɗaki wayarki kawai kike"

"to Amal haukacewa kike so kiga nayi ko yaya? Shima Allah ya ƙara masa waishi ga me mutunci ya zauna yana jiyyar uban da ya tsinta a rana, kinga hakan ze zamo masa darasi gobe baya ƙara taimakao ba"

Amal tace "bekamata ki faÉ—i haka ba Ramlah? Ta wani fannin in aka duba abunda Yaya yayi beyi laifi ba, ko so kike duniya ta farga da halin da'ake ciki? Ace bashi da lafiya amma babu wanda ya damu a cikinmu? Ni wallahi abun ya fara damuna koba komai Yaya Anwar É—an uwanmu ne"

Ramlah tayi ajiyar zuciya tace  "kuma fa hakane, ni kaina ta wani fannin inajin ba daɗi rufe shin da'akayi, amma me zan iya akai wanda Mummy ta kasa"?

Amal tace  "Fahad zakiyiwa magana, dan Mummy taje har gidansu ta gayawa mahaifinsa amma yaƙi ɗaukar abun da mahimmanci, ke tunda kuna ɗasawa dashi kisa yayiwa mahaifinsa magana yasa baki a saki Yayanmu"

Ramlah tace "Anya kuwa? Fahad fa akwai lafiyar kafiya mussman yanzu da suke takun saƙa da yaya"

Amal ta taɓe baki tace "ashema ba son naki yake ba tsakani da Allah tunda ze iya barinki cikin damuwa, Allah wadaran wannan soyayyar"

"Amal ni kike cewa Allah wadaran?"

"Na faɗa Allah ya wadaranta, dama wannan banzan Fahad ɗin me fuskar jakai kansa kawai ya sani, in ba soyayyar ƙarya ba, yayiwa mahaifinsa magana yasa baki a saki ɗan uwanmu mana, naga shima dai ɗan uwansa ne"

Ramlah tace "Aikuwa Amal i will prove you wrong, zan nuna miki soyayyar mu ta gaskiya ce"

Amal tace "in gani ƙas, ancewa kare ana biki a gidansu, ƙaryar banza burodi a lefe, ina amfanin soyayyar da baka da alfarma a gun wanda kake so"

Ta tashi ta bar mata É—akin, tana ci gaba da mita da tsaki.

Nurat ta shirya cikin doguwar riga, tayi rolling ta ɗau wayarta da jakarta ta fito, ta leƙa ɗakin mamanta taga tana bacci, ta taho cikim sanɗa ta fito harabar gidan, da sauri sauri ta tafi bakin gate tace "zoka buɗemin ƙofa zan fita"

Me gadi ya kalleta yace   "ina zaki?"

"ka aikeni ne? Ka buÉ—emin zan fita"

Ya É—an sosa kai yace "Madam, me gidan nan yace kar in kuskura in sake bari ki fita, muddin bashi ya bada umarnin hakan ba"

A É—an hasale tace "ka buÉ—emin ba nisa zanyi ba, yanzu zan dawo"

Girgiza mata kai yayi yace "dan Allah kiyi haƙuri, wallahi zan fuskanci fushinsa muddin na bari kika fita"

Juya tayi cikin gida, jiki ba ƙwari tana tunanin meye mafita, can wani abu ya faɗo mata, ta miƙe ta fito tace masa  "kazo Mummy na kiranka"

Ya miƙe ya biyo bayan Nurat, yana gaba tana binsa a baya, yana shiga falonsu cikin sanɗa ta dawo baya a hankali, tayi waje tana zuwa tasa mukulli ta buɗe gate ɗin tayi waje abunta.

Gidansu Widad ta tafi, tana zuwa tayi sa'a ta tarar da Amal a babban falo tana karyawa, Amal na ganinta ta buÉ—e baki tace "Nurat yau kece a gidanmu haka? Abun mamaki"

Nurat tayi murmushi tace "meye na mamakin kuma?"

Amal tace "ni dai nasan koda zaki zo gidan nan saboda Widad zaki zo, kuma duk garin nan ba wanda be san anyi kidnapping É—insu ba, kuma dai amma baban ku besan kinzo ba"

Nurat tayi murmushi tace "tabbas nasan an sace Widad da É—an uwanta, sedai...

Amal tace " É—an uwanta kuma? Direbanta dai"

Nurat tace "direba kuma kamar yaya direba?"

