← Book details Akidata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 82

Sashe 5

Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abbas da Isa suka dinga É—auka suna ci suna kallon tv, shikam Yusuf ya kasa cin komai, gaba É—aya a takure yake, gashi ko É—aga kai baya son yi saboda kallon da'ake masa.

Kaman ance ya ɗaga kai idonsa yayi tozali da wata irin kyakywar halitta, babu shakka itace a jikin hoton da Abbas ya tura masa, Amma a zahiri tafi haka kyau, gabansa ne ya dinga faɗuwa ƙirjinsa yana bugawa da ƙarfi, yarinya ce sharaf amma se kwarjini fara ce ƙal tana sanye da skin tied iya gwiwarta, se wata over size shirt data saka har wajen gwiwarta, kanta babu ɗan kwali gashin ta a hargitse babu ribbon, ta sake shi a kafaɗun ta.

Fuskarta a haɗe babu annuri, ta ƙaraso cikin falon ta zauna kusa da mahaifin ta. Tana zama Hajiya Halima ta miƙe ta canza wata kujerar

Alhaji Nasir yace "Lovely daughter ina fatan ba'a takura miki ba?"

Girgiza masa kai tayi alamar A'a

Alhaji Nasir yace "Sabon driver ne gashi nan, yazo ki gani in yayi miki"

Kamar baza tace komai ba ta ɗago ta kalle su ɗaya bayan ɗaya ta tsaida idon ta akan Yusuf ta ɗan ɗau lokaci tana kallon sa kaman tana ƙoƙarin gano wani abu.
ÆŠauke kai tayi ta haÉ—e rai cikin isa tace

"Ramla kawo min madara da cup, sannan kije falona ki kawomin wata folder akan kujera"

Waigawa Yusuf yayi ya Kalli wadda aka kira Ramla,  ta girmi yarinyar da har yanzu be san sunan ta banesa ba kusa ba, dan shi har yanzu beji wanda ya faɗi sunan ta ba,  ramla ta miƙe ta tafi cika umarnin ta.

Yarinyar da dudu bata fi shekaru sha takwas zuwa sha tara ba, a idon ta da yadda take magana zaka gano tsabar izza, da isa, Ta kalli Abbas tace "kai kaman na sanka ko?"

Abbas yace "eh ni abokin Bala ne, ina zuwa gurin sa"

"good, kai Bala meye aikin ka?"

Cikin Rawar jiki yace "gadi ranki ya daÉ—e"

"to ka tashi da kai da shi ku fita ka koma kan aikin ka"
Ba musu bala ya miƙe, Abbas ma ya miƙe, kafin su bar falon  ta kalli Hajiya Halima tace

"Madam i need privacy you can leave"

Ɗan taɓe baki Hajiya Halima tayi ta miƙe ta nufi wata ƙofar daban.

Ta kalli inda Amal take ta mata wani kallo, tun kafin ta furta komai Amal ita ma ta miƙe ta nufi barin falon.

Gaba É—aya mamaki ya cika Yusuf, yadda take wannan izzar take wa manya magana babu respect kuma a gaban mahaifin ta amma bece komai ba, ya ma maida hankali akan jaridar sa kaman be san me take yi ba.

Ramlah ta dawo ɗakin ɗauke da cup da madara  tazo ta ajiye, sannan ta miƙa mata folder, taje ta nemi guri akan  kujerar da ta tashi zata zauna, Amma suka jiyo zazzaƙara muryar ta tace

"wait don't sit, get out from here, bana buƙatar wani a falon zan gana da shi"

Wata irin Ajiyar zuciya Ramlah tayi ta ɗan jinjina kai ba tare da ta waigo ba ta miƙe ta fita ta bar falon itama.

Madarar ta ɗauka ta zuba  a cup tana sha, tana kaɗa ƙafa kaman tama manta da Yusuf a gurin.

Alhaji Nasir ya kalle ta yace "gimbiyar Daddy bari inje in É—an watsa ruwa zan fita anjima, yadda kuka yi dashi kya gayamin in na dawo, in yayi miki.

ÆŠan É—aga girar ta É—aya tayi ta lumshe ido ba tare da tace komai ba.

Bayan tafiyar mahaifinta haka suka ci gaba da zaman kurame ita da Yusuf

Can ba zato ba tsammani yaji tace

"what's the level of your Education?"

Yusuf ya ɗanyi jim sannan yace "secondary school" yai maganar ƙirjinsa na bugawa

Shiru ta kuma yi tana kallon tv seda aka kuma jan wani lokacin sannan ta kuma cewa
"Meye sana'arka?"
Gumi ne ya fara tsatstsafo masa dukda sanyin AC da yake ɗakin, Yusuf baya son kuma yin ƙarya, Amma yace

"Eh ina É—an zuwa kasuwa ne ina yaron shago"

Cikin Tsara magana da take daki daki, da muryarta me sanyi tace

"Anyway naga kaman za kayi hankali, zan iya yadda ka zama direba na amma ina da sharuÉ—ai"
Ta É—anyi shiru kaman ba zata kuma magana ba, sannan ta É—ora

"bana son ƙarya, duk ranar da na gano kayi min ƙarya zaka fuskanci hukunci me tsauri, bana son sa ido da shishigi a cikin lamurana, bana yafewa maƙaryaci ko wanda yaci amana ta, babu ruwan ka da irin mutanen da nake hulɗa dasu, bana yadda da mutum kowaye ni kaina wani lokacin bana yadda da kaina balle wani, dan haka duk lokacin da kayi motsin da ban yadda da shi bama zan iya sawa a kulle ka, ban yadda da saɓa lokaci ko Alƙawari ba, sannan lokacin dana ɗauke ka aiki mallaki na ne bana ka ba, ibada kaɗai kake da 'yancin yi, bayan wannan baka da hurumin yin wani aiki idan ba nawa ba, se dai idan ni na baka dama, in ka amince da sharuɗai na" ta ajiye wata takadda

