← Book details Akidata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 82

Sashe 62

Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mai gari na ganinsu tare yace "Masha Allah, Saleh fatan dai ba wata matsala ba suce, mun musu wani laifin bako?"

Saleh yace "Lafiya ƙalau babu wata matsala, munzo da wata 'yar magana ne"

Maigari yace "Masha Allah"

Saleh yace "Ina son in Allah ya kaimu jibi da rai da lafiya, ka ɗaurawa baƙinka Aure"

BuÉ—e baki Maigari yayi yace "dama ba matarsa bace?"

"Eh ba matarsa bace, ƙanwarsa ce hatsarin ya ritsa dasu tare kamar yadda nayi maka bayani, 'yar uwarsa ce amma da Aure a tsakanin su"

Maigari yace "Shikenan babu laifi, amma hakan baze kawo matsala ba idan suka koma gida?"

Saleh yace "kaikam Baffa ba dai tsoro ba,' yan uwane fa kuma ba lallai su koma gida nan kusa, se rigimar da'ake a garinsu ta lafa"

Maigari yace "Shikenan Allah ya kaimu, idan anyi sallar Juma'ar se' a É—aura"

Saleh yace "yawwa Baffa godiya muke, nima ina nan bazan tafi ba se Allah ya kaimu juma'ar idan an É—aura Auren"

Maigari yace "to madalla babu laifi"

Suka fito shida Yusuf, Yusuf yace "nikam me ka cewa Maigari ne a kanmu?"

Saleh yace "kasan mutumin ƙauye, kawai kifeshi nayi, nace masa faɗan ƙabilanci ake a garinku, kun samu kun tsira da ƙyara akan hanyarku ta guduwa kuma akayi garkuwa daku, har yanzu garinku babu lafiya"

Yusuf yayi murmushi yace "Allah sarki, yana da kirki da karamci kam,
Amma nifa bani da sadakin da zan bayar"

Saleh yace  "karka damu zan bayar, Allah yasa Auren ka yayi silar shiryuwarta daga wannan baƙin taurin kan da izzar, shegiya me kama da Aljanu"

Yusuf yace "dan Allah kadena zagin ta, bana jin daÉ—i idan ka zageta, É—azuma ka sata kuka"

Saleh ya yamutsa fuska yace "Yusuf ina zaton kana son yarinyar nan ne, in bahaka ba tun a baya su Nura dama sunce baka ganin laifinta, da'an mata abu sekaji haushi"

Yusuf yayi murmushi yace  "Saleh, duk ɗan adam tara yake be cika goma ba, duk rashin kirkinta akwai halayenta masu kyau, su kansu su Nuran yanzu zasu gane Amfaninta"

Saleh yace "eh amma rashin kirkinta yafi kirkinta yawa ai"

Yusuf yayi murmushi yace  "koma dai yane ni nasan tana da kirki ai, amma dagaske kaje gidanmu? Ya akayi kasan gidanmu?"

Saleh yayi murmushi yace" Yusuf kenan, har gurin aikinka nasani kai jami'in tsarone na farin kaya"

Gaban Yusuf ne ya faÉ—i "ya akayi kasan hakan?"

"saboda ina tare da maƙiyan Daula, binciken da'aka saka ma duk cikin shirinsu ne, ni naje na shirya komai, ba lallai kasan komai yanzu ba, amma anaso ka gama ka tattara bayanai akan binciken se akai sama, su kuma su karɓa su basu, duk cikin ƙoƙarin su na goge duk wata sheda da zesa asan sunawa Daula da 'yarsa zagon ƙasa, sedai basu san cewar kai aka saka kayi binciken ba, sudai kawai zaman jiran sakamakon bincikenka suke, basu san kaike binciken ba shi kanaa me gidanka Suleiman be san hakan ba, sedai akwai wani abokin aikinka da nayi connecting dashi, da zimmar idan ka gama binciken ya dinga bani wasu bayanai daga abunda kake binciken, sedai bazan gaya maka waye ba"

Shiru Yusuf yayi gaba É—aya kansa ya gama kullewa, kenan dama duk wannan wahalar da yake sha shirine, jiki a sanyaye yace "Widas tasan koni waye?"

