← Book details Akidata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 82

Sashe 42

Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yusuf ko nawa kake so zan mallaka maka, in har zaka yadda ka karɓi soyayya ta"

"Shi son gaskiya tsada ne dashi, kuɗi komai yawan su basa siyansa, dan haka Allah be baki arziƙin da zaki siyi soyayya a gurin Yusuf ba"

Yana gama maganar ya juya ya fice daga lambun yana mamakin wannan naci irin na Amal.

************************************
Ramla ce kwance hannunta riƙe da waya tana magana a hankali cikin iyayi

"Abun ƙauna ta, yau kwananka huɗu da dawowa Nigeria, yakamata ace kazo na ganka fa, Allah badan inajin nauyi ba da tuni ni zanzo inda kake in ganka"

Daga can ɓangaren Fahad yace "Am Sorry beb, ina cikin damuwa ne gidan naku ne gaba ɗaya bana son zuwa, Ramla wai Daddy ze haɗani Aure da wata mahaukaciya a gidan ku, Ramlah kamarni za'ayiwa Auren dole? Auren ma da mahaukaciya, kuma Daddy se masifa yake wai se nazo mun gaisa da ita"

"Fahad nasan maganar nan tun kafin ka dawo, ban gaya maka ba saboda bana son ɓacin ranka, Amma ina cikin damuwa Fahad you know I love you" tai maganar cikin damuwa

"easy baby, ki kwantar da hankalinki, idan nazo se nayiwa yarinyar nan rashin mutunci, ni bazan aure ta ba dan ba sonta nake ba, bazan taɓa yadda da Auren nan ba, naga Daddy ya fara fushi, in anjima zan shigo gidan naku in ganta, Amma ni ke zanzo gani Beb"

Murmushi tayi tace "Ohh my God, amma naji daÉ—i Fahad seka zo".

Ta kashe wayar tare da yin wani tsallen murna.

************************************

Se ƙarfe sha ɗaya na safe tayi miƙa, ta farka daga nannauyan baccin da take, ta sakko daga kan gadonta magen ta yana biye da ita.
Corridor ɗin ɗakin ta tabi wanda ze sada ta da barandar benen, miƙa ta sake yi tana ambaton sunan Allah tare da shaƙar sassanyar isakar dake kaɗawa, haka nan take jin wai irin nishaɗi da bata san dalilin jinsa ba, tsyawa tayi tana kallon komai dake harabar gidan.

Yusuf ji yayi kamar ana kallon sa dan haka ya ɗaga kansa sama, ai kuwa karaf idanunsa suka sauka a cikin nata, alama tayi masa da hannu ya zo, dan haka ya miƙe ya tafi.

Dukda yana jin haushin abunda tayi masa akan kayan daya bata, amma yau yaga fuskarta ba yabo ba fallasa haka nan yaji hakan yayi masa daÉ—i.
A ɗakinta ya sameta, tana tsaye a gaban madubi ta janyo drower mudubin tana ƙoƙarin ɗakko wani abu.

Idan kunnuwan ta ba ƙarya suke gaya mata ba tabbas Yusuf cewa yayi "Good morning daughter" kamar yadda Daddyn ta yakan faɗa, shiru tayi ta cigaba da duba abunda take nema tsawon wasu daƙiƙu, sannan ta ɗago ta kalle shi tace "Roux taƙi cin komai tun jiya, na rasa meke damunta na bata Madara taƙi sha, ka siyo mata ko cabin ne, in gani in zata ci ban san me yake damunta ba" (wato magenta)

Haushi ne ya kama Yusuf, saboda tsabar wulaƙanci mage ze fita siyowa Abinci.
Bece komai ba ya juya ya fita yana ƙoƙarin ɓoye jin haushin sa.

Yana tafiya ya tuna da Message É—in da'aka turomasa da daddare dan haka ya samu guri ya kira Oga Suleiman.

Bayan sun gaisa Yusuf yace "Yallaɓai na so in shigo yau in nuna maka report ɗina amma abu ya gagara, Wannan rigimammiyar ta kasa ta tsare ban samu na shigo ba"

Suleiman yace "Aikam dan har na fara ƙorafin, yanzu me ake ciki?"

"Yallaɓai akwai abubuwa na ban mamaki a binciken nan, zan turomaka report ɗin ta Email ɗinka ka duba, Yallaɓai case ɗin akwai sa hannun mutanen dan ban zata ba, sannan karo na biyu ana min barazana wanda ya ƙara tabattar da tabbas ana bibiyar yarinyar nan ana son karɓar wani abu a hannunta wanda ni kaina ban san menene ba"

"Masha Allah, har kayi aiki haka Yusuf? Ka turo zan duba in Allah ya yadda inda yuwuwa zan miƙa report ɗin naka gaba, nasan zaka iya dama bazan can zaka daga kan aikin ba"

"Yallaɓai da karɓar aikin za kayi?"

"karka damu da wannan, ka turomin zan duba dan daga sama ana tambaya ta ina muka tsaya a binciken?"

Yusuf yace "Amma Yallaɓai wai wa yasa ayi wannan aikin ne? Waye yace ayi binciken?"

"Yusuf nima ban saniba, daga sama aka bada order ayi wannan aikin"

"Yallaɓai ya kamata kasan gawa zaka bada aikin, dan abun akwai sarƙaƙiya"

"Karka damu Yusuf, komai ze tafi daidai insha Allah, kamar yadda kace ana maka barazana, duk lokacin da ka buƙaci temako kayi magana, sannan ka kasance cikin shiri ka dinga yawo da makaminka"
"Ina lura sosai Yallaɓai, Allah yayi mana jagora gaba ɗaya"

"Ameen Yusuf Allah ya tsare"

Yusuf seda ya tsaya ya turawa Suleiman aikin sannan ya tafi.

