Sashe 23
Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yusuf yayi Murmushi yace "Inajin daɗin wannan aikin a hakan, bana so kiyi wani abu da ze ɓata ran mahaifiyar ki, Amma ina godiya da karamcinki a kowane lokaci, tunda kin gama, muje in sauke ki a gida nima in tafi, kafin Madam ta farga tare muka fita dake" yai maganar cike da ƙoƙarin basar da maganganun Amal
Amal ta jinjina kai ta miƙe, suka bar gurin.
***************************
"Bayanai sun sameni cewar, Akwai yuwuwar Bala ya tona mana Asiri, yayi iƙrarin cewa tunda aka kaishi prison babu wani ƙoƙari da muke dan fitar dashi, munawa kabmu ƙoƙarine kawai, dan haka na yanke shawarar in kiraka muyi wata magana, fatan zaka buɗe kunnenka ka saurereni"
"To Yallaɓai, ina saurarenka"
"Hashim, Abunda nake so da kai shine, So nake a zuba magani a Abincin daza'a bawa Bala, wanda ze sashi rashin lafiya, daga nan se a kaishi Asibitin doctor Mukhtar, a can nake so a ƙarasamin shi, a kauda shi daga duniyar gaba ɗaya dan baze ɓata mana shiri ba"
Hashim Yace "Amma Yallaɓai aikin nan fa yana da hatsari sosai, kasada ne me girma, idan aka gano da hannuna a ciki zan rasa aikina, kuma za'a kamani"
A hasle mutumin yace "Kowace irin kasada ce gara ayita matuƙar Sunana baze fito ba, bazan zuba ido suna na ya ɓaci a banza ba ba tare da na cimma burina ba, Amfanin Bala ya ƙare dan haka a kauda shi bashi da sauran amfani a gareni, kana da damar yin hakan, kana da dama a hannunka dan haka kayi yadda nace, tun kafin raina ya ɓaci"
Hashim yace "Amma Yallaɓai......
"Sadakin aikinka naira million biyu ne, idan ba zaka iya ba zan saka a gefe in saka wani yayi min, Amma kasani kaima bazan barka a doron ƙasa ba tunda kasan sirrina, tashi ka fita na gama magana da kai "
**********************
Widad ta koma normal kamar ba ita ba, dan haka Daddy ya fara shirin komawa saboda Ayyukan da yake dasu, sedai sun fafata da Widad sosai dan ya sake yi mata batun Aure, ita kuma ta ƙara tabbatar masa tana nan akan bakarta ba gudu ba ja da baya, hakan yasa suka ɗan samu saɓani, ya tafi ba tare da tayi masa rakiya ba.
Yusuf yaje ya tsananta bincike akan gano waye mahaifin Nurat, wadda suka je gurin birthday ɗinta shi da Widad, ya samu bayanin wasu abubuwan ne daga gurin Amal, wadda ta riga ta gama narkewa a ƙaunar Yusuf.
Mahaifin Nurat babban ɗan siyasa ne, sukan haɗu da mahaifin Widad a gurin kasuwanci, amma bayanai sun nuna akwai tsohuwar Alaƙa dake tsakaninsu wadda daga baya tayi rauni, 'yarsa da Widad sun haɗu a gurin karatu ne a ƙasar waje, ita kaɗaice ƙawar Widad a Nigeria, se
'ya'yan Alhaji Bulama, shima ba wata alaƙace ta kusa tsakanin su ba, dan bata yarda a raɓeta, ba kowa ke iya jure halinta ba.
Tsangwama ta yau daban ta gobe daban, haka Hajiya Halima, Ramla da ma'aikatan gidan suke nunawa Yusuf, shi kuma ko a jikin sa, aikin da yaje yi shi kawai yake.
Isa mai gadi yayi yayi yasan daga ina Yusuf yake zuwa, Amma fafur Yusuf yaƙi gayamasa, daga baya ma se ya janye jikin sa, bayan gaisawa babu abunda ke shiga tsakankanin su.
Wasa2 aka shiga wata na uku, Amma Widad bata biya Yusuf haƙƙinsa ba, shi kuma koda wasa be taɓa magana ba.
