← Book details Akidata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 82

Sashe 4

Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yusuf Yana zaune har Bayan sallar isha'i yana kallon labarai, yaji anyi Sallama amsa sallamar yayi tareda ɗan ɓata rai.
Me sallamar ta shigo falon ta ajiye jakarta da mayafi ta É—an kalli inda Yusuf yake tace
"fushi kuma ake dani, ko a kalli inda nake? Ai gani na dawo"

Yusuf yace "haba Umma tun azahar kika fita se yanzu bayan isha'i duk kaÉ—aici ya dameni"

Umma tace "kai tafi can, sekace wanda nake shayarwa ba damar in É—an fita, ka dinga damuwa kenan"

Cikin shagwaba yace "wana keda shi inba Ummana ba? Dole in shiga damuwa duk lokacin da kikayi nisa dani ummana, daga Allah seke se kuma Aikina ku kenan nake da su, niba Abokai ba ko wasu mutane na musamman ke ɗin ce dai, Allah ya jiƙan Abba na, tun abunda ya faru Umma ke kaɗai nake da yaƙinin ƙaunar ki a gare ni baza ta gushe ba, shiyasa bana son kiyi nisa dani"

Tausayin Yusuf ne ya mamaye ta, har zuciyar ta ta karaya hawaye na ƙoƙarin fita daga idon ta, da sauri ta fice ta bar ɗakin da nufin yin Alwala.

Bayan Umman Yusuf ta idar da sallar isha'i suka ci Abincin dare tare suna hira, Yusuf yana ta so ya sanar da Umman sa batun Aikin da'aka bashi a Office amma ya kasa, dan yasan idan har ya gaya mata ranta zata ji babu daÉ—i, ace É—anta Yazama direban yarinya, Yarinyar ma mara tarbiyya wadda bata san darajar É—an Adam ba, dan haka ya bar abun a ransa be gaya mata ba.

Haka ya kwana yana tunanin wace karɓa ze samu a gurin yarinyar nan? Ya aikin ze kasance? Haka yaita tunani har bacci ya ɗauke shi.

Washegari ma Yusuf yayi ƙoƙarin yiwa Umman sa zanncen amma ya kasa, haka yai breakfast ya tafi gurin Aiki.

A office ma kasa wani aikin kirki yayi, wayar sa ya É—akko yana kuma duba hotunan wannan tsaleliyar yarinyar, ya kuma tuna irin halayen ta da Abbas ya bashi labari. ÆŠan tsaki yayi ya ajiye wayar ya jingina da kujera ya dafe kansa yana tunani.

Sallamar Abbas ce tasa ya É—ago kansa, Abbas yace "Yusuf dama ka shigo yau baka nemeni ba?"

"na shigo tun É—azu ina aiki ne shiyasa ban neme ka ba"

"OK tashi muje, Yallaɓai Suleiman na son ganin mu yanzu"

Yusuf ya miƙe yabi Abbas suka fice, suna zuwa suka gaisa cikin girmamawa, yai musu umarni suka zauna.

Yallaɓai Sulaiman yace "Yusuf nace kuzo tare da Abbas ne dan tabattar da cewar aikin da muka ɗora muku zaku iya, mussman kai Yusuf nasan kana da kula da aiki kuma kana da haƙuri matuƙa"

Cikin girmamawa Yusuf yace "Insha Allah Yallaɓai baza'a samu matsala ba"

"Good kayi taka tsan2 kabi a hankali, karka kuskura wani yasan bincike ne ya kaika gidan, kasan aikin ka base na gaya maka ba, samun matsala a wannan aikin gagarumin hatsari ne da kuma Asara ina fatan kun san hakan"

Yusuf ya risinar da kai yace "Insha Allah ba zamu baka kunya ba sir"

"kai kuma Abbas ku kula yadda ya kamata"

Abbas yace "Insha Allah sir za muyi iya ƙoƙarin mu"

Haka suka ci gaba da tattauna wa akan harkar aiki, sannan Yallabai Suleiman ya sallame su.

Bayan fitowar su Abbas yaita bawa Yusuf ƙwarin gwiwa tareda bashi shawarwari, suka tsara yadda tafiyar tasu zata kasance ranar Asabar zuwa gidan Alhaji Nasir Daula.

