← Book details Akidata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 82

Sashe 45

Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"maza ki ziga shi, wallahi duk wanda yayi yunƙurin kawowa auren nan cikas zega matakin da zan ɗauka, sannan kija masa kunne, wallahi idan yayi yunƙurin yi mata wani abu ta ɗaureshi wallahi ba zan sa baki a sake shi ba, kinji na gaya miki ku bar komai a hannuna nasan matakin da zan ɗauka"

Yai maganar tare da barin falon ya koma benensa

Yusuf kam tunda aka masa warning yaja bakinsa ya tsuke har sukaje suka dawo be kuma cewa komai ba, amma yana jinsa a ƙoshe saboda garar da ya kwasa yau.

Se bayan isha'i ya baro gidansu Widad, yanata sauri ya koma gida

Ba zato kawai yaga an saka masa wuƙa a saitin Ƙirjinsa, tasayawa yayi cak ba tare da yayi yunƙurin guduwa ba.

Kamar waccan ranar mutanen da suka tareshi ne suka sake tareshi.

"munzone dan mu cigaba da jadadda maka har yanzu muna bibiyarka, muna jiran karɓar wannan abun daga hannunka muna nan muna cigaba da sa maka ido da duk wani motsinka"

"Wai wani abune wannan kuke son karɓa? Ku gayamin in karɓo in baku ku ƙyaleni"

"An gaya maka bamu da lissafi ne? Ba zamu gaya maka menene ba, amma da zarar ka samu abun zamu sani, kuma zamu biyoka mu karɓa"

Suka koma cikin motarsu suka tafi, sedai sunyi ganganci dan tuni Yusuf ya É—auke lambar motar akansa.

Yau yaci sa'a basu dake shiba suka tafi suka barshi, gida ya tafi yana tunanin meye wannan abun da'aka damu se an karɓa a gurin Widad.

A haka har ya ƙarasa gida, Seda ya zauna sukayi hira da Ummansa dukda abubuwa sun cunkushewa ƙwaƙwalwarsa.

Ya gama cin Abinci ya tafi É—akinsa, dole zeyi tracking É—in lambar motar nan ya gano motar waye.

Da ya koma gida Ummansa taita mita akan daren da yake kaiwa a waje, yaita bata haƙuri yana rarrashinta sannan ya tafi ɗakinsa, ya nutsa a duniyar tunani sosai wayarsa ta fara ringing.
Lambar Sakina ce kamar kar ya É—aga, sekuma ya É—aga yasa a kunnensa tare da sallama.

"Yusuf baka yi bacci ba?"

"Eh banyi ba" ya bata amsa a taƙaice

"dama magana nake so muyi"

"Amma kinsan dare yayi ko?"

"eh nasani, maganar tana da mahimmanci ne a gareka"

Yusuf yace  "to ina jinki"

"Yusuf akwai buƙatar ka dinga taka tsantsan da wasu abubuwan, akwai mutanen da suke nuna suna tare da kai amma a bayan idonka suna cin dunduniyarka, ba kowane mutum ne aboki na gaskiya ba"

Yusuf yace  "nifa bana son irin wannan ƙananan maganganun, ni ina zaune da kowa lafiya"

"ba ƙananan maganganu bane ba, ka dai yi a hankali sannan karka yadda wani yasan sakamakon binciken da kake komai kusancinka dashi in ba yallaɓai ba shawara ce yakamata ka kula"

"Shikenan nagode" Yusuf ya faɗa cike da ƙosawa, shi sam baya san abunda ze haɗa shi da Sakina baya son mace mara kamin kai sam.

Amma nazarin maganganun ta  ya shiga yi, wayarsa ce ta sake ɗaukar ringing har yayi tsaki ze kashe wayar yaga lambar Alhaji Nasir.

Cikin ladabi ya ɗaga wayar suka gaisa da Baban Widad, Alhaji Nasir yace  "Yusuf meyefaru ɗazu da Fahad yazo gurin Daughter"
. Cikin kame kame Yusuf yace  "Amm.. Yallaɓai yazo sun gaisa"

"Yusuf karka kareta, ka gayamin gaskiya me tayi masa? Wace irin karɓa tayi masa?"