Saleh yace "Yadda take shiri haka maƙiyanta sukeyi, sannan da ta san kai waye, wallahi da yanzu kana prison saboda bata yafewa wanda yayi mata ƙarya koya yaudare ta, kayi fatan Allah yasa ta fara sonka kafin lokacin da zata san ko waye, wataƙila ta sassauta maka"

Gaba É—aya Yusuf yayi shiru ya rasa abunda yake masa daÉ—i.

Saleh yace "zomu je mu ɗan zazzaga, kaga yanayin yadda ƙauyen yake"

Haka akayi Yusuf yabi Saleh, garin yana da kyau sedai ƙauyen ƙayau ne, babu ababen more rayuwa sam.

Ramlah tasha kwalliya cikin wasu ƙananan kaya, tayi kyau sosai, tana zaune a falo tana kaɗa ƙafa, aka kirata a waya, tana ganin me kiran ta miƙe tsaye, ta ɗau ƙaramin gyalenta ta yafa tace  "Mummy yazo bari inje"

Hajiya Halima tace "shikenan sekin dawo"

Amal tace "wallahi Ramlah baki da aji, daga zuwansa harkin miƙe kina rawar ƙafa zaki fita da nice da yanzu kina nan kinamin surutu, wani banza dashi gwalagwaji se shegiyar ƙarya da iyayi"

Ramlah a fusace  "Mummy kinga kiyiwa Amal magana ba ruwanta dani"

Mummy tace "Amal kar in ƙara jin bakinki a gurin nan"

Amal ta kwaɓe fuska tace "eh ai tuni na gane, kin fi son Ramlah akaina, damuwar ta ce kawai damuwa ni kuma baki damu dani ba, shikenan"

Ta miƙe fuuuu ta bar falon, Ramlah tayi waje abunta, a harabar gidan taga Fahad sanye da ƙananan kaya da tabarau yana tsaye a jikin motarsa, ta ƙarasa gurinsa tana wani yauƙi, tana ƙarasawa inda yake ya rungume ta, ba kunya ba tsoron Allah suka fara kissing ɗin juna a gaban ma'aikatan dake gurin, Fahad ya zame bakinsa a hankali yace
"you look so cute Baby"

Ramlah tace  "Really, you look good too baka ga yadda kayi kyau ba"

Ya riƙo ƙugunta yace "mu tafi ko"

"Ke Ramlah!" muryar Anwar ce cikin fushi yace "meye haka? Baki da hankali ne? Malama wuce ki koma gida"

Fahad yace "kamar ya ta koma gida, meyasa kake hakane Anwar"

A tsawace Anwar yace "zaki koma ko sena ɓaɓallaki a gurin nan, ballagaza kawai"

Da sauri Ramlah ta jiya da gudu cikin gida.

Anwar ya kalli Fahad yace  "Fahad kayi Asara wallahi, ita waccan da kake iƙrarin zaka aura baka samu ba, shine ka dawo zaka lallaɓa ka lalata ƙanwata, meyasa baka da imani Fahad, kana da 'yar uwa mace fa, baka tsoron ayimata abunda kake wa' ya'yan wasu, ya zakaji idan wani yayiwa Iman abunda kake yi "

Be rufe baki ba ya jiyo muryar Hajiya Halima tana masifa
" Anwar meye haka, yaushe ka zama haka? Ya zasu fita da yarinya zaka ce ba zata ba, tunda wannan shashashar ta ɓata ai ita ze Aura, me zesa ka kore ta haka akeyi? "

Anwar kamar zeyi kuka yace
" Mummy ke uwace, kamata yayi kisa ido sosai akan Yaran nan, yanzu ya dace Ramlah tabi saurayi da yammacin nan, kalli suturar dake jikinta fa"

"rufemin baki ko in gaggaura maka mari, ke wuce ku tafi"

Anwar yana kallo Ramlah ta shige motar Fahad, yayin da Fahad ke masa wani irin kallo na ya kaga lamarin.

Anwar dama Asibiti zashi gurin Alhaji Nasir, dan haka be sake cewa komai ba ya juya ya tafi.

