← Book details Akidata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 82

Sashe 78

Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka Widad ta raba dare ba tare da tayi bacci ba, data motsa sedai tayi ta shafa masa ruwa, amma jikinsa kamar wuta.

Tun tana yi da ƙarfinta, har bacci ya mamaye idonta ta kife a gurin tana bacci, a haka ya janyo ta jikinsa, yana kaɗe mata sauro yayin da ya kasa bacci saboda azabar ciwon gaɓoɓi da zafin zazzabi.

Da Asuba Widad ta farka, tana buÉ—e ido tace "Yoseef"

Da Mm ya amsa mata.

"baka yi bacci bane?"

"Nayi ya faÉ—a a hankali"

"ya jikin naka?"

"Naji sauƙi, samomin ruwan Alwala"

Ta miƙe ta fita waje, ta kawo masa ruwa yayi alwala yayi sallar Asuba.

Gwaggo tayo kunu ta aikowa da Yusuf, kasa sha yayi saboda yana jin jiki, amma saboda kukan da Widad take, ya karɓa ya sha kaɗan, haka nan ya amayar da shi gaba ɗaya, nan fa abun duniya ya ishi Widad, ta kasa cin Abinci se kuka.

Megari ya tashi É—ansa, yace "yaje can gaban su, ya aro babur azo a tafi da Yusuf Asibiti"

Har wajen ƙarfe sha ɗaya Widad tana tare da Yusuf, ko tsakar gidan ta kasa fita, ta kama yatsunsa tana ja masa a hankali kamar yadda yake mata, sam taƙi cin komai.

Wajen sha biyu na rana Saleh yazo gidan, zuwan Saleh ba ƙaramin daɗi yayi mata ba, Megari yace "Alhamdilillah, kazo a dai dai, dama Yusuf yana kwance babu lafiya na aika azo ds babur a kai shi Asibiti, tun jiya ko magana baya iyayi"

A gigice Saleh ya tafi ɗakin su Widad,  Hindu da Hanne dasu Gwaggo suka bishi dan a yanke shawarar ƙarshe game da rashin lafiyar nasa, Saleh yayi Sallama Widad ta amsa, ya shiga ɗakin ya tarar da Yusuf ya ɗora kansa akan cinyar Widad, idanunta sunyi ja har sun fara kumbura.

Seda Saleh ya É—anyi turus dan tabattar da abunda yake gani, wanda ko a wasan kwaikwayo akace Widad zata yi hakan baze yadda ba.

Ya ƙarasa cikin ɗakin, ya kalli Widad yace "meyasa me shi haka?"

Tsuke Fuska tayi sannan tace "zazzabi yake"

Ya kalli Yusuf yace "Sannu Yusuf, bari inje wannan sedai ko mota a samu, ba zaka iya hawan babur ba, se inzo akaika Asibiti"

Yusuf be iya cewa komai ba, se jinjina masa kai da yayi, tun a hannun wanda suka sace su Widad ta jinjinawa jarumta irin ta Yusuf, tunda harta kai ga baya magana to tabbas ta tabbatar yana jin jiki ƙwarai.

Saleh yace "Ranki ya daÉ—e bari inje a duba motar ko, se a zo a tafi dashi"

Cikin isa da take nunawa ma'aikatanta tace "ina fatan kaga halin da yake ciki, dan haka bana buƙatar ɓata lokaci, duk inda abun hawa yake a nemo azo a kai shi Asibiti, kar ya sake galabaita"

Mamaki ne ya kama su, Yadda Widad take wa Saleh magana cikin isa da gadara, dukda irin taimakon da yayi musu, ga kuma tarin tazarar shekaru da ya bata, amma take masa wannan isar haka, se suka ga ta canza kamar ba Widad É—in dake magana sanyi sanyi ba.

Saleh ya ɗago ya ɗan ƙurawa Widad ido na wani ɗan lokaci.

Cikin tsawa tace "Kamar na gaya maka bana son ɓata lokaci, ka tsaya kana kallona, he's condition is getting worse, ko nawa za'a kashe ayi a nema masa lafiya" tai maganar tana wani sauke wahalallen numfashi.

