← Book details Akidata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 82

Sashe 60

Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daula yayi murmushi yace "Alhamdilillah, tambayi Anwar da kaina na tashi na zauna, sedai bana jin daÉ—in Abincin sam tunanin 'ya' yana nake, ban san a halinda suke ciki ba"

Saleh yace "Insha Allah suna lafiya, kuma da yardar Allah za'a gansu"

Nurat tayi shiru zuciyarta gaba É—aya ta tsinke, tausayin Daddyn Widad ya kamata, ji take tamkar ta gaya masa abunda ke faruwa, Amma idan ta faÉ—a da wani suna za'a kirata, kuma meye hujjarta na cewa da hannun mahaifinta a sace Widad tunda ita kaÉ—ai taji abunda suka faÉ—a, Mahaifinta yana zaune da nasa iyalin cikin kwanciyar hankali, amma ya jefa rayuwar wannan iyalan cikin fargaba da damuwa.

Tana cikin tunanin Daddy yace  "Nurat, ki koma gida kinji ko, nagode sosai Allah yayi miki Albarka"

Nurat tace "Ameen Daddy"

Ta miƙe tsaye ta fita, Anwar yabi bayanta suka fita, suna fita harabar ta tsaya ta kalli Anwar tace "Yaya Anwar wai meyasa baza'a fita da Daddy waje ba, tunda yana da kuɗin nan ba babu ba? Kana kallon da yadda yake numfashi fa"

Anwar yace "Wallahi Nurat, nayi iya yina amma su Mummy sunƙi Amincewa, wai anan ma ana kula dashi, Jiya Saleh ya bani shawarar ko Asibiti in canza masa basu sani ba, sedai kawai suga an canza amma ina tunanin abunda ze biyo ba idan nayi hakan"

Nurat tayi ajiyar zuciya tace "ya batun taron kasuwanci da'ake yi duk ƙarshen shekara da ma'aikata da 'yan kasuwa kuwa?"

Anwar yace "Ana nan za' ayi jibi insha Allah"

Nurat tace  "babu wanda ze wakilci Daddyn Widad kenan?"

"Nurat ana ta lafiyarsa wake ta wani taron kasuwanci"

"Amma idan da kara, tunda shike jagorantar taron ayi wani abu akai, tunda yana kwance ba lafiya"

"Ayi wani abu kamar me kenan?"

Nurat tace "A É—aga taron zuwa wani lokacin"

Anwar yace  "kina ganin su saura mahalarta taron zasu yarda da haka?"

"Yaya Anwar, ƙaddara bata wuce kan kowa ba, dan haka babu laifi idan munyi wani abu akai"

Anwar ya gyara tsaiwa yace "to gurin wa zamuje ayi mana wannan Alfarmar?"

Nurat tace "karka damu ina da hanya, duk yadda ake ciki zan kiraka amma wannan maganar da gani se kai, karka gayawa kowa"

"insha Allah babu wanda zan gayawa, Allah ya saka da alkhairi da wannan taimako da zakiyi"

"Babu komai yaya, yiwa kaine inda kara ai bekamata ayi taron nan Daddy na kwance ba"

A ranta kuwa cewa tayi "daka san Abunda ake shirya yi a gurin taron nan, da kaima ka nemawa Alhaji Daula mafita '

Saleh ya kalli Alhaji Daula yace
" Yanzu idan nace maka na san inda Widad take zaka yadda? "

Daula yayi murmushi yace " daka san inda Widad take da baka ƙyaleni ina fama haka ba"

Saleh yace  "Hakane, jikina yana bani Su Widad sun kuɓuta, sedai kasan su dawo cikin garin nan hatsari ne?"

Daula yayi shiru yace "Tabbas, dan mutanen nan basu da imani, Allah kaÉ—ai yasan halin da suke ciki, ina cikin damuwa sosai Saleh"

Saleh yace "Insha Allah nan ba da daÉ—ewa ba zanzo maka da Labari me daÉ—i a kansu"

"kamar yaya kenan?"

