Sashe 22
Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ta yaya za'a bawa mutum kariya ba tare da sanin sa ba? Kaima kamar baka san aikin naka ba?"
"Umma nasan aiki na, Amma nima umarnin manya na nake bi, wataƙila be kamata in sani bane"
"Hakane amma kayi taka tsan tsan, naji tausayin yarinyar nan, Amma ni jikina yana bani wani abu game da aikin nan da aka saka, Amma kasa gane ko menene, ina dai yi maka addu'a a duk inda kake Yusuf, ni dai fatana ka kula da kyau"
"Insha Allah Umma na"
Haka suka cigaba da taɓa hirarrakin su na ɗa da uwa.
Sosai tunani ya auri Yusuf, maganar Umma tana bisa hanya, waye wannan da ya nemi a bawa Widad kariya a ɓoye, dole akwai wata a ƙasa.
*******************
Washegari da safe, Yusuf ya koma gidan su Widad, bayan sun gaisa da su Nura, Yusuf yace "Nura ya jikin uwa É—akina kuwa?"
Nura yace "ta yaya zamu sani? Kaine dama aka É—auka mutum a gidan nan, da kai ake komai mu ina zamu san wani abu? Ai kaine mutum a cikin mu"
Yusuf yayi Murmushi ya samu guri ya zauna. Murtalah ya ƙaraso inda Yusuf yake yana faɗin "Malam Yusuf, ɗazu Alhaji ya leƙo yana tambayar ko kazo, dama yace in kazo a shiga da kai ɓangaren sa"
Yusuf yace "shikenan babu laifi, muje"
Murtalah yayi gaba Yusuf ya bishi a baya, Sam Yusuf be taɓa sanin da wannan ɓangaren a cikin gidan ba, gjda se kace ba'a duniya ba, Yusuf ya buɗe ido yana bawa idonsa Abinci.
Suna shiga Ƙaton falon, Murtalah yace
"to ni na tsaya daga nan, dan bani da ikon ƙarasawa ciki, seka fito"
Seda Yusuf ya gama waige2 sannan ya kalli ƙatuwar ƙofar dake cikin falon, a hankali ya taka yaje ƙofar ɗakin ya ƙwanƙwasa tare da yin sallama.
Alhaji Nasir ne ya amsa tare da cewa "Shigo"
Yusuf ya tura ƙofar ɗakin ya shiga, Alhaji Nasir ne zaune Widad ta ɗora kanta akan cinyar sa, idonta biyu tana ta jujjuya ƙwayar idon ta, gefe kuma Alhaji Bulama ne zaune a kusa da Alhaji Nasir.
Yusuf ya durƙusa yana gaishe su, Alhaji Nasir ya faɗaɗa murmushinsa yace "Me babban suna, ashe kazo?"
"Eh nazo ranka ya daÉ—e, yame jiki"
Alhaji Nasir yace
"Jiki da sauƙi, Alhamdilillah an samu ta dawo hayyacin ta, Amma taƙi magana sam"
Yusuf ya kalle ta yace "Sannu ya jikin naki?"
Haɗe rai tayi ta tura baki tace "Malam ni lafiya ta ƙalau"
Alhaji Bulama ya jinjina kai yaceÂ
"gaskiya akwai ka da sa'a, tun ɗazu muke magana taƙi kulamu amma kai gashi tayi maka magana"
Alhaji Nasir yace "My lovely, kin san wannan?" yai maganar yana nuna mata Yusuf
"Daddy nifa ba mahaukaciya bace"
Daddy yace "Ai na sani Babyna, tambayar ki kawai nayi"
Ta tura baki tace "Nasan shi"
Alhaji Bulama yace "to waye?"
"Direba ne" ta bashi amsa a taƙaice.
Daddy yace "direban wanne daga ciki?"