Koda Yusuf ya dawo daga aiken yiwa mage siyayya, ya tarar da uwar É—akinsa ta fito daga wanka, pink É—in rigar wanka ce a jikin ta, ta naÉ—e gashin kanta da towel shima pink.

Zare towel ɗin dake kanta tayi, gashin ta ya zuba a kan kafaɗunta, Satar kallon ta Yusuf yake, tabbas Allah yayi mata halitta mekyau, tana da kyau sosai ga dogon gashi, Yarinya ce sedai izza da gadara, tana kallon Ya dawo amma taƙi kula shi.

Wani ƙaramin plate ta ɗakko ta miƙawa Yusuf tace "ka sa mata cabin ɗin anan, ga madara ka haɗa mata dashi"

Yusuf yai shiru yana sauraren ikon Allah, yanaji yana gani aka sashi haÉ—awa mage Abinci.

Still dai magen bataci ba se kwanciya da take.

Cike da damuwa Widad ta kalli Yusuf tace "taƙi cin wannan ma, inaga bata da lafiya idan akwai wani private veterinary se mu kaita" ta faɗa cike da damuwa tana sake shafa magen, hakan ya ƙara fito da tsantsar yarintar ta.

"waye ze buɗewa wani private veterinary? Babu wani private veterinary dana sani nidai, yunwa take ji kawai bata ƙoshi ne"

"kamarya? Ina bata Abinci sosai fa"

"Ai kema ba Abinci kike ciba balle magen, kullum abu É—aya ai dole ta gaji ta dena ci"

Cikin damuwa tace "to me zan dinga bata?"

"Abinci me nauyi na hausawa, amma kullum daga popcorn se madara ai dole ta mutu"
Da sauri ta kalli Yusuf tana girgiza kai tace
"A'a ni bana so ta mutu ina sonta fa"

Gaba ɗaya yau Yusuf cike yake da mamakin yadda take masa magana cikin nutsuwa ba izza, yasan kuma saboda magen ne, dan ya lura tana tausayin dabbobi fiye da yadda take tausayin ɗan Adam, tana matuƙar ƙaunar dabbobi Yusuf a ransa yace "ta wani fannin rayuwar turai ba tayi ba"

"to muke rasa 'yan uwanmu mutane ma balle dabba, idan ta mutu seki É—akko wata"

"Ni nafison wannan gaskiya, tun ire iren magunan Ammi ne, idan ta mutu zan shiga damuwa"

Shiru yayi yana kallon Widad data sunkuyar da kanta tana shafa jikin magen, magen tayi lamo a jikinta, gashin kanta har rufe mata fuska yake, Yusuf yana mamakin wannan dogon gashin na kan Widad dan har yanzu yana tantama idan nata ne.

A hankali ya matso daf da ita ya shafa jikin magen dake hannun ta yace "Allah ya bata lafiya, don't worry Madam zata warke Insha Allah"

Widad ta jinjina kai, tare da jin ƙaruwar bugun zuciyar ta kasancewar yadda suke daf da juna, ta ɗago idonta ta kalle shi tace "da ina so mu fita zanje Saloon, Amma zan zauna inga yadda jikin nata ze kasance ko zuwa yamma ne semu tafi"

Yusuf ya ɗan ƙura mata ido sannan a hankali yace "As you wish your majesty" ji tayi tsigar jikin ta tashi, wanda ta rasa dalilin jin hakan, haɗe rai tayi tace
"karka sake ka fita kaje ko'ina idan ba nina baka izini ba, ka zauna zuwa la'asar insha Allah zamu fita"
Murmushi yayi mata tare da ɗan duƙawa cikin girmamawa yace "Considered it done Gimbiyar Daddy"

Ya yunƙura ze miƙe Amal ta shigo hannun ta ɗauke da waya, turus tayi tana binsu da kallo, yayin da taji wani abu tundaga ƙafarta zuwa ƙirjinta ya to kare mata wuya.

Da ƙyar ta miƙawa Widad waya tace "gashi Daddy zeyi magana dake"
Widad bata kalle ta ba, bata bata amsa ba ta kalli Yusuf tace "bani wayata akan mirror"
Amal bata kuma cewa komai ba ta juya ta tafi a hasale.

Widad ta karɓi wayar ta kira lambar Daddy, ya ɗaga suka gaisa yace "Lovely meyasa wayarki bata shiga?"

"Jinyar Roux nake, bata da lafiya"

"To Allah ya bata lafiya, dama munyi waya da Daddynki yau baƙonki zezo"

"waye baƙona?"

"Fahad mana, zezo ya ganki ku gaisa dan Allah Lovely banda wulaƙanci ko makamancin haka, shima ɗanuwankine Yayan Ramadan ne, yana nan tafe Anjima Insha Allah"
Nan da nan dukkan annurin fuskarta ya É—auke ta dire wayar tace

"Ina nan ina jiran zuwan sa, yazo ya sami Widad Nasir Daula, yazo yaga mahaukaciyar da'ake shirin ƙaƙaba masa"

Ayshercool
07063065680

                     _*AƘIDATA*_
       

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

ELEGANT ONLINE WRITER'S

                         PART1
                                Page 18

Binta da Kallo Yusuf yayi, ganin yadda ta canza lokaci É—aya annurin fuskarta ya É—auke, tabbas akwai drama yau.

"Jeka anjima zamu fita" ta faÉ—a ba tare da ta kalli Yusuf ba

Miƙewa yayi ya fito daga ɗakin ya nufi hanyar fita, ba zato Amal tasha gabansa wanda ya tilasta masa tsayawa.
Chapter 42 · 0% Book details