Yusuf yana zaune a harabar gidan yana danna wayar sa, daga sama yaji ance "Ssss" ɗaga kai yayi ya hango Widad ta saman bene, tayi masa alama da hannun ta yaje.
Yusuf ya miƙe ya shiga, tana zaune a falo tana cin gugguru, tana ci tana bawa magenta, Su Hajiya Halima na falon ita da su Ramla gaba ɗaya.
Yana shigowa Amal ta kalle shi tana kashe masa ido, seda yakusa faɗuwa dan gani yake gaba ɗaya sunga abunda Amal tayi, Widad dake kaɗa ƙafa tana kallon Abunda Amal tayi, bata tanka ba ta cigaba da watsa popcorn ɗinta.
Gefen kujerar da Widad ke zaune yaje ya zauna a Æ™asan carfet yaceÂ
"Gani ranki ya daÉ—e"
Ta kalle shi ta yamutse taceÂ
"Kai nifa bana son all such kind of names, Malam sunana Widad, ka dinga kirana da sunana"
Murmushi yayi mata tare da ɗan girgiza kai yace "Bazan iya ba, nafi jin daɗin ince Madam, ko ranki ya daɗe"
"to bana so, niba basarakiya bace, ka kira ni da sunana kawai"
"Aike kinfi basarakiya ma gimbiyar Daddynta"
Wani É—an guntun Murmushi tayi, wanda ita kaÉ—ai tasan ma'anar sa.
Wani uban tsaki Amal tayi wanda bata san ya fito ba, ta miƙe a fusace da nufin ta bar falon saboda haushi.
"Amal!" Widad ta kira sunan ta. cak ta tsaya ba tare da ta waigo ba.
"Me nayi miki ne?" Widad ta jefa mata tambayar
Fuska a cunkushe Amal tace "bakomai"
Murmushi Widad tayi wanda ya ƙara fito da kyawunta, tana girgiza santala santalan ƙafafuwanta, sannan tace
"Kin san Widad bata Soyayya, balle ince zan so abunda kike so, shi kansa Son ban yadda dashi ba balle inyi shi, koda zanyi so bazan so maƙasƙancin Mutum kamar direba na ba, balle inyi wani abu da zesa kiji haushi saboda shi, ki kwantar da hankalinki ba abunda zanyi da wannan abun, rainin hankalinsa da ƙwarin gwiwarsa gurin karyamin dokoki ne ke burgeni wasu lokutan, ban taɓa ma'aikacin da yake rainamin hankali da son yimin katsaladan a cikin lamaurana yadda yakeso kamarsa ba, wani abu dana fuskanta shine, ze iya jure duk wani hali da AƘIDATA, hmm ki huta beb ba wani abun damuwa a cikin abunda nake" ta ƙarasa maganar tare da wani murmushi na rainin hankali.
Yusuf ya kalli Widad, yaji haushin maganganun ta, ya ƙudurce wani abu a ransa.
Ta kalli Yusuf cike da kashedi tace "Kaikuma tara ka kawai nake, ina sane da duk abunda kake yi, ina gargaɗinka akan contract ɗin daka sawa hannu, Ni kaɗai na ɗaukeka aiki, ni kaɗai zakayiwa Aiki, idan har zakayi soyayya or what ever Rubbish you call it, kayishi bayan ka bar gidan nan, hope I made my self clear "
Yusuf ya jinjina kai, a fusace Mummy tace "Aikuwa se naci uban Amal akan yaron nan, ka kiyayi 'yata ba kai ba ita, banda tsiyar ɗan talaka ina kai ina Amal, ƙwarya tabi ƙwarya mana, wallahi duk lokacin da ka kuma shiga sabgarta sena saɓa maka"
"Cewa akayi ana sonsa bashi yace yana so ba, ko ba kya gani ne? Kina zaƙewa gurin ci masa mutunci wasu lokutan, na lura Daddy yana matuƙar ji dashi saboda biyayyarsa, yana girmama shi sosai, ko dan haka at least dole a ɗagamasa ƙafa saboda yana matsayi me girma a gurin megida, dan haka a dinga ɗaga masa ƙafa a dena son shiga hurumin dabe dace ba"
Ta kalli Yusuf tace "Aiken ka zanyi, kaje ɗakina, ka ɗauki key a drower mudubi, ka buɗe wardrobe ɗina ta ƙarshe, ka ɗakko ATM ɗina kazo"
Ba Hajiya Halima ba har Ramla da Yusuf seda suka kalle ta da sauri.