"da alama dai beyi mata bane, ta É—an dai nuna masa bata sonsa ne"

"Yusuf karka fara ƙarya saboda ka kare uwar ɗakinka, Bulama ya tabattar min da wulaƙanci tayiwa Fahad, kuma nasani zata aikata na kiraka ne dan in tabattar, saboda zan ɗau mataki na ƙarshe daya dace da ita, duk abunda nake dan gyaran rayuwar ta nake amma ta kasa ganewa, dan haka zan ɗau matakin da bata taɓa zata ba akanta wanda ze kasance hukunci na ƙarshe da zan yanke akanta "

Domin gyara sharhi ko shawara, feel free to contact me
Ayshercool
07063065680

                       _*AƘIDATA*_
       

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

ELEGANT ONLINE WRITER'S

                         PART1
                                Page 19_20

Gaba ɗaya Yusuf ya dirircei yace  "Amm... Amma Yallaɓai wani mataki zaka ɗauka haka akanta, ina fatan ba wanda ze mata tsauri bane?"

"Yusuf kenan, ka damu da al'amarin Widad haka nan naji na yadda da kai, shiyasa har nake saka a cikin abunda ya shafi rayuwar mu, na yanke shawarar tsayar da ranar Aurenta a ƙarshen wannan watan zuwa farkon wata me kamawa"

"Amma yallaɓai baka ganin hakan ze sake jefa rayuwarta cikin hatsari, duba da yadda babu Aure a tsarin Rayuwar ta?"

"Yusuf, Widad fa mutum ce kuma lafiyayyiya tana ƙin Aurene saboda wasu dalilanta da suke masu rauni a gurina, bana so in mutu in barta cikin kaɗaici, nasan Bulama baze taɓa barin ɗansa ya Wulaƙanta Widad ba ko bayan raina, dan Allah ka cigaba da yimana addu'a, Amma insha Allah ko ba taso zan ɗaura mata aure karo na farko a rayuwata da zan ɓata mata rai, amma ina fatan hakan ya zama alkhairi a gareta, Insha Allah gobe zuwa jibi zan dawk"

"shikenan Yallaɓai, Allah ya tabattar da alkhairi ya dawo da kai lafiya"

"Ameen Yusufa nagode sosai"

Tunda sukayi Sallama da mahaifin Widad abun duniya ya damu Yusuf, ji yake matakin da mahaifin Widad ke shirin ɗauka tamkar ƙarasa rugurguza rayuwar uwar ɗakinsa ne gaba ɗaya, matakin yayi tsauri sosai, haka nan yaji wani irin matsanancin kishi na taso masa game da Widad ɗin.

Dafe kansa yayi tare da faÉ—in "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Allah ka tsareni da sake faÉ—awa hatsarin Soyayya, Allah yasa tausayinta kawai nake ji, tabbas idan na fara son Widad zan shiga matsala fiye da wadda nasha a baya"

Bacci kam se Ɓarawo ne ya kama Yusuf.

Kwana biyu a tsakani Yusuf yana zuwa gidansu Widad amma ba wani aiki da yake yi, kuma sam baya ganinta.

Abubuwa sun ƙara cakuɗewa Yusuf, tunani kala kala a zuciyarsa amma zuciyarsa tafi fargaba akan hukuncin da Daddy ya yanke ɗauka akan Widad.

Ya ɗakko wayarsa yana ɗan duddubawa kawai yaga message ya shigo wayarsa, anyiwa ma'aikata canjin gurin aiki ciki harda Abbas, an maida Abbas aiki a kudancin Nigeria, abun ya ɗaurewa Yusuf kai sosai, mafi akasari anfi yin wa mutum wannan canjin aikin ne, kodai dan wani mahimmin bincike, ko ƙarin girma kokuma dan hukunci ga wani laifi da ya aikata, sedai shi a ganinsa babu ɗaya da Abbas yayi wanda zesa ayi masa wannan transfer.

