Sashe 19
Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan tafiyar su Widad Bulama na nan inda suka barshi yana zaune yayi shiru, Matarsa Hajiya Sarah ce ta fito da shirin ta tsaf, da alama fita zata yi.
Inda Alhaji Bulama ke zaune ta nufa, ta samu kujera ta zauna ta kalle shi taceÂ
"Ya dai? Wannan dogon tunanin fa? Shekaru sun fara ja, dogon tunani be kamace ka ba"
Ya sauke Ajiyar zuciya ya kalle ta yace "dole inyi dogon tunani, Yanzun nnan Widad ta bar gidan nan, lamarin yarinyar nan kullum ƙara taɓarɓarewa yake, wai ita ba zata yi Aure ba kwata2, haka zata ci gaba da zama, Rayuwa zata yuwu a haka? "
Ɗan taɓe baki tayi tace "waini Alhaji meye nasa damuwar 'yar wani a ranka? Naga dai ba kaine ubanta ba, taje tayi abunda taga dama mana"
"A' a Sara, Kin san yadda nake da Mahaifinta, damuwata tasa ce, damuwar sa ta wace, kuma har yanzu ana kainata hari, nace a samo mata masu tsaron lafiyar ta, taƙi se wannan yaron da take yawo da shi, kome ze tsare mata oho?"
"to ku ƙyaleta tayi abunda ta ga dama mana, tunda bata san abun Arziki ba, dama ba dole a cigaba da kai mata hari ba wannan Wulaƙanta mutane da take, Yarinya ƙarama se baƙar Aƙida"
"A'a be kamata a ƙyaleta ba Sarah, nifa mun yanke shawarar zamu haɗa ta Aure ne da Fahad"
Kallon sa tayi galala sannan taceÂ
"ban gane haÉ—a ta Aure da Fahad ba? Wannan Yarinyar mara tarbiyya da bata san Darajar mutane ba zaku haÉ—a da Fahad, ko manta Fahda É—in shima yadda yake da saurin Fushi da zuciya? Tabbas babu inda wannan Auden zeje, gara ma karka fara"
"Babu ruwan ki, Insha Allah zasu zauna lafiya"
Miƙewa tayi tsaye tace "Ai se ayi in gani, ni na haifi abuna ba wani ya haifar min ba, bame Aura masa Mahaukaciya mara tarbiyya"
Ta ɗau jakarta ta bar gurin tana ƙunƙuni.
Yusuf ne zaune ya zubawa sarautar Allah ido, Widad ce take zaga dabbobin gidan, wanda mafi Akasari karnuka ne da maguna se tsuntsaye, Abunda ya bashi mamaki shine yadda tasa aka fito mata da wani jibgegen ingarmar doki, aka ɗaura masa linzami, ta ajiye Wayarta ta da 'yar ƙaramar Jakarta, ba tare da an taimaka mata ba ta haye kan dokin nan.
Kasancewar harabar gidan ƙatuwa ce sosai, hakan yabawa Widad damar yin sukuwa akan dokin nan yadda take so, ba ƙaramin ɗaurewa Yusuf kai tayi ba, yadda take sukuwa akan dokin tana sarrafa akalar sa yadda take so, ze tabattar maka ta saba hawan dokin, kuma ga dukkan Alamu hakan yana bata Nishaɗi.
Seda tayi me isar ta sannan taci birki ta sauka daga kan dokin, ta shiga cikin gidan.
Yusuf yana nan zaune ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan wanda Aƙalla ze shakara talatin da wani abun ya ƙaraso inda Yusuf yake zaune shima ya zauna kusa dashi.
Ya miƙawa Yusuf hannu suka gaisa, ya kalli Yusuf yace
"É—an Samari daga wani gari kake ne?"
Yusuf ya ɗan ƙura masa ido Sannan yace "Kano"
Mutumin Yayi Murmushi yace "Ashema ɗan garin nan ne kai, a wace unguwa kake?"
Yusuf yace "Me yasa kake tambaya ta ne?"