Ta basar ta maida hankali kan talabijin, kamar ba ita tayi magana ba, jiki a sanyaye Yusuf ya miƙe ya nufi ɗakin ta, gaban sa se faɗuwa yake, inda ta kwatanta masa yaje ya ɗau key ɗin ya buɗe wardrobe ɗin da tace.
Ramla ta kalli Widad tace "Amma Widad kamar be kamata kitura ƙato kamar wannan ɗakinki ba"
Widad bata kalle ta ba taceÂ
"gayamin abunda ya kamata Uwata"
Ramla taja bakin ta ta tsuke, dan tasan idan taja maganar se ranta ya ɓaci.
"Subhanallah" shine abunda Yusuf ya furta, dan bayan sutura dake cikin wardrobe ɗin Widad, hadda bandir bandir na kuɗi na Nigeria dana ƙasashen ƙetare.
A gagguce ya ɗau abunda ze ɗauka ya fita ya kai mata, maimakon ta karɓa se ce masa tayi "Kaje na baka hutu na sati ɗaya dan ba inda zanje a kwanan nan, ina so kaje da ATM card ɗin nan, ka cire kuɗi, ka siyomin latest trending phone me kyau guda biyu"
Yusuf yace "Yanzu zan siyo in kawo miki?"
Ƙura masa ido tayi ba tace komai ba, kallon gargaɗi take masa akan bata son rainin hankali, dan haja Yusuf ya girgiza kai ze fita, Widad tace "Ji mana" ya tsaya tare da waigowa ya kalle ta
"Yanzu idan na tambaye ka kasan inda rai yake, wace amsa zaka bani?"
Æoye mamakin tambayar da tayi masa yayi yace "Allah Mahalicci shikaÉ—ai yasan wannan Amsar"
Ta jinjina kai tace "Good you can go"
Hajiya Halima a gigice taceÂ
"Widad baki da hankali ne? Ya zaki bawa baƙo wanda baki san daga inda yake ba ki ɗau ATM wanda Account ɗin cike yake da kuɗi, Yallaɓai ma yana zuba dukiyar sa a ciki, kodan baki san zafin dukiyar ba sama taka aka tara aka baki, yanzu idan ya gudu yaƙi dawowa fa?"
"Kalma ta farko kin faɗi abunda ya dace a kaina, kin faɗa daidai ba kuskure, bani da hankali ni mahaukaciya ce kamar yadda kuka saba faɗa, dukiya kuma ta ubana ce, idan na salwantar da ita ba abunda zece tunda nima akwai tawa a ciki, ki dena tada jijiyar wuya akan dukiyar daba taki ba, idan tunanin ki abunda zaki samu bayan me ita ya mutu, sena tabattar da na ƙarar da komai kafin ya mutu koni na mutu, shine hanyar da zan baƙantawa masu harin dukiyar nan rai, and Mark you idan wani abu ya samu dukiya ta a yanzu to ba shakka kece, saboda babu wanda yasan da ATM ɗina a hannun sa seke da iyalanki"
Widad ta miƙe ta barmusu falon suna kallon kallo.
***********************
"Mummy, me yasa Daddy yayi yunƙurin sawa a sace Widad ne? Am so much Confused fa, tunda akayi abun nan ta bar gidan nan bata ƙara kirana a waya ba"
Mahaifiyar Nurat tayi ajiyar zuciya tace "Nurat nima ban sani ba gaskiya, ni banda yanzu da kika gayamin ma ban san abunda yake shiryawa ba, yanzu ina magana ze iya É—aukar mummunan mataki a kaina, kin san halin sa"
"Amma Mummy abun ya É—auremin kai, kinji yadda ya dingamin masifa dan na bari an É—auke ta, kuma fa wani ne yayi barazanar ze saceni nima in har ban gaya masa inda take ba"