Sashe 2
Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ba tare da ya É—ago ba yace mata "be shigo ba"
Haka ta fita ta bar office ɗin gwiwa a saɓule tana tunani "komai za'ayi ba'a taɓa birge gayen nan daga shi har Yusuf, gara ma wannan akan waccan me kama da saƙagon da magana ma se ya ga dama yake yi" tai maganar a fili da sigar mita
Ya tattara system din ya kashe, ya É—auki wayarsa da mukullin motar sa, ya É—ora top É—in kayansa a kafaÉ—a da jakar sa ya fito ya nufi wani ofishin.
Yana shiga dayan ofishin ya ƙame cikin girmamawa ya sarawa wanda ke office ɗin da alama shugaban sa ne, be zauna ba seda aka yi masa izini sannan ya zauna suka sake gaisawa.
Mutumin ya É—ago ya kalle shi yace
"Abbas kana ganin babu matsala a wannan aikin da'aka baka kasan hatsarin dake cikin aikin zaku iya kuwa? Kana ganin akwai wani cigaba akan case É—in?"
Wanda aka kira da Abbas yai murmushi cikin girmamawa yace "karka ji komai ranka ya daÉ—e Insha Allah zan iya, zamu yi nasara, kuma ina fatan nasara Insha Allah yanzu idan na bar nan zanje in samu Yusuf
ne kasan shine jigon aikin"
"hakane to shikenan Allah ya tabbatar da Alkhairi ya baku sa'a na yadda da ƙwazon ku, Allah ya bada sa'a"
"Ameen yallabai muna godiya".
**********************************
Zaune yake Ya barbaza takaddu da na'urori masu ƙwaƙwalwa har biyu akan gadon sa ya tattaɓa wannan ya taɓa waccan, kafin daga baya yayi zugum yana kallon hotunan wata tsaleliyar yarinya, yarinyar wadda zata yi kimanin shekaru goma sha takwas sanye take da farin gajeren wando, se wata 'yar riga a jikin ta itama fara, ta saka farar hula hat ta baza gashin da ya kasa tantance nata ne ko na sawa ne, ga ƙaton baƙin tabarau a idonta ta buɗe fararen haƙoran ta tana dariya, bayan ta wani irin makeken ruwa ne shuɗi sosai, hannun ta na hagu riƙe da igiya da aka saƙalo wuyan wani jibgegen kare, jikinsa fal farin gashi ƙal, ba ƙaramin kyau yarinyar tayi a hoton ba. ko ƙwakwaran motsi ba yayi hotunan kawai yake dubawa kaman yana ƙoƙarin gano wani abu a jikin hotunan.
Wayarsa ce ta fara ruri, wanda ya sashi dawowa daga dongon nazarin da yake yi, ya duba wanda yake kiran wayar tasa yaga sunan Abbas akan Allon wayar tasa, yasa hannu ya kai wayar kunnen sa yace "Assalamu Alaikum warahmatullah"
Daga ɗaya bangaren aka amsa sallamar sannan wanda ya amsa din ya ɗora da cewa " ina ƙofar ɗakin ka kana cikine in shigo? akwai labari da nazo maka dashi"
"eh ina ciki shigo kawai"
Kafin ya kashe wayar aka turo ƙofar akayi sallama a ɗakin nasa, tashi yayi zaune ya aje wayar yana faɗin
"kai tun shekaran jiya daka turomin hotunan wata yarinya bamu kuma haɗuwa ba, kuma ka kashe wayarka, gashi saboda aikin nan ko Office bana zuwa ina ta ƙara bincike, ina ka shiga haka?"
Abbas yace "ka bari in zauna se in maka bayani sarkin ƙorafi"
"to zauna maza ka koramin bayani, wani labari kake tafe dashi?"
Abbas Ya samu guri ya zauna ya ajiye jakarsa ya tattara hankalinsa kan Yusuf sannan yace
" Yusuf kaga hotunan yarinyar dana turo maka dasu ta email É—inka?"
"Eh nagani, su nake ta nazari ban san dalilin da yasa ka turo su ba"
Abbas ya gyara zama yace "
hotunan 'yar gidan Alhaji Nasir Daula ce, kusan aikin mu gaba ɗaya akan ta yake, sati biyu kenan ina zuwa ina gidan su a matsayin me saida mangwaro da yankan farce, na samu karɓuwa a gurin megadin gidan su, hakan yasa idan naje se in zauna muyi ta hira da megadin su sannaan in tafi"
Yusuf ya gyara zama yace "to aini banga Alƙar binkicen mu da ita ba"
"Injiwa ai ta hanyar ta zamu samu duk abunda muke so, ita kaɗaice 'yar Alhaji Nasiru, kuma itace target ɗin maƙiyan sa, aikin mu ba' a akan iya bincike bane hadda bata Kariya"
Yusuf yace
"Abbas sanin kanka ne binciken nan na sirri ne, shi kansa Alhaji Nasir be san ana yin shi ba ta yaya zamu bawa 'yarsa kariya"
Abbas yace "Yawwa ɗan gari bazata taɓa sanin Aikin da muke ba, yadda mahaifinta be sani ba itama baza ta sani ba, a hirar da muke dame gadin su yau watan ta uku da dawo wa daga America a can take Rayuwar ta, maman ta ta rasu a hannun step mum ɗin ta take, a tsawon lokacin nan mahaifinta ya sangar tata da kuɗi a taƙaice dai muguwar taɓararriya ce me wata irin AƘIDA ta kafiya da taurin kai ga mugun tsatstauran ra'ayi kamar baturiya, yarinya ce da bata da yadda tafi bawa mage da kare mahimmanci fiye da mutanen dake kusa da ita, bata san zafin talauci ba balle tayi wa wani talaka uzuri ko ɗaga ƙafa hasali ma gani take kaman talakawa bayin sune masu kuɗi bata ɗaga ƙafa ko sassauta wa na ƙasan ta san.....