"Ahh karka damu kawai dai na tambaya ne, Amma idan ba zaka damu ba, dan Allah wani irin aiki kakewa Madam haka da take yawo da kai ko ina? A iya sanina da ita tun shekarun baya bata sake wa da mutane haka, Amma kai gashi tana yawo da kai ko ina"
Yusuf yayi Murmushi yace
"Ita yakamata ta baka wannan Amsar bani ba"
Suna cikin maganar ne Widad ta fito sanye da wasu kayan daban.
Ƙure Yusuf da Saleh tayi ido, tana musu kallo irin na tuhuma, ba tace komai ba ta nufi inda Motar su take, Ma'aikatan gidan suka biyo ta suna mata kirari suna Allah ya kiyaye, bata kula kowa a cikin su ba ta hau motar Yusuf ya ja suka bar gidan.
Suna cikin tafiya yaji taceÂ
"Me Sale yace maka?"
"Waye Sale?" Yusuf ya tambaye ta, shiru tayi masa tsawon wasu daÆ™iÆ™u sannan cikin maganar ta ta isa, taceÂ
"Kana jin daɗin rainamin hankali a lokuta da yawa, na kan ƙyaleka ne saboda ina jin nauyin hukunta ka a lokuta da yawa, saboda hatsarin da rayuwar ka ke ciki Kasancewar ka tare dani, Amma hakan baze hanani koya maka hankali idan ka saɓawa Yarjejeniyar mu ba, na tambaye ka ɗazu da Safe baka bani haƙiƙanin Amsar tambaya ta ba, ka rainamin hankali, yanzu ma na tambaye ka kana sake tambaya ta, wannan abubuwan da kake kana jawowa kanka zargi ne a gurina, karo na biyu Me Sale yace maka? "
Murmushi Yusuf yayi yace
"Ya tambaye ni Sunana ne, da kuma aikin danake miki, na gaya masa sunana, Amma aikin da nake miki nace ya tambaye ki"
Jinjina kai tayi tace "Amma kamar na gaya maka duk inda muka je, ba zakayi magana da kowa ba se idan ni nayi maka izinin yin hakan"
Juyowa yayi ya kalli Widad, Yarinya ƙarama se izza da jin kai.
Yusuf ya É—an rausayar da kai yace
"Allah ya baki yawan rai ya kare ki daga sharrin maƙiyanki, banyi hakan da saɓa dokarki ba, sedai idan nayi hakan mutane zasu ga tamkar wulaƙanci ne, nasan tsoron ki kar a haɗa kai dani a cutar dake, Amma ina tabbatar miki da cewa bazaki taɓa samuna da cin amanar ki ba"
Ba tare da ta kalle shi ba tace
"Zan gani ai"
Sunyi shiru na wani lokaci, can ta jinjina kai taceÂ
"Lallai Sale, kar nake kallon sa, yana son ganin bayana saboda abunda nayiwa ɗan uwan sa, duk randa na kama shi red handed wallahi se yaje inda ɗan uwansa yaje, babu Amfani zama da maƙaryaci me cin Amana"
Yusuf ya juya yana kallon ta, yana tunanin randa ta gano waye shi, wane irin mataki zata É—auka akan sa?
****************************
A kwana a tashi Yusuf yayi wata guda cif yanawa Widad aiki, kullum cikin hantarar sa take da wulaƙanci amma sam seya nuna mata ko a jikin sa, duk abunda yayi baze burgeta ba, yayin da Amal keta ƙara tura kai a gurin Yusuf, dan ita nan duniya babu wanda yayi mata kamar shi tana matuƙar ƙaunar Yusuf saboda nutsuwar sa, Yusuf yana ta ganin Abubuwa na ban mamaki a game da uwar ɗakin sa yayin da gefe guda ya kasa gane bakin zare al'amuran gidan nan, gaba ɗaya yanayin yadda mutanen gidan ke gudanar da mu'amalarsa da ban mamaki dan kowa da inda yasa gaba kuma kowa akwai wani boyayyen abu da yake ɓoyewa a ransa.
Har wata ya cika, aka shiga wani watan Widad bata biya Yusuf haƙƙin sa ba, shi kuma bece mata komai ba, sannan duk lokacin da ta buƙaci zuwa wani guri, zeje ya kaita ba tare da ɓata lokaci ba.