"Kai dai ka kwantar da hankinka Alhajin Allah, kasan retired solder neni, nasan techniques na abubuwa da dama, dan haka ina daf da gano su"

Riƙo hannun Saleh yayi yace "Dan Allah Saleh dagaske kake? Gaba ɗay....

Farinciki yasa Daula kasa cigaba da magana, sema tari daya sarƙeshi.

Saleh yace" ka kwantar da hankalinka, Amma wannan maganar iyani da kaine, ban yadda wani yaji ba, ko Bulama karka sake ka gayawa "

" Insha Allah bazan gayawa kowa ba, Nagode Saleh "

Yusuf ya cigaba da kallon Widad da take masa wani irin kallo, zame hannun ta yayi daga jikin rigarsa yace
" Shikenan tunda baki amince ba, na manta baki da babban maƙiyi kamar Aure, kuma Aure ma kamar Auren maƙasƙancin mutum irin direbanki, bani da wani zaɓi na zama dake inba Aure mukayi ba, kuma niba abunda ze haɗa ni dake har mu gama zamanmu anan mu koma gida, tunda baki amince ba shikenan "

Ya ƙarasa maganar tare da miƙewa ya nufi hanyar fita, jiki a sanyaye Widad tace
"Na Amince!"

Share, share and Share please 🙏🙏🙏

Domin gyara sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680

                    _*AƘIDATA*_
       

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

NOT EDITED

ELEGANT ONLINE WRITER'S

                         PART1
                                Page 30_31

Yusuf ya tsaya cak ya waigo ya kalle ta yace "are you serious kin amince?"

Shiru tayi, taƙi ce masa komai, har yanzu izzar tana nan, abune mawuyaci ta maimaita magana sau biyu, Yusuf yace "Shikenan, idan Saleh yazo zanyi masa magana, kokuma in samu maigari in masa bayanin komai"

Gyara kwanciyarta tayi tace "kuma ranar da zamu koma gida zaka sakeni,gara kasa wannan a ranka"

Yusuf yayi murmushi yace "karki damu, nidai fatana ki samu lafiya komai ya lafa mu koma gida"

Nurat ta koma gida, ta lallaɓa zata silale ta shiga ɓangarenta, "daga ina kike?"

Taji muryar mahaifinta, tsayawa tayi amma takasa cewa komai, cikin tsawa yace "Nace gidan ubanwa kikaje?"

"Amm.. Ammmm. Dama... Damanaje gidansu ƙawata ne shine....

" shine ubanki, yaushe kika fara fita ke kaÉ—ai babu direba? Daga gidan ubanwa kike? Zaki gayamin ko sena kwantar dake na yankaki a gurin nan"

Nurat ta faɗa a Shagwaɓe "Nifa ba inda naje"

"Ubanwa ya kaiki duba Daula a Asibiti ubanki ne?"

A razane ta É—ago ta kalleshi, ta shiga rarraba ido.

"ba magana nake miki ba?"

"Daddy waye ya gaya maka naje duba shi?"

"Ubanki ne ya gayamin" Alhaji Musa ya bata amsa

"Kin san a duniya mutumin nan maƙiyinane, shine kika kwashi jiki kika tafi?"

Nurat tace "Daddy, 'yarsa ƙawatace kuma dukda abunda ke tsakaninku tazo gidan nan birthday na ta bani kyautar mota, yanzu kuma a sace ta mahaifinta a gadon Asibiti in kasa duba shi"

Kafin ta ƙarasa ya ɗauketa da mari, wanda seda ta dena gani na wani ɗan lokaci.

Da sauri Mahaifiyar Nurat ta fito tana cewa "lafiya kuwa? Me tayi maka ne?"

"dole ki tambayi me tayimin mana, munafuka daga ke har ita, wato da saninki ta fita taje Asibiti duba Daula, babban maƙiyina ko?"