Amal tace "kamar yadda na gaya miki, ita da Yusuf ne aka É—auke su, Yusuf kuma direbanta ne"

Nurat tayi shiru, sannan tace "Amma meye alaƙar dake tsakaninta da Yusuf?"

Amal tace "Allah kaɗai yasani, Wallahi Nurat ina cikin matuƙar damuwa ɓatn nan nasu, mussman Yusuf idan nace zan nuna damuwar da nake ciki ma babu me saurarata a gidan nan, Amma duk rashin yardar Widad ta yadda da Yusuf fiye da tunaninki"

"Amma Amal mezesa matashi kamar Yusuf ya ɓige da aikin direba a gidan masu kuɗi?"

Amal tace "bake ba ni kaina ina wannan tambayar, amma kin san da wani aikin gwamnatin gara aiki a gida kamar wannan, dan ba Widad ba hatta me gidan nan ya yadda dashi sosai, Amma a yadda Yusuf ya haɗu kam, bekamata ace aikin direba yake ba, nayi masa zancen ya nemi wani aikin, amma yaƙi yarda, yafi ƙaunar kasancewa a ƙarƙashin wannan uwar izzar, tana hantararsa tana komai amma baya ganin laifinta"

Shiru Nurat tayi kamar ba zata ce komai ba, can tayi ajiyar zuciya tace "Amal ya batun Yaya Anwar kuwa?"

Amal tace "hamm, yana can Mummy tana ta fama anƙi sakinsa, wai har yanzu bincike ake akai"

Nurat tace "wani station É—inne?"

"Suna state CID shida Likitan"

Nurat tace "Allah ya fidda shi lafiya, Insha Allah zanje in ganshi"

Amal tace "kai amma kuwa mungode sosai Nurat"

Nurat tace "bakomai Amal, se anjima"

Yusuf yayi baccinsa ya tashi, ya buÉ—e jakarsa ya É—akko kayan tea daya bada sautu aka kawo masa, ya É—ora tea Widad tana tsakar gida suna hira da Hindu, da hansai.

Yayinda Hanne se wani gyatsine fuska take yi, bata kallon ko inda Widad take, Widad data fita bata taɓa nuna tasan da halittar Hanne ba, abun da Hanne bata sani ba shine, mutanen da suka damu da itama ba kowa take iya shiga sabgarsa ba, balle wanda ya nuna be damu da ita ba.

Yusuf ne ya fito tsakar gida, yaje ɗakin megari suka sake gaisawa  ya zauna suka shiga hira.

Widad na zaune kusa da gwaggo, tana dama koko tana kallon yadda take yi, Widad tace "Mama haÉ—a kokon nan ma ashe ba wahala, na iya haÉ—a custard shima zan iya wannan"

Hansai tace "meye kuma kostan?"

Widad tace "wani abune shima sha ake, kamar haka ake dama shi amma suna da É—an banbanci da wannan, Ai zaki ban watarna nima inyi ko?"

"taɓ za'a sha kwaɓa kuwa, yadda kike a sangarcen nan ba uwar da kika iya, mijinki na fama wallahi, ba uwar da kika iya se zance"

Widad ta ɗaga ido ta kalli Hari tace "Mijinki ne yake fama da ƙazantarki ba nawa ba, kuma karki ƙara cemin sangartacciya"

Gwaggo tace "yi haƙuri Amarya, ƙyaleta"

Gwaggo ta fara rabon koko, ana zuba na kofin megari Widad tasa hannu ta É—auka tace "wannan nake so, wannan kofin yafi kyau"

Gwaggo ta É—anyi shiru, Hansai tace "Amarya kofin megari nefa"

Widad ta tura baki tace "toni ina son kofin, wannan nake so"

Gwaggo tace "Hindu, jeki ki duba ƙasan gadona a cikin kwanukan Hanne ki ɗakkon sabon kofi irina Malam"

Hanne tace "kai gwaggo kofin Auren nawa za'a É—akko?"

Gwaggo tace "eh kema ba Allah ne ya baki ba, a sai miki wani"

Haka aka ɗakko sabon kofin silva, se ƙyalli yake da murfinsa aka zubawa Widad koko a ciki, Hanne ta dinga mita tana kumbura baki, ai Widad bata nuna tasan da zaman Hanne a gurin ba.
Chapter 72 · 0% Book details