Cikin harshen turanci Saleh yace "You are under my care now, why are you still shouting at me like this, so you are still rude up to now"

"My name remains Widad Nasir, Nothing will make me change, No matter what you did to help me, my policies remains constant, nothing has change"

Cikin rawar sanyi Yusuf ya shiga girgizawa Widad kai alamar tayi shiru.

Sudai mutan gida se binsu su kayi da ido.

Hanne ce taja wani uban tsaki tace "Aikin banza, ace mutum baya ganin girman kowa, se tsabar wulaƙanci da rashin ta ido"

Da sauri Saleh yace "Ke dawa kike? Idan kika kuma gangancin yin wannan mummunan furicin akanta duk abunda ya biyo baya ke kika siya, ko dan kin ganta zaune a gidanku, kin sam wace ita?"

Gwaggo tace "ayi haƙuri dai, naji tsayuwar Babur a waje, ina ga Ila ne ya dawo, maza jeka ku samo akori kura a kai shi Asibiti"

Haka akayi, Saleh yaje suka hau babur suka tafi nemo akori kura.

Sosai Fahad ya fara missing ɗin Ramlah, dan ba ƙaramin hutawa yake da ita ba, itama a ɓangarenta tana missing ɗinsa, amma tana so ta tabattar da idan dagaske yana sonta, kamar yadda Amal ta goranta mata.

Fahad ya É—au waya ya kira Ramlah, tana ganin kiransa babu ko jan aji ta É—auka da rawar jiki
"Hello Baby, shine kika watsar dani ko?"

"ba watsar da kai nayi ba, kaine ka watsar dani ka kasa Yimin abunda na tambayeka"

"Ramlah ki gane, baƙi nayi ba fa, kin san halin Daddy, ko zancen baya so na ɗakko masa, yaƙi saurarata sam gashi bani da lafiya se tunaninki nake, kuma nasan damuwa ce tamin yawa"

"dan Allah dagaske baka da lafiya? Ai ban sani ba, ohhh Sorry please i understand you, nasan kana son za kayi iya ƙoƙarin ka, bakomai hakanma nagode sosai my love"

Yayi ajiyar zuciya yace "Never mind baby, yanzu ya za'ayi ne? Inzo mu É—an fitane yau É—in?"

"Ni gaskiya a'a"

Ya ƙara marairaicewa yace "please na, ko so kike ace kizo ga gawata?"

"No bazata kaimu ga haka ba, kazo anjima mu fita, kasan bana son dsmuwarka my one"

"wow that's my only Ramlah, na ɗauka nikaɗai nake sonki na damu dake ai, shikenan dan Allah ki ƙure a daka, kiyi kwalliyar nan wadda ke narkamin zuciya"

"shikenan karka damu, sekazo"

Sukayi Sallama Fahad yace "akanme zanso a sako wani Anwar, yazo ya hanani rawar gaban hantsi, ai gara ayi ta tsare shi a can kowa ma ya huta.

Wasa2 labari ya karaÉ—e gari, an nemi Daula an rasa, abu kamar wasa kusan sati biyu amma babu ko wanda yaji É—uriyarsa, Alhaji Munir ne da Alhaji Haruna zaune a office, sunyi jugum jugum.

Alhaji Munir yace "Nifa gaba ɗaya abubuwan nan suna nema su kwaɓe, wai kamar almara har yanzu babu ɗuriyar Daula, babu ta wannan shegiyar 'yar tasa me baƙin taurin kai kamar ubanta, kuma gashi an ɗaga taron kasuwanci komai ya watse, nifa gaba ɗaya na fara karaya"

Alhaji Haruna yace "wace irin karaya kuma? Ai ba gudu ba ja da baya a wannan harkar, mun ɓata shekaru da dama akan wannan sabgar, kawai kuma semu sare yanzu, a'a baze yuwu ba, ni yanzu na fara tunanin anya ba wanine yake mana maƙarƙashiya ba?"