Maimakon ta basu amsa seta kalli Yusuf taceÂ
"kai ka gaya musu niba mahaukaciya bace, naga suna yadda da maganar ka, wallahi ni ina da hankali"
Yusuf yace "ai dama basu ce ke mahaukaciya bace, kina da hankali"
Ta kuma cewa "ka gaya musu wani na ƙoƙarin kasheni a gidan nan, ka cewa Daddy dan Allah ya ƙyaleni in koma England"
Yusuf yace "Shikenan ki kwantar da hankalin ki, zan gaya musu Insha Allah"
Alhaji Nasir yace Â
"Naga taku tazo É—aya da Yusuf Lovely, kamar shi kin yadda da shi ko?"
"Allah ya kiyaye, direba ne kawai, yana nan a matsayin sa na direba, karma ka faÉ—i wani abu da zesa yaji cewa shi na musamman ne, ko yana da wani matsayi, i don't trust anyone"
Alhaji Nasir ya girgiza kai yace "Yusuf nagode sosai, zaka iya tafiya abunka kaje ka huta, dama na kiraka ne in ƙara maka godiya nagode"
Yusuf yace "Ai babu wani abun godiya da nayi Yallaɓai, Allah ya bata lafiya"
Suka yi Sallama ze tafi, sedai yana ƙoƙarin barin ɗakin, Hajiya Halima ta shigo da tray da kayan marmari a kai, tana ganin Yusuf ta haɗe rai ta bishi da wata uwar harara ba tare da ta bari Alhaji Nasir yaga hakan ba.
Yusuf ya kama hanyar fita, yaji ance "Yusuf ashe kazo?"
Ya juyo ya kalli inda Amal ke masa magana yace "Eh nazo, tun ina ciki na duba jikin Madam ne"
Amal tace "shikenan É—an jirani ina zuwa"
"to shikenan bari in jiraki a waje" Yusuf ya koma harabar gidan yana jiran fitowar Amal, mintuna kaÉ—an sega Amal tazo, kaya ne a jikin ta wanda sukai matuÆ™ar matsarta, ta dube shi taceÂ
"dan Allah so nake muje gurin shan ice cream tare, Akwai maganar da nake so muyi"
"Kina ganin ba matsala kuwa? Kinga wancan karon, Madam bata ji daÉ—in fita da mukayi tare ba"
"Shikenan idan ba zaka iya min Alfarma ba, na fasa zuwa"
ÆŠan shiru Yusuf yayi yana nazari a ransa, tabbas Amal bata da wayo sosai, idan ya bugi cikin ta ze samu bayanai, dan haka ze iya shanye masifa da tsiwar Widad, a fili yace "shikenan kawo car keys É—in naki mu tafi"
Ta kalle shi tayi fari da ido tace "Dan Allah meye matakin karatun ka ne? Ka iya turanci Yusuf"
ÆŠan basarwa kawai yayi murmushi ya nufi inda motocin suke.
Wani Joint tasa ya kaita, tayi ordering Pizza da tea, ta tambayi Yusuf me zeci yace shi baya cin komai.
Yusuf ya kalleta yace "Wai ya naganki duk wata iri ne yau?"
Ɗan taɓe baki tayi tace "ba lafiya ba, shine ko ka tambayeni ya jikina? bayan a gabanka Widad ta ƙonani jiya ba abunda kayi, baka damu dani ba, Amma nasan saboda rashin lafiyar ta yasa kazo da wuri yau" ta ƙarasa maganar tana tura baki
Yusuf ya É—anyi Murmushi yace
"kiyi haƙuri, kinga bata da lafiya wani mataki zan ɗauka akanta? kuma kinga kaman mamanki da Yayar ki basa Son ina yawan shiga al'amuran gidan ku"
Amal tace "ba Al'amuran gidan nan ne basa son kana shiga ba, Al'amarin Widad ne da kake nuna damuwa dashi sosai ne basa so, ko baka ga Yadda take Wulaƙanta mutane ba?"
"Eh amma, ita ina maman ta ne take rayuwa ita kaÉ—ai?"