Tunda gari ya waye Asabar gaban Yusuf yake faÉ—uwa, ya rasa dalilin da yasa tun da'aka gaya masa Aikin daze yi yaji gaban sa na faÉ—uwa a duk sa'ar daya tuna, har seda Umman sa ta fuskanci ya rage walwala, ta tambayeshi yace mata "bakomai" haka Yusuf yaci gaba da Adduo'i.

Yana nan zaune a ɗakin sa ya rasa abunda yake masa daɗi, misalin ƙarfe sha ɗaya na safe Abbas yazo, ya tsaya a tsakar gida suka gaisa da Umman Yusuf sannan ya shiga ɗakin ya same shi.
Abbas ya kalleshi daga sama har ƙasa yace

"gaskiya Yusuf wannan kayan naka ba suyi kama da wanda zeyi aikin direba ba, gaskiya ka canza kaya, ni baka ga kayan da na saka ba"
Se lokacin Yusuf ya lura da koɗaɗɗen Yadin dake jikin Abbas, Yusuf ya ɗanyi murmushi yace "Taɓɗijan, wannan wane irin kaya ne?, ni ban san wani kaya zan saka ba"

Abbas ya buɗe wardrobe ɗin Yusuf, duk kayan Yusuf masu kyaune, da ƙyar ya ɗakko masa wasu ƙananan kaya ya bashi ya saka suma dai basu ji jiki ba, Yusuf ya karɓa ya saka, yace "Allah yasa kar Umma tayi min magana akan kayan nan"

har zasu fita Abbas yace "É—an tsaya idan muka je gidan Sunana Sani me mangwaro ba Abbas ba "

Yusuf ya jinjina masa kai sannan suka fito, Yusuf ya kalli Ummansa dake kwashe kayan wanke2 yace "Umma zamu fita"
Umma tace "to Yusuf, Abbas ka gaida gida sekun dawo"

Har zasu fita Umma ta kira yusuf tace "Yusuf zo nan"
Dawowa yayi tace "Wannan wace irin shiga kukayi, kalli kayan jikinka be kamata ace ka fita da su ba, Allah ya rufa maka Asiri amma kasa wannan kayan kana yawo a gari"

"Umma shima hakan cikin harkar Aiki ne, idan na dawo zan miki bayani Insha Allah"

Umma tace "Amma harkar aiki shine zaka fita da wannan suturar kamar mara galihu"

"haba Umma wallahi kayan nan da kyansu, kiyi min Addu'a sena dawo"

ÆŠan girgiza kai tayi yayin da Yusuf yayi waje da sauri.

Napep suka tara suka hau zuwa gidan Alhaji Nasir, yayin da gaban Yusuf keta faÉ—uwa.
Tun daga bakin layin shiga rukunin gidan jam'ian tsaro ne ke kaiwa suna komo wa, seda aka musu tambayoyi kafin su wuce da yake sun gane Abbas yana zuwa, aka barsu suka wuce.

Koda suka je gidan Abbas ne ya sallami me Napep ɗin, tun daga waje Yusuf ya fara ƙarewa gidan kallo tirƙash lallai mamallakin gidan yaci ai masa inkiya da Daula.
Suka ƙarasa ƙofara katafaren gate ɗin suka tsaya, Abbas ya ɗakko wayarsa ya kira Isa me gadi, yace masa suna waje.
Befi mintuna uku ba aka buɗe ƙaramar ƙofar dake jikin gate ɗin ya leƙo yana ganin su Abbas ya washe baki yace

"bismillah ku shigo Ashe kaine"
Suka shiga suka tsaya suka gaisa da Isa.
Isa yace "Sani wannan ne É—an uwan naka daze aikin?"

Abbas yace "Eh shine"
Isa yace "Ya sunan shi?"