"Hmm bari kawai, ni kaina nayi tunanin hakan, an tuhumi doctor Sufyan har yanzu yace be san komai akan ɓatan Daula ba, ga ɗan gidan Hajiya Halima shima da yake kula da Daula, an tsare shi amma yace besan komai ba, wannan wane irin lamarine haka?"

Alhaji Haruna yace " Wani abun haushin ma, Halima se shiga take tana fita a sakar mata É—anta, tana neman ta tona mana Asiri "

Alhaji Munir yace " Ai duk wata sabga daza'a saka mata a ciki, to tabbas za'a sha takaici, tun farko nace kar a saka matar nan amma aka ƙi bin shawarata, gashi nan komai se kwaɓewa yake"

"Haba Munir, kai badan da temakonta ba ai da wata nasarar bamu sameta ba, ta bamu gudunmuwa sosai, sedai yanzu tana neman ta ɓata rawarta da tsalle"

Alhaji Munir yace "Kai ba wannan bama, kasan se siyar da manyan motocin Daula, tana ta holansuba ɓoye tana siyarwa, da wasu ƙananan kadarorinsa a ɓoye"

Zaro ido Alhaji Haruna yayi yace "bangane ba, kai waye ya gaya maka?"

"Al'amarin duniya baya ɓuya fa, nima labari naji kuma kana ganin mun fita wayo ne, kar take kallonmu matar nan mugun wayo ne da ita fa, tsohuwar  'yar duniya ce"

Shiru Alhaji Haruna yayi yace "Amma wannan ta cika muguwa, rabu da ita in tasan wata ai bata san wata ba, zamuyi magana da Musa, su tattauna da Bukar, muga yadda zamuyi maganinta"

Se wajen la' asar sannan Saleh suka zo da Mota, sedai akori kuran ta ɗanfi wadda aka kawo su ƙauyen a ciki, da ƙyar Yusuf ya miƙe Saleh ya riƙe shi, yana takawa a hankali.

Widad ta zuro Hijjabi tace binsu zata yi, Aikuwa Seleh yace "A'a base kinje ba, nida Ila da Megari za muje mu kai shi"

Ai nan da nan tasha gabansu ta tsaya ta kalli Seleh tace "wai kai a tunaninka har nayi yaddar da zaka É—auke shi ka tafi da shi, bayan ban san inda zaka kai shi ba, baze yuwu ba duk inda za'aje sedai aje dani"

Saleh yace "look, idan ina da nufin cutar daku, to da yanzu ba wannan zancen ake ba, ni bani da niyyar cutar ku, Asibiti zamu kai shi"

Megari yace "ki kwantar da hankalinki, Insha Allah babu abunda ze sameshi"

Kunyar Megari da Gwaggo ne yasa Widad fasa binsu, ta kalli Yusuf tace "Allah ya baka lafiya Yoseef, Allah ya kula da kai kamar yadda kake kula dani"

ÆŠagowa Yusuf yayi ya kalle ta, ya sakar mata murmushi suka yi waje.

Wajen ƙarfe Biyar na yamma, Anwar yazo gidansu Ramlah, ya kirata a waya ta fifo, har tazo falo suka haɗu da Amal, Amal ta kalli Ramlah tace "se ina?"

"zan fita ne" Ramlah ta bata amsa.

Amal ta jinjina kai tace "A dai dinga kula Ramlah, a dinga abunda ƙuda zebi, wannan gabtalin da kike ba yau ba gobe, ze ɓata miki suna ne"

"Ke dalla sauraramin, bana son shisshigi na gaya miki, ina ruwanki dsni ne? Kinfa fara isata na gaya miki"

Ta sa kai ta fice daga falon cike ɓacin rai.

Kai tsaye taje ta shige motar Fahad suka fita, Nura yace  "Allah wadaran wannan shegiyar Ramlah me kama da balbela"

Isa yace "bari, iskancin da take mana a gidan nan ko Gimbiyar Daula ba tayi shiba, kullum suna titi ita da wannan me kai kamar tumatir É—in"

Murtalah yace "Ai har gara ma Amal da Anwar, Amma da matar gidan nan da Ramlah Allah ya tsine musu Albarka"
Chapter 78 · 0% Book details