"kaga dakata wannan dogon labari haka, kamin bayani a taƙaice" Yusuf ya katse shi
Abbas yace "Dadina da kai ƙosawa, hotunan dana turo maka hotunan tane"
Yusuf yace "to me zanyi dasu?"
Abbas yace "Yawwa anzo gurin, da dawowar ta a wata ukun nan direbobi biyar aka sallama saboda baza su iya jure halin ta ba, tana da gadara da wulaƙanci, a gabana tayi wa direban ta korara wulakanci jiya, Yanzu haka megadin ya bani labarin mahaifinta yasa shi ya samo mata wani direban daze dinga kaita unguwa, yake gayamin ya gaji da samo mutane tana wulaƙanta su, akwai Albashi me kyau amma halin ta da AƘIDAR TA kesa mutum ya gudu da kansa, dan haka nace ni ya barni zan samo mata direba, kuma kai nake so ka zama direban nata!!"
Wani mugun kallo Yusuf yayi wa Abbas
"Ashe baka da hankali, kaime ya hana kaje ka zama direban nata?, ni zanje in dinga tuƙa ƙaramar yarinya tana wulaƙanta ni akan me? Bazan yi ba gaskiya, ai kaine gaba dani a gurin Aikin kai kaje mana"
Cikin sigar rarrashi Abbas yace
"Calm down brother, nasan zaka iyane kai ƙarshe ne gurin haƙuri, kaga ni bani da haƙuri zan iya lakaɗa mata duka idan tayi min ba daɗi ƙarshe in ƙare a prison in shiga uku, kaikuma kowa ya san ka akan haƙuri da hikima, dan haka zaka iya, ɗazu mukayi magana da Yallaɓai na tabattar masa zamu iya aikin nan, ita kanta yarinyar a cikin gagarumin hatsari take, akwai bukatar a bata kariya da kulawa "
Ɗan tsaki Yusuf yayi yace" gaskiya ni bana son wulakanci ne, yarinya ƙarama ta wulaƙanta ni dan ni talaka ne, gaskiya ni ka gama dani daka haɗani da wannan aikin, daka barni da kayan computers ɗina da damuwar da nake ciki da se yafi min"
Abbas ya kuma gyara zama yace "cigaban mu ne idan mukayi nasara dan Allah ka daure, Sannan Yusuf lokaci yayi da zaka cire damuwa ka fuskanci Rayuwa ka manta da ƙalubale ka gina Rayuwar ka"
Cikin takaici Yusuf yace
"Abbas kenan kana yiwa matsala ta kallon ƙaramar matsala, amma Allah shi ka ɗai yasan zugi da Raɗaɗin da nake ji a raina idan na tuna ni wane ne, wace Rayuwa zan gina bayan bani da dirakun da zasu riƙe min ginin Rayuwar tawa? Abunda ya faru dani yasa naji komai yafi ta daga raina, yanzu na barwa Allah al'amura na, in riƙe mahallici na, in rungumi ummana da Aikina nasan bani da kamarsu"
Abbas ya dafa kafaɗar Yusuf yace "Yusuf nasara bata samuwa ba tare da an jarabci ɗan adam ba, kayi haƙuri da taka ƙaddarar, Allah yana sane da kai"
Yusuf yace "Hakane Allah yabani ikon cin jarrabawa"
Abbas ya amsa da Ameen, sannan ya É—ora da cewa
"Aiki na gaba se bayan ka zama direban ta sannan zan sanar da kai shiri na gaba, zan gaya maka aikin da'a ke so kayi"
Yusuf yace "to Allah ya bani iko ya tabattar da alkhairi ya bamu nasara"
"Ameen ya Allah, É—azu fa mutuniyar ka tazo office É—ina tana ta kwarkwasa, take tambaya ta kana ina?"
Yusuf yace "wa kenan?"
"kafini sani ai, wacece in ba Sakina ba"
Tsaki Yusuf yayi yace "dan Allah Abbas ka dena sa kamin wannan yarinyar cikin lamurana, ni tun abunda ya faru dani duk wata harka da mata gudun ta nake yi, wannan aikin ma da kuka bani kaida yallaɓai dan ba yadda zanyi ne harka ce ta aiki, balle wata Sakina, ni ina tsoron mata nafi ƙaunar tsira da mutunci na da kuma tsayawa matsayin da Allah ya ajiye ni, nayi darasi akan abunda ya faru dani"
Abbas yace "hakane kana da gaskiya Yusuf, Amma ka sani idan har mukayi nasara a Aikin nan cigabanka ne, sekafi kowa benefitting gaba kaɗan in aikin ya kankama zan ƙara sanar da kai wasu abubuwan"
Abbas ya ci gaba da kwantarwa da yusuf hankali tare da lallaɓa shi har ya ƙara gamsuwa ya Amince Amince akan zasu je gidan Alhaji Nasiru Daula da weekends domin a tantance shi in ze iya zama direban Wannan yarinya me muguwar AƘIDA sannan a gabatar da Yusuf a matsayin Sabon direban wannan 'yar Hamshaƙin Attajiri Me murɗaɗiyar AƘIDA!!!.