Nura yace  "Bala'i ana shegiya a gidan Nasir Daula, duk iskanci shigar banza da izzar Gimbiyar Daula ban taɓa ganin ta aikata makamancin abunda wannan kwazgwamar tayi a gaban mu ba"

Isa me gadi yace "kaidai bari Nura, ai iskanci guri yake samu, kai da Yarinyar nan tana nan waya isa ya shigo gidan nan ya aikata wannan baÉ—alar, kuma wallahi kayan basu yiwa wannan shegiyar Ramlan kyau ba, wanka ai se Gimbiyar gidan nan, kaga kaya cas a jikinta kamar ita tayi kanta"

Nura yace  "kai dai bari Malam Isa, ni se yanzu nake ganin Amfaninta a gidan nan, duk wulaƙancinta idan tana nan se an bamu Abinci sau uku a rana munci mun ƙoshi a gidan nan, amma kalli yanzu sau ɗaya ma ba'a bamu"

Isa yace  "kai ba wannan ba, nifa ban gane kan wannan matar ba, kofa Asibiti basa zuwa, Anwar ɗin nan ne kawai yake zuwa yana kula dashi su kuwa ko a jikinsu"

Nufa yace "Hmm kai dai bar kowane munafuki inda ka ganshi, kallon mutan gidan nan kawai nake yi"

A kayan da Saleh ya kawowa su Yusuf, hadda kayan sawa ya kawowa Yusuf, dan Widad Akwatinan ta akawai kayan sawa, ya kawo musu man shafawa da sabulun wanka, dasu Omo, ya siyo musu sabon risho, da fitila sekuma kwalin batir, saboda garin ba Wuta.

Rana bata ƙarya sedai uwar ɗiya taji kunya, Ranar Juma'a bayan an idar da sallar juma'a aka ɗaura Auren Yusuf da Widad akan sadaki naira dubu goma sha biyar, shi kansa inda masallacin juma'ar nasu yake se anyi wata uwar tafiya daga nan inda su Yusuf suke kafin aje, ga shi duk ya lalace ya fatattake.

Nurat ce zaune a É—akinta da system akan cinyarta, a hankali ta zare earpiece É—in kunnenta tace "Alhamdilillah, done with this chapter"

Ta É—akko wayarta ta kira Anwar, tayi sa'a ya É—aga, ko gaisawa ba suyi ba tace "Alhamdilillah Yaya Anwar, na turo maka lamabar wani Bature, abokin cinikayyar baban Widad ne sosai, tare dashi za'ayi zaman taron kasuwancin, dan sune kusan wanda suke shirya taron kasuwancin, na san shi lokacin da nayi makaranta a England, muna zuwa gidansa tare da Widad, nayi masa bayani, Amma dukda haka nace zan bashi lambarka kuyi magana "

Jiki a sanyaye, tunda acikin damuwa yake yace " Madalla, Allah yasaka miki da Alkhairi Nurat, abokan kasuwancinsa da yakamata suyi wannan ƙoƙarin babu wanda yayi tunanin yin hakan, kowa harkar gabansa kawai yake, kamar ba wanda ya damu da halin da yake ciki"

Nurat tace "Hakane dama Yaya Anwar, kasan wani ya gayawa mahaifina naje duba Baban Widad, yanzu ya hanani fita kwata2"

Anwar yace "haba dai? Waye ya gaya masa?"

"Nima ban sani ba, amma insha Allah karka damu, zamu cigaba da communicating ta waya, ya jikin nasa kuwa?"

Anwar yace "to Alhamdilillah za'ace, yau dai naga jikin nasa ya tashi, dan se NG tube aka samasa tanan na bashi Abinci yau"

Nurat tace "Allah yasaka maka da alheri Yaya Anwar"

Anwar yace "Nurat kome nayiwa Alhaji Nasir Daula ai kaina nayiwa, karki damu Allah yayi mana jagora"

Ta amsa da Ameen.
Sukayi sallama tace "Alhamdilillah, saura kuma kuɓutar da Yusuf, Allah ka bani ikon kuɓutar dashi"  tunani ta shigayi, ta yaya zata san inda su Yusuf suke balle ta kuɓutar dasu?

Yusuf, da Saleh se megari da samarin 'ya' yansa suka shigo gidan, hannunsu É—auke da goro dabino da alawa, uwargidan megari wadda suke cewa gwaggo tace
"Malam ya dai na ganku da kayan É—aurin Aure haka? Bikinwa akeyi?"

Megari yace "baƙin 'ya' yanmu aka ɗaurawa Aure yau, ga naku kayan Ɗaurin Auren nan ayi musu addu'a"
Chapter 62 · 0% Book details