Isa me gadi yana ta ƙoƙarin bugun cikin Yusuf yaji wani abu game da shi amma Yusuf yaƙi gaya masa komai.
Gaba É—aya ma'aikatan gidan suka tsangwami Yusuf suna ganin ana fifita shi akan su.
Shikam ko a jikin sa, shima ya dena shiga harkar su, har gara Murtalah me kuka da shuke shuken gidan suna hira da Yusuf wasu lokutan.
Hajiya Halima na zaune a falo tana aiki a System, gefen ta kuma Amal ce ke cin Abinci, mai aiki ta fito daga sashin Widad, ta durƙusa a gaban Mummy tace
"Hajiya, Anty Widad fa tun jiya ɗakin ta a rufe, na ƙwanƙwasa taƙi buɗewa, tun jiya da safe naje in gyara mata amma ɗakin a rufe"
Tsaki Hajiya Halima tayi tace "To ina ruwana, yarinya ce ita ƙarama da zan dinga binta, in taji yunwa zata kashe ta ta fito"
Amal tace "Mummy kina tunanin Yunwa zata saka ta fito ne? In baki wasa ba sedai kiga gawar ta kin san halin ta, idan ta mutu da wani kalamai zaki ƙwaci kanki a gurin me gidan nan? Bama ke kaɗai ba dukkan mu, sannan Burinmu baze cika ba, ƙarshe ma dukkanmu sedai mu mutu a prison"
Ɗan zaro ido Mummy tayi tace "Kuma fa hakane, tashi muje mu gani"
Suka nufi part ɗin Widad, Amma suka tarar ta rufe bedroom ɗinta, suka yi bugun duniya taƙi ta buɗe.
Rasa abunyi suka yi, suka kira Alhaji Bulama suka sanar masa da abunda ke faruwa, da kiran wayar tasa beyi mintuna Arba'in ba se gashi.
Yaje ya tarar dasu sunyi cirko cirko a ƙofar ɗakin Widad, ya taka yaje gaban ƙofar ya fara ƙwanƙwasawa
"Lovely daughter, Dad ɗinki ne, ki buɗe ƙofa kinji, karkiwa kanki illa"
Still Widad ba tayi responding ba, dan ko motsin ta basaji.
Alhaji Bulama yaceÂ
"Kuma babu wani abu daya haɗaku da ita? Kowani saɓani ko ayi mata wani abun?"
Ramlah tace "waze nata wani abu kuwa? Ita wannan se an mata wani abu? Ai sedai tayi wa wanima,wataƙila haukan nata ne ya motsa"
Alhaji Bulama yace "ku bani mukullin É—akin ta, a buÉ—e É—akin karta"
Mummy tace "taɓ wake da mukullin ɗakin basarakiya, ita da bata yadda da kowa ba, wa zata bari ya mallaki mukullin ɗakin ta ba wanda yake da mukullin ta"
Alhaji Bulama yace "to ko maza za'a kirawo su ɓalla ƙofar a gani"
Ramlah tace "A'a karka jamana Jaraba, a ɓalla mata ƙofa ka samu a tashin hankali da masifarta, a kira Baban ta aji meze ce"
Alhaji Bulama yace "Keba babanki bane Ramlah"?
Cikin tsiwa Ramlah tace "Niba baba na bane, kullum bata da gori seba gidan ubanmu bane, dan haka ubanta ita ya haifa bani ba"
Yau Yusuf ya makara dan se sha ɗaya ya tashi na safe, tunda ya koma bacci ƙarfe takwas na safe, dan haka a gurguje ya kintsa ya fito, yayi sa'a Umma bata nan ta fita, dan haka ya kulle gidan ya fita, ya nufi gidan su Widad.
Yana zuwa suka gaisa dasu Nura sama sama,suna masa wani kallon banza
Yusuf ya kalli Murtalah yace "Murtalah Madam ta fito kuwa? Ko tazo nema na naga yau na makara sosai"
Murtalah yace "ina fa, tana can tun jiya taƙi buɗe ƙofa, ana can anata fama da ita, ba wanda yasan tana raye kota mutu, gashi babu wanda yake da mukullin ƙofar ta, ana tunanin ko ɓalla ƙofar za'ayi