"kayi signing anan, salary 200k and your hard work determines your salary promotions"

Shiruu Yusuf yayi yana tunani, gaba É—aya ya rasa abun yi
Yusuf yace
"ranki ya daÉ—e ko zaki iya bani dama inje inyi shawara"

"I don't gives second chance, and I don't want too much waste of time" ta bashi amsa tana maida hankalinta kan talabijin

Shiru Yusuf ya kuma yi ya É—auki takardar yana jujjuya ta ba tare da ya karanta meye a jiki ba, gumi se karyo masa yake ya ciro biro a Aljihun sa, hannun sa na rawa ze sa hannu yaji tace

"that means you accept the terms and conditions i have mentioned?"

Jinjina kai yayi alamar yana ƙoƙarin ya saka hannu tace

"if you are here to spy don't sign this paper"

(idan kazo nan ne dan leƙen Asiri kar kasa hannu a takardar nan)

Ras! Gaban Yusuf ya faɗi, Anya babu wata a ƙasa, yarinyar nan bata san komai ba? Cikin ƙwarewar Aikin sa ya dake  yace

"ranki ya daÉ—e menene Spy kuma?"

Banza tayi masa ba tace komai ba.

Seda Yusuf yayi Addu'a a zuciyar sa sannaan yasa hannu akan takardar.

Ta sa hannu ta É—auki takardar ta jujjuya ta sannan tace

"signing this paper is like signing on your death contract!!! Jeka sena neme ka"

Tana gama faɗin haka ta miƙe ta bar falon

Ras! Ras!! Ras!!! Gaban Yusuf ya faÉ—i
A fili yace "My death Contract kuma?"!!!

Ayshercool
07063065680

                      _*AƘIDA TA*_

                 
                *PART1*      
                            _Page 3_

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Special thanks to my Association Members
Perfect writers Association

Maimaita death contract Yusuf ya dinga yi, ya rasa abunda ya kamata yayi, a hankali ya miƙe ya biyo hanyar da Isa ya biyo da su ya fice.

Abbas yana tare da Isa yana jiran fitowar Yusuf, kallo ɗaya Abbas yayi masa yasan akwai matsala, da ƙyar Yusuf yake ɗaga ƙafarsa,  Isa da Abbas suka dinga tambayar sa meyafaru? Amma yaƙi cewa uffan, Abbas yayi wa Isa Sallama ya ja Yusuf suka tafi, be ƙara tambayar Yusuf ba har suka je gidan su Yusuf.

Da suka je gidan ma Yusuf yai mursisi yaƙi faɗa wa Abbas yadda suka yi, daga ƙarshe dai Abbas ya ƙyale Yusuf ya ɗauka ire iren wulaƙanci ya fara fuskanta, dan haka yaita bashi haƙuri yana kuma rarrashin sa kan ya daure kar ya karaya.

Sam hankalin Yusuf baya kan Abbas, gaba ɗaya ƙwaƙwalwar sa ta shiga lissafe lissafe daban2, a karon farko da shigar sa Aiki wannan ne aiki me matuƙar wahala da sarƙaƙiya a gare shi, yana buƙatar nutsuwa da taka tsantsan akan komai.

"Yusuf naga kaman hankalin ka baya kaina fa?"
Yusuf yayi ajiyar zuciya yace "ta yaya zaka samu hankali na, tace ba'a mata ƙarya bata yafe wa wanda yayi mata ƙarya, Nikuma akan ƙaryar ma naje nake aikin, yanzu idan ta gane gaskiya fa?"

Abbas yace "karka damu kayi abunda ya kamata kawai tana ƙoƙarin yi maka ba razana ne, idan kabi a hankali ba zata gane komai ba"

"to Allah yasa?"

Abbas yace "Ameen"

Bayan tafiyar Abbas fa tunani ya auri Yusuf, kasa jurewa yayi seda ya gayawa Umman sa aikin daze jeyi a matsayin direba gidan Alhaji Nasir Daula amma ya ɓoye mata gaskiyar halin yarinyar da sharuɗai da ta saka masa.

"Yusuf wace irin lalacewa ce kana aikin ka gwanin sha'awa zaka koma wani direba?"

"Umma ba lalacewa bace, harkar aiki ce ta kawo haka"

"hakane amma ni bana son sabga da masu kuɗin nan yaran su ba tarbiyya suka cika ba, bana so a wulaƙanta min ɗa a banza, gurin aikin naku babu wanda zasu saka se kai"

Yusuf yace "Umma Addu'arki da goyon bayanki nake buƙata, idan kika soki abun zaki kashe mun gwiwa ne"

Umma ta numfasa tace "shikenan Allah ya tabattar da Alkhairi, Allah yabada sa'a, ka kula da kanka"

"insha Allah umma na nagode sosai"

'yan kwankin nan Gaba ɗaya bacci ya ƙauracewa idaniyar ta, duk motsin da zata yi surar Yusuf take gani, rashin walwalarta da yawan son kaɗai cewa ne yasa 'yar uwatta lura da akwai abunda yake damun ta kasancewar ta me surutu da san hira.
Ramla ta dubi yadda' yar uwar tata tayi shiru tana jujjuya spoon a cikin cup ko sau É—aya bata kai abunda ke kofin bakin ta ba, bayan shafe kusan mintuna goma da zaman da tayi da niyyar cin Abinci.

"Amal wai me yake damunki haka ne, na lura tun jiya kin zama wata iri"
Chapter 5 · 0% Book details