Mahaifiyar Nurat tace "haba Alhaji kai waye ya gaya maka can taje"

Alhaji musa yace "Rufemin baki kafin in haɗa dake in muku duka, na wuce duk yadda kuke tunani, duk wani motsinku a waje ina da masu kawomin rahoto, kuma daga yau na saka doka, kada ki kuskura Nuratu ta sake fita daga cikin gidan nan, ban yadda ta sake zuwa ko'ina ba, idan kuwa ta sake sena saɓa muku daga ke har ita"

Maman Nurat taji zafin marin da yayiwa 'yarta, dan ba taga laifin da tayi wanda harta cancanci wannan marin ba.

Taja hannun Nurat zuwa ɗakinta, ta kalleta tace "kema Allah ya ƙara, gobe ma ki sake, gashi nan ya mareki a banza, kin fiye rawar kai Nurat"

Nurat ta share hawayenta tace  "Ni ban san wani tantirin munafikin ne ya gaya masa naje ba, Amma idan harna cika 'ya ta halak inason mahaifina ya dace da rahamar Ubangiji, dole in shiga rusa duk wani mummunan ƙudirinsa, ta haka ne kawai zan huce wannan marin da yayi min"

"kinga karki jawa kanki wani tashin hankalin, ki É—akko mana magana kin san halinsa sarai"

"Mummy, wallahi zubawa Mahaifina ido yana abunda yaga dama, alhalin nida ke munsan ba dai dai yake ba bamu kyauta ba, babu ruwanki a ciki nikaÉ—ai zanyi komai.

" Na sani, amma Nurat ina jiye miki matakin daze É—auka akanki, idan ya gane abunda kikeyi "

Nurat tace "ba abunda ze gane, sedai inke zaki gaya masa"

Ta É—au jakarta ta bar É—akin, ta nufi nata É—akin.

Amal ta zama kamar wata me jinya, ta rame sosai dan ko Abinci bata iya ci Sam, sedai abunda ba'a rasa ba, yanzu ma Mummy ce da Ramlah suke cin Abinci suna hirarsu, yayin da Amal juya cokali kawai take, ba ta kai ko loma É—aya bakin ta ba.

Ramlah tace "wai Abincin ne bakyaci, kokuwa? naga se juya spoon kike"

Hajiya Halima tace "na lura da yarinyar nan, kwanakin nan sam bata walwala ta takure kanta da yawa"

Amal tace "Nifa wallahi ɓatan Yusuf ne ke ɗaga min hankali, wallahi na damu sosai beji ba be gani ba am sace shi, Allah kaɗai yasan wahalar da yake sha"

Ramlah tace "Ai kece 'yar wahalar, dama abunda yasa kike wannan damuwar kenan?"

Hajiya Halima tace " waini Yusuf ɗin nan ko tare mukayi Naƙudarki ne muka haifeki ban sani ba? Ubanki ne shi? Ko haifarki yayi idan baki kiyayeni da maganarsa ba sena fasa miki baki, kije ki kashe kanki saboda wani ɗan iska, Allah yasa su haɗa dashi su kashe"

Zare ido Amal tayi tace "Mummy a kasheshi kuma?"

"Eh a kashe shi, munafikin yaro na tsani yaron nan wallahi ba ƙaramin daɗi naji ba da aka sace dashi"

Ramlah tace "wallahi nima naji daɗin hakan, munafuki yaita sunkuyar da kai kamar na Allah, saboda shi ba irin wulaƙancin da wannan makirar ba tayi mana ba, yanzu da suka ƙara gaba se hutawarmu muke"

Amal ta dire cokalin ta miƙe ta bar musu dining ɗin.

Mummy tace "Allah ya kawo lokacin da burinmu ze cika, ita kuma tana wani shirme daban"

Ramlah tace  "kedai bari Mummy, nifa harna fara tunanin irin bushshar da zanyi, da yadda zan fantama in kece raini a cikin manyan yara, wayyo Allah daɗi"
Chapter 60 · 0% Book details