Amal ta ɗan taɓe baki tace "Kashe ta akayi fa, shine dalilin da yasa ta zama mahaukaciya bata son mutane"
Zare ido Yusuf yayi kamar besan komai ba yace "waye ya kashe ta?"
Amal ta taɓe baki tace "Oho wayasani? Kana gani dukda mahaifinta yana da kuɗi amma a binciko wanda yayi laifin abu ya gagara, shi ne ita kuma tace zata nemo wanda suka kashe mahaifiyar ta, akwai mutanen data sa aka kama aka kulle a prison ba tare data nada wata cikkakiyar hujja ba, dan haka itama ake farmakinta, sannan akwai wani abu da'ake so a karɓa a gurin ta wanda nima ban san komenene ba, Shiyasa nake gujemaka yawan Shiga lamarin ta bayan Aƙidarta ta Wulaƙanta mutane, duk randa ka bari wani kusanci me ƙarfi ya shiga tsakanin ka da ita, ba shakka za'a fara farmakin rayuwar ka domin za'ace kasan inda abunda ake nema a gurin ta yake, shine death Contract ɗin data gaya maka ai!!!"
IN AN KARANTA AYI SHARHI PLEASE
SANNAN AYI SHARE
07063065680
Ayshercool.
          Â
 Â
            _*AƘIDATA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *
I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
ELEGANT ONLINE WRITER'S
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in
           PART1
               Page 10
Shiru Yusuf yayi yana bin Amal da kallo, tare da nazarin maganganun ta.
"Waye ya kashe Mahaifiyar Widad? Me yasa aka kasheta!!? Meyasa ake bibiya da barazana ga dukkanin wanda yake da kusanci da ita!!!? Meye dalilin rushewar binciken wanda suka kashe mahaifiyar Widad? Meye Alaƙar kisan Mahaifiyar Widad da wanda Widad tasa aka ɗaure!!!? Meye alaƙar ciwon Widad da ƙwayar dake cikin tea ɗin da'aka kawo mata?
Wannan sune jerin tambayoyin da suka shiga kaiwa suna komowa a cikin ƙwaƙwalwar Yusuf.
Ta ɗago ta kalli Yusuf tace "let's keep this aside, Yusuf ka taɓayin budurwa? Ko kana da budurwa a halin yanzu?"
Jin tambayar Yusuf yayi wani banbarakwai, ta tuna masa da abu mafi ciwo a rayuwar sa da baze manta ba har ya koma ga Allah, ya kalle ta ya ɓoye damuwar sa yayi murmushi yace "Budurwa kuma? Wacece zata so talakan mutum kamata? Ni bani da wata budurwa ni kaɗai ne, ai nayi ƙarami inyi budurwa"
Murmushi tayi tace "ka fiye abun dariya, a haka kamar baka magana, Amma ka iya sa mutum dariya, yanzu babba da kai kace kayi ƙarami da budurwa?"
"Eh mana ko dan kin gani ƙato? Yarone ni ƙarami"
Ta sake yi masa wani murmushin tace "hmm Shikenan, kodai Widad kake so?"
Zare ido yayi kamar idon ze faɗo yace "Ni, rufamin Asiri, inani ina 'ya' yan manya, ai iyakacin talaka daku yayi muku aiki ku biyashi"
"Amma meyasa kake nuna damuwar ka a kanta haka? Dukda tarin wulaƙanci da rashin mutunci da take maka a wasu lokutan?"
"Saboda batamin wulaƙanci se idan na saɓawa umarnin ta, kuma mahaifinta yana matuƙar mutuntani, kuma kinga nine a ƙarƙashin
ta, dole inyi haƙuri da duk abunda zata yi min"
Amal ta numfasa tace "hakane, Amma ina shiga matuƙar baƙin ciki a duk lokacin da naga tana cin zarafin ka, shiyasa nake ganin meze hana ka ajiye mata aikin ta, in samo maka wani aikin ka huta da wulaƙanci?"