"Sunana Yusuf" Yusuf ya bashi amsa

Isa yace  "masha Allah to Allah yaba ka iko, dan seka yi haƙuri aikin akwai samu amma babu sauƙi, bari inje in sanar wa da Alhaji zuwanku"

Abbas yace "shikenan babu laifi"

Bayan tafiyar Isa, Yusuf ya kalli harabar gidan, wasu irin motoci ne masu rai da lafiya a tsaye a gefe ɗaya, yayin da ainihin ƙofar shiga katafaren gidan se kayi wani gajeren tattaki daga gate ɗin kafin ka kai ga ƙofar.
Yusuf ya numfasa yace

"wai ni Abbas ya aka yi rukunin gidajen nan jam'ian tsaro ke gadi, Amma kuma nan gidan naga wannan ma shiriricin ke gadi"

Abbas yace "Sani dai ba Abbas ba"

Yusuf yace "Am sorry, Sani"

Abbas yace "duk yana cikin binciken da za kayi, ka kula kayi taka tsan2, banda sakin jiki da kowa dama nasan kai ba me son hayaniya bane"

Isa ya dawo yace "bismillah ku taho mu shiga, Alhaji yace a shiga daku"

Tunda suka kama hanyar shiga cikin gidan Yusuf yake ƙarewa ko ina kallo, an danƙarawa gidan dukiya kaman ba'a san ciwon ta ba.

Wasu irin faluka suka dinga ratsawa, kowanne da kalar sa da irin tsaruwar da yayi, shikan sa Abbas be san haka cikin gidan yake ba.

Sunyi doguwar tafiya kafin su iso wata ƙatuwar ƙofar glashi,Isa yasa hannu ya murɗa suka shiga da sallama.

Iya girman falon nan ya ishi wani talakan gina wadataccen gidan da ze zauna, Yusuf ya fara tambayar kansa shi kuwa wannan wane irin sana'a yake yi da har ya gina wannan gidan kamar baze mutu ba?

Babban mutum ne a zaune akan wata luntsumemiyar kujera yana karanta jarida gefen sa da wata mata, se 'yan mata biyu zaune akan kujerar dake facing É—in su.

Aka amsa musu Sallamar, cikin girmamawa suka gaisa da me gidan tare da iyalan sa, yanayin gaisawar tasu ze nuna maka mutum ne me fara' a, dan kuwa fuskarsa É—auke da murmushi ya amsa musu.

Isa yace "Yallaɓai sabon driver ne da kace a samo, shine suka zo yanzu"

Ya ajiye Jaridar hannun sa yace "Masha Allah wanne ne daga cikin su?"

Cikin girmamawa Yusuf yace "Nine"

Alhaji Nasir ya ɗan ƙura masa ido yace "masha Allah, ya sunan ka?"

"Suna na Yusuf"

Alhaji Nasir ya jinjina kai yace "Hajiya Halima kinji me sunan Yaya na ko?"

"Aikam dai me sunan shi" ta amsa

Alhaji Nasir yace "Allah sarki, Allah yasa me irin halin sa ne, ni duk Yusuf É—in dana sani mutanen kirki ne, ina fatan kaima haka?"

Abbas yace "Alhaji ba ganin ido ba Shima mutumin kirki ne sosai"

Alhaji yace "ai dama na sani, ban taɓa ganin Yusuf mutumin kawai ba"

Ya kalli 'yan matan nan dake zaune yace "Amal jeki part ɗin gimbiya ta, ki gani idan idon ta biyu bata komai ki gaya mata Daddy na son ganin ta, idan kuma da abunda take yi ki ƙyaleta"

Wadda aka kira Amal ta miƙe tare da cewa "to Daddy" .

Babban abunda ya bawa Yusuf mamaki be wuce tun lokacin da' aka ce shine ze zama direban, matar da 'yan matan nan suke binsa da kallo ba, mussman wadda aka kira Amal yadda ta tsare shi da idanuwa.

Seda akayi Minti goma sha biyu da tafiyar Amal, sannan  ta dawo tace "Daddy tace tana zuwa"

Alhaji Nasir yace "to babu laifi"

Wasa2 seda sukayi minti Arba'in ba suga Alamar wadda aka kira É—in zata fito ba, iyalan suka ci gaba da hirar su aka bar su Yusuf shiru kamar mayu.

Gaba ɗaya Yusuf ya gaji da zaman, ga sanyin A. C da kallon ƙurillar da'ake masa duk yabi ya takure.

Alhaji Nasir ya kuma cewa "Ramla bawa baƙin nan Abinci kafin ta zo"

Ba tare da Ramla tace komai ba ta miƙe ta fice, ruwa da fruits ta kawo ta ajiye musu.
Chapter 4 · 0% Book details