Ba shiri Yusuf ya bar gidansu Widad ya tafi gurin aikinsu, kai tsaye ofishin Oga Suleiman ya wuce, gaje suka gaisa Suleiman yace  "Yusuf naga aikin daka turomin, kayi ƙoƙari sosai Yusuf sannan ina taya ka murna da sabon muƙaminka"

Yusuf cikin rashin fahimta yace  "Yallaɓai nida ban fahimci abun nan ba, me Abbas yayi za'a ɗauke shi daga gurin nan akaishi wata uwa duniya?"

"Nima ban san meyasa hakan ta faru ba, sedai daga sama ne akayi wannan transfer sannan ka samu ƙarin matsayi"

Yusuf ya dafe kai yace  "Yallaɓai babu yadda za'ayi a bar Abbas a gurin nan ne? Bekamata a raba shi da iyalinsa ba zuwa wata uwa duniya ba, ni dai banji daɗin hakan ba, zanyi kewar abokina kuma ɗan uwana"

Suleiman ya jinjina sauƙin kai irin na Yusuf yace  "ya za'ayi se haƙuri haka sha'anin aiki yake"

Jiki a sanyaye Yusuf ya baro office É—in Suleiman ya nufi na Abbas, se sarawa Yusuf ake ana masa murna amma shi sam hankalinsa yana kan wannan transfer da'akayiwa Abbas.

Da sallama ya shiga Office É—in ya tarar da Abbas yana ta tattara kayansa dake Office É—in.

"Abbas ya akayi haka? Me yasa akayi maka transfer haka ta gaggawa?"

Abbas yace  "nima ban sani ba Yusuf, jiya aka sanar dani kuma akace lallai gobe in Allah ya kaimu in tafi"

"yanzu babu wani abu da zamu iyayi a fasa wannan transfer É—in?"

"Yusuf nayi duk ƙoƙarin da zanyi amma abun ya gagara"

Gaba É—aya Yusuf ya rasa abunda yake masa daÉ—i, dan har cikin ransa yake jin rabuwa da Abbas É—in, dan yana jin Abbas tamkar wani É—an uwansa.

Wayar Yusuf ce ta fara ringing, ya É—akkota daga aljihunsa ya É—aga.

"Yusuf mai gida ya dawo yanzun nan, yace a kiraka"

"Shikenan gani nan zuwa"

Yusuf ya kashe wayar yace "Abbas zanzo gida insha Allah, zan ganka muyi sallama"

Abbas yace "Yusuf na ta yaka murna, an ƙara maka matsayi"

Yusuf yace  "Abbas sam bana murna da wannan ƙarin matsayin, ni tafiyarka ce damuwa ta, bari inje wannan kiran zan nemeka Insha Allah"

Sukayi musabiha, Yusuf ya juya ya fita, Abbas ya raka bayan Yusuf da harara tare da yin ƙwafa.

Tun daga harabar gidan Yusuf yaga manyan motoci da alama bayan dawowar maigidan anyi baƙi a gidan.

Kansa tsaye ya nufi cikin gidan, a falon ya tarar da Alhaji Nasir, Bulama, Fahad Hajiya Halima da iyalanta.

Yusuf ya ƙaraso yana gaishesu, Alhaji Nasir yace  "ƙaraso kusa dani Yayana, nace a kiraka aka cemin ka fita ne"

Yusuf yace  "eh naje wani uzuri ne"

Fahad se wani hararar Yusuf yake, shiko Yusuf ya basar kamar be gani ba.

Tsit falon yayi na wani lokaci, Yusuf ya rasa dalilin hakan, yana ɗaga kai yaga gimbiyar ta fito daga ƙofar part ɗinta, da alamu wannan zaman fitowarta ake jira, seda ta tsaya ta ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya sannan ta ƙaraso cikin takunta na isa, ta samu kujera ɗaya ta zauna ba tare da ta kula kowa ba.

Alhaji Nasir yace "daughter"

"Na'am Daddy"
Chapter 45 · 0% Book details