← Book details Akidata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 82

Sashe 37

Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Seda ya kammala sannan ta ajiye masa ATM ɗinta, ta miƙe ta nufi hanyar fita, Yusuf kuma ya nufi gurin biyan kuɗin, kafin Widad ta kai ga ƙofar fita wani mutum da tunda suka shigo yake kallonta yabi bayanta.
Yusuf yace "ashe akwai mini Drama yau"

Ya biya kuÉ—in ya fito, sedai yana fitowa ya tarar tana zazzagawa Mutumin masifa.

"Kalle ka ni zaka biyo kace in baka lambata? Bazan bayar ba shashsasha an gaya maka kowa sakaraine irin ka?"

"Ni kike cewa sakarai?"

"Na gaya maka ko akwai abunda zaka iya ne?"

Yusuf ya ƙaraso da sauri gurin yace "haba bawan Allah, ya zaka biyo matar Aure kace kana so?"

Mutumin ya kalli Yusuf yace "Matar Aure kuma? Da wannan shigar tata?"

"koma wace irin shiga ce tayi ina ruwan ka? Haka muka tsara rayuwar Aurenmu, haka muka ga damar yi, idan har kasan shigar da tayi bata dace ba meye na biyo ta? Kana gurin nan muka zo tare mu kaci Abinci, danme zaka biyo ta kace kana so?"

Mutumin yace "Amma indai wannan matarka ce gaskiya kayi dacen Auren kyakykyawar mace, sedai bata da É—a'a kuma bata san darajar Auren ta ba"

"bakomai a haka nake son a bata, sannan karka kuma gangancin kiran ta da wasu miyagun kalamai, ka gode Allah da ban É—au mummunan mataki akanka ba"

Ya juya ya kalli Widad da mamaki ya hana ta magana, A fusace ta juya ta tafi mota ba tare da tace komai ba

Yusuf ya juya ya koma motar shima yana shiga ya zauna, ya kunna motar suka fara tafiya, ba tace komai ba se tafasa da zuciyar ta take yi

Ba zato ba tsammani, Widad ta Ƙanƙance ido tace
"i thinks you drunk something abusive today, kasan me ka faÉ—a kuwa? Which type of Weed did you take today? Wane irin rashin hankali ka aikata? Meye hakan kake ne dan me zaka dinga danganta kanka dani a matsayin mijina, kai ko Auren zanyi zan auri talakan mutum kamar Kane?"

Dukda yadda kalaman Widad suka daki zuciyar Sa haka ya daure, yayi parking ɗin motarsa, ya matsa Kusa da ita ya matsa yace "Abunda kika ci dai shi naci, dukda baki san meye So ba, ƙarewa ma kince baki yadda dashi ba, amma the magic behind Love is that, ba ruwan sa da talaka kome kuɗi, sannan wannan abunda nayi shine kaɗai mafita daze hana kowane kare da biri binki, da kuma ƙarewa surar jikin ki kallo, please Dress decently to avoid such type of people, dukda ina matsayin me miki aiki, aikin ma na direba, I have to tell you something, you have an attractive beauty Widad, stop exposing it anyhow yana taɓa zuciyata a duk lokacin da kika fito da wannan shigar naga wasu na ƙarewa wannan kyakykyawar halittar kallo, your beauty suppose to be only for your husband, duk wata mace me tsadace jikinta ma me tsada ne meyasa zaki dinga bari ana ganin naki?"

Ɗaga ido tayi tana kallon sa, gaba ɗaya Yusuf ya rufe mata baki, ya kulle mata kai, gaba ɗaya ta nemi izzar da jin kan da zata masa wulaƙanci ta rasa, yau wani irin kwarjini yayi mata data kasa cewa komai, shi kuma ya samu damar hakan yake ta abunda yaga dama, a baya zata iya rantsewa baze aikata haka ba, ganin yadda ko magana baya son yi.

Haka suka cigaba da tafiya kamar kurame, kowa da abunda yake saƙawa a zuciyar sa, gaba ɗaya tunanin rashin mutuncin da zata yi wa Yusuf take.

