← Book details Akidata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 82

Sashe 26

Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kai É—an Yimin shiru mana, idan ban manta ba kafin in É—auke ka aiki na gaya maka salary É—inka, kasan sunyi yawa meyasa kace zaka yi aikin? A beg keep this aside follow me"
Tayi maganar tana miƙewa tsaye ta nufi bedroom ɗin ta, jiki ba ƙwari Yusuf yabi bayan ta.

Wardrobe ɗinta ta buɗe ta ɗakko wayar nan da tasa ya siyo, ta tako zuwa gaban Yusuf, sedai tana zuwa suka ji wani shock a tare, ƙamshin turaren da Yusuf yake yasha banban da wanda ta hana shi sakawa, amma muddin zata ji ƙamshi a jikin sa se wata kasala ta saukar mata.

Shikam Yusuf ƙirjin sa ne ya shiga bugawa da ƙarfi ba tare da yasan dalilin hakan ba.

Widad ta tattaro nutsuwar ta ta dube shi ta miƙa masa wayar, yasa hannu ya karɓa yana kallon ta, a hankali tace

"Yanzu misali a ce wannan wayar ranka ce, a ina zaka ɓoye ta?"

Yusuf yayi ajiyar zuciya yace "zan mata kyakkyawan ɓoyewar da babu wanda ze san inda take se Allah"

"Good haka nake son ka ɓoye wannan wayar tamkar na baka ranka, duk kusancinka da mutum karka kuskura yasan da wannan wayar a tare da kai, karka yarda da kowa, wannan wayar tamkar na baka ranka ne!!! ka kula da ita"

A diririce Yusuf yace "Amma me yasa zan kula da ita haka? Ban gane tamkar kin bani raina ba"

Ɗan taɓe baki tayi ta juya tace "bashi da mahimmanci kaji wannan a yanzu, saboda sanin hakan a yanzu tamkar sake jefa rayuwar ka cikin hatsari ne, let me tell you something, don't trust anyone, i repeat myself don't trust anyone, jeka ƙarfe biyar zan fita yau"

Yusuf ya jinjina kai yace  "Amma kuɗin nan da kika bani wallahi sunyi yawa"

Widad tace  "You can go, na sallame ka"

Yusuf yace  "Amma ban san yadda zanyi da wannan maƙudan kuɗin ba"

Ba tare da ta kula Yusuf ba ta shiga ƙoƙarin rage kayan jikin ta zata shiga wanka, ba shiri Yusuf ya juya da sauri ya bar ɗakin, yana mamakin wauta irin ta Widad.

*********************************

Alhaji Musa ne zaune a falon sa, 'yarsa Nurat na kujerar dake facing É—insa ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunata.

"Wallahi Nurat na rasa me zan miki in huce, da tuni harkar nan ta kankama, amma kikayi mana wauta da hauka, idan abun da muke nema ya samu, se kinfini mora"

Murya na rawa da alama tana tsoron mahaifin nata tace 

"dan Allah kayi haƙuri, nima wani ne yace ze saceni idan ban nuna masa inda take ba"

"waye shi É—in?" ya tambaye ta a É—an hasale

"Wallahi ban san waye ba, nima bata gayamin waye shi ba"

"Ni zan gano ko waye inyi maganin sa, yanzu dole ki samo wata hanyar abunda zaki yi ta sake zuwa gidan nan"

Saurin girgiza kai tayi tace  "Ai kasan ba zata ƙara yadda dani ba, wallahi kome zanyi ba zata zo ba"

A fusace yace  "tashi ki bar nan, komai a kasa dake se kinyi wauta, ni nasan abunda zanyi"

****************************

Album guda na hotunan Widad yake dasu a System ɗinsa, ji yake kamar ya janyo kwanakin da ze koma Nigeria, kallon hotunan ta kawai yake hakan ke ƙara samasa nishaɗi.

Video call ya kira Mummy, Hajiya Halima na ganinsa tayi murmushi tace 
"'yan makaranta, lokaci ya kusa ko?"

Anwar yace  "Eh Mummy se missing ɗinku nake, ina su Ramla ne"

"Suna nan gasu a kusa dani"

"shine ba zasuzo mu gaisa ba, dama ba nemana suke ba"

Amal tace  "waze kira ka a kwashe masa kuɗi"
Haka suka dinga video call suna hira da 'yan uwan sa, can yace  "Mummy wai ina Widad ne? Naji ance tana Nigeria kuma tunda nake kira bana ganin ta"

Tsaki Mummy tayi tace  "Ban sani ba, ita ta haifeka koni? Idan bani kske nema ba shikenan, kullum baka da zance sena wanne banzar yarinyar?"

"yi haƙuri Mumsy, Yadda mahaifinta ya riƙemu ai senake ganin kamar babu laifi dan na tambayi inda take"

Ramla tace "Brother dan Allah karka ɓatawa mutane rai, waya ke maganar wannan mahaukaciyar"

Anwar yace "ni a ganina, Widad rashin me janta a jiki da kuma depression yasa condition É—inta ya zama complicated, amma...

Cikin tsawa Hajiya Halima tace " Rufemin baki dan uban ka, kaga ka kiyaye ni ko in ɓata maka rai, in baka son ɓacin raina karka sake Yimin zancen yarinyar nan, ko dan kai kana can baka san irin zaman da muke a gidan nan ba"

Ramla tace "ina ze sani, muna nan ta mayar damu kamar bayi, cin kashi kala kala, ana Wulaƙanta mu muda mahaifiyar mu amma kana neman ta"

Anwar yace  "Amma Mummy....

A fusace tace "ke Amal katse min kiran nan, shashashan banza kawai"

Amal ta katse kiran.