Har suka ƙarasa airport bata iya cewa komai ba, parking yayi amma bata buɗe murfin motar ta fita ba, shima zaman sa yayi yaƙi fita, ya sauke glasan suka cigaba da zama, lokaci2 ta dinga duba agogon hannun ta.

Buɗe ƙofar tayi ta fita, shima ya buɗe ya fito, Alhaji Nasir ne yake tahowa da brief case ɗinsa a hannun sa.

Yusuf ya ƙarasa da sauri yana gaida Alhaji Nasir tareda karɓar brief case ɗin hannun sa.
Alhaji Nasir yace "Yayana na kaina, fatan na sameku lafiya ya amana ta?"

Yusuf yay murmushi yace "Alhamdilillah"

Ya kalli Widad yace "my Lovely har yanzu kina fushi da Dad ko?" yai maganar yana rungume Widad, kamar anmata dole tace "Welcome Daddy"

Alhaji Nasir ya É—an shafa bayan ta yace"thank you sweetheart" suka É—unguma zuwa mota gaba É—aya, suna tafiya Alhaji Nasir da Yusuf ne kawai ke hira, Amma Widad tunanin ta ta yaya zata hukunta Yusuf.

Har Yusuf ya gama aikin sa na ranar ya tafi Widad bata samu mafita ba.

***********************************

"Jama'a bafa a bori da sanyin jiki, wannan ce damar da yakamata muyi amfani da ita, tunda Allah yasa yarinyar nan tana ƙasar nan musan abunda za muyi" cewar Alhaji Munir

Alhaji Musa yace "Ni idan an samu abun nan falillahil hamd, amma babban burina be wuce in Wulaƙanta Alhaji Nasir a idon duniya shida ahalinsa ba kamar yadda ya Wulaƙanta ni ya ɓata min suna"

Alhaji Haruna yace "gaba ɗayanmu buƙatar mu ɗaya ce, kuma kunsan Alhaji Bukar shike bamu umarnin abunda zamuyi, karmu yadda muyi abunda ze waegaza shirin mu, yanzu yarinyar taje gidan yari tayi wa Hashim barazana akan indai da hannun sa akan wannan lamari daya samu Bala to tabbas zata ɗau mataki akansa "

Alhaji Musa yace " Umarnin Alhaji Bukar kawai nake jira, amma akwai yuwuwar shima a kauda shi, dan komai ze iya faruwa barinsa a doron ƙasa"

Alhaji Haruna ya zame akan kujera yana shafa tumbinsa yace
"Ni dai kam da zan samu yarinyar nan, So nake gaskiya, dan akwai ta da ƙira daidai gwargwado".

Tsaki Alhaji Munir yayi yace "kai ka fiye shirme, ana ta kai wake ta kaya, in in hutawa kake so, ka fita ƙasashen waje ga mata nan farare yadda kake so, amma yanzu ka bari idan muka karɓi abunda muke so, muka aika Nasir Daula kiyama, se kayi yadda kaso"

Wata uwar dariya suka saki hadda shewa.

**********************************

"Bulama tafiya tayi Alhamdilillah, na samu approval na fara business É—ina da China"

"Masha Allah, naji daÉ—in hakan, Allah yayi jagora"

Baban Widad yace "Ameen ya Allah, sedai ko kun samu saɓani da 'yar taka ne? Tunda na dawo naga bata walwala ko akwai matsala ne?"

Alhaji Bulama yai murmushi yace "hmm Widad' yata ta kaina, tabbas munyi faɗa, kasan tunda nace ayi mata Aure take jin haushi na, tazo ta sameni akan wai sena mata Visa ta koma naƙi, shine take fushi"

Alhaji Nasir ya girgiza kai yace "Nima wancan satin ta kirani tana kuka, akan lallai sena kiraka nasa an mata visa ta koma, ni kuma gaskiya bazan bari ta koma ba, idanma zatavkoma se bayan Auren ta da Fahad sa tafi tare"

"hakane, daga lokacin da ta fara tara iyali dole ta dena wannan halayen nata, sannan mamanta ta kawomin ƙararta akan yadda suke da direban nan, na kirata nayi mata faɗa, nanma ta sake yin fushi dani"

Alhaji Nasir yai murmushi yace "ina tunanin akwai wani ɓoyayyen al'amari a tattare da yaron nan, ba ƙaramin daɗi naji ba ganin shine mutum na farko bayan nida kai da Widad take sakewa dashi"

"Amma karfa muyi sake yazo suyi shaƙuwar da zamu yi da nasani"

"Insha Allah ba zamuyi ba, dan yaron yana da tarbiyya sosai"

"Amma idan soyayya ta shiga tsakanin su fa?"

Alhaji Nasir yace " Yarinyar da bata yadda da soyayya ba, ta ina zasu fara soyayya? Gaba ɗaya Widad ɗina a birkice take bata da alƙibla"

Bulama yace "Kasan bata da alƙibla ai kuwa ba abun mamaki bane ta fara soyayya da direban ta, tunda shi so baya sallama".

"to nidai duk abunda ze saka ta farinciki shi nake so, idan ta kawo shi tace tana so bakomai se in Aura nata shi"

Bulama yace "Allah ya kiyaye mu aura mata direba haba Daula"

"to masu 'ya, ai seka biye mata kuyi tayi"

Sukayi dariya suka shiga hirara duniya.

***********************************
Sintiri take a ɗakin ta, tana son gazgata abunda take ji a zuciyar ta game da Abokin ta. Dagaske na kamu da Son wanda yake daga ɓangaren maƙiyin mahaifi na, amma ban san alaƙarshi da Widad ba, amma tunda na gansu tare suna da alaƙa.
Shiru tayi tana tuna yadda ya zauna a kusa da ita yana mata magana, cikin rarrashi danta saki jiki dashi.

Kamar light da yake kiran ta dashi yafi komai yi mata daÉ—i, Amma dagaske yana da Aure? Ta tambayi kanta, anya za'a yarda a auramin me mata? Gashi kuma É—an uwan Widad.

Dafe kai tayi tace "Subhanallah"

"ke lafiya kuwa? Sintirin me kike tayi haka kamar kinwa sarki ƙarya?"

Juyawa tayi ta kalli inda Maman ta ke tsaye tace "bakomai fa"

"bakomai, a hakan? Gaba É—aya alamu sun nuna baki da gaskiya sam"

Ta É—an tura baki tace "wallahi ina da gaskiya"

"shikenan, idan tayi wari maji"

Nurat ta koma kan gadonta ta zauna ta É—akko wayarta ta shiga kiran layin Yusuf amma shiru baya shiga, tayi2 harta gaji ta ajiye, tana mamakin ya akayi hakan ta faru?

Shikuwa Yusuf tun ranar data kira shi agaban Widad, yana komawa gida ya cire layin ya ajiye gaba É—aya.

**********************************

Oga Suleiman ne zaune akan kujera yana gwadawa Sakina wasu ayyuka a computer, sun maida hankali sosai kan aikin.

Abbas ne yayi sallama, suka ɗago gaba ɗaya suka dube shi tare da amsa sallamarsa, Sakina ta gaida Abbas, yayin da Abbas ya ƙamewa Suleman cikin girmamawa.

Suleiman ya bashi damar zama, sannan ya miƙa masa hannu suka gaisa, Suleiman yace "Abbas kwana biyu banga Yusuf ba fa, ya kamata ace yazo ya gabatar min da sakamakon binciken da yayi"

Abbas yace "ranka ya daÉ—e, nima kaina na kasa gane inda yasa gaba, gaba É—aya kamar ba aikin yake ba, yaje ya shantake se abun Arziki yake samu a gidan, alherin da suke masa yasa gaba É—aya hankalin sa baya kan aikin, da dai da hali a canza shi da wani kawai"

Suleiman yace "Amma kaika cemin ze iya aikin, da kai nace zan bawa ka nunamin ya fika haƙuri da juriya"
Chapter 37 · 0% Book details