Anwar ya turawa Amal message
"Amal É—an turomin lambar Widad"

Ta masa reply da  "Taɓɗijan wa kake tunanin ze samu lambar wannan? Duk yadda kake tunanin abun ya wuce haka, ba ruwan ta damu fa"

Jujjuya message É—in ya dinga yi, babban abunda yake bashi takaici be wuce duk lokacin da ya kira Mummy, ya tambayi ina Widad seta balbaleshi da masifa, duk wanda ya tambaya ya bashi lambar ta kowa se yace bashi da ita, ya rasa meye dalilin hakan.

Yana wannan tunanin Fahad ya shigo ɗakin da sallama, ya kalli Anwar yace  "Man what's wrong ne? Nayi sallama baka amsa ba"

Ɗan guntun tsaki Anwar yayi yace  "Fahad, ni gaba ɗaya na kasa gane kan lamuran nan dake faruwa, duk lokacin da zamuyi waya da Mummy, idan har zan tambayi Widad se taita faɗa, babban abunda yake bani mamaki shine, wai ace duk gidanmu babu me lambar Widad balle ya bani"
Fahad yace
"Widad Widad Widad, kai dai baka da zance se wannan Yarinyar, please don't kill yourself mana, Nifa yadda kake bani labarin ta sam bata Yimin ba, nifa tun tana ƙarama yadda take wannan Share mutanen haushi take bani, kuma gashi da bakin ka ka gayamin tana da taɓun hankali "

Anwar yace " shut up please, tunda ba zaka bani shawara ba ka ƙyaleni, baka san yadda nake ji akan ta ba, kai kana soyayya amma kamar baka san meye son ba, Ni anya ma in baka Ramla zaka iya riƙe ta kuwa? "

Fahad yayi murmushi yace
"Anwar kenan, aini Soyayya ta da Ramla tana sona ina sonta, amma kai banda wahala babu abunda kake yi"

"Kai kaga wahala, ni bangan ta ba, Ni na ƙagu kamar in janyo lokaci in koma gida, gashi seka rigani komawa Nigeria"

"Allah ya baka lafiya Anwar, dan ga dukkanin alamu ta shafa maka haukan"

Shiru Anwar yayi ya miƙe ya bar ɗakin, dan Fahad ya fara baƙanta masa rai.

Widad tana ta shirin fita, wayarta ta fara ringing, hannu tasa ta ɗau wayar tasa a kunnen ta, shiru ta ɗanyi tace 
"Ok, thank you very much, send the address via my email" ta ajiye wayar tana ci gaba da shiryawa.

Maimakon ta fito seta tsaya ta saman bene tana duba lokaci, Yusuf ta hango ya fito da Mota yana ta gogewa dukda a wanke take, abun da ta fuskanta da Yusuf mutum ne meson tsafta sosai, baya son datti sam.

Message ne ya shigo wayar Yusuf ya É—aga ya duba.

"Ba'a wannan motar zamu fita ba, ka fita waje ka jirani"

Mamaki ne ya kama Yusuf, tabbas Wannan message É—in daga Widad ne, 'Amma yaushe ta samu lamba ta?' ya tambayi kansa, basarwa yayi ya mayar da motar, yana fita wajen gate yaga wata mota, ba dai me tsada bace dan kamar ma ta É—anji jiki.
Guri ya samu ya tsaya yana jiran fitowar ta.

Seda yayi kusan mintuna talatin kamar ance ya ɗaga kai ya kalli gate, ganin Widad ne yasa ƙirjin Yusuf bugawa da ƙarfi.

Wani arnen black leg jeans ne a jikin ta, da wata tied pitted blue body hook, tayi stocking ta saka beilt, ɗan ƙaramin baƙin veil ta ɗaure gashin kanta, dukda ƙasan gashin nata ya fito.
Google glass ne a fuskar ta baƙi, ga takalmi me matuƙar tsini, se 'yar ƙaramar jakarta, gaba ɗaya bazaka ce idan Widad ta buɗe baki zata yi hausa ba, duk wani shape da surar jikin ta ya fito.

Tabbas da Yusuf nada damar Mayar da Widad ta canza kaya da tabbas zeyi, dan haka kurum yaji takaicin fitar Widad a haka.

Ƙarasowa tayi ta miƙawa Yusuf key ba tare da tace komai ba, jiji a sanyaye ya karɓa, ya buɗe mata motar ta shiga ya rufe ya zaga mazaunin direba ya zauna, gaba ɗaya ƙamshin turaren da take ya cika motar, ya kalle ta yace
"Ina zamu je?" shiru tayi na ɗan wani lokaci sannan ta miƙa masa wayarta, yasa hannu ya karɓa ya duba.
Adress ɗin inda ze kaita ne, ya ɗago ya kalleta zeyi magana, amma yaga ta ƙara yi masa kwarjini, dan haka ya bata wayar ta ya kunna motar.

Yana cikin tuƙi wayarsa ta fara ringing, Umman Yusuf ne a jikin screen ɗin wayar, ya ɗaga wayar yasa a hansfree ya ajiye ta yace
"Umman Yusuf"

"ÆŠan gidan Umman sa, yau zaka dawo da wuri ne, an kawomin wani kifi tun daga Yobe, nayi maka farfesu ka dawo da wuri karya huce, ko kuma in cinye abuna"

Duk da ransa a dagule yake wanda ya rasa dalilin hakan, Amma seda ya maze yace 
"Umman Yusuf, ai bazaki iya ci baki ajiye min ba, zan siyo gurasa yai akwai dinner me kyau"

Hirarsa yake yi da maman sa hankali kwance, se shagwaɓa yake yi kamar yaro ƙarami, Widad kuwa ƙura masa ido tayi ko ƙiftawa ba tayi, dukda ta cikin Glas ɗin idonta take kallon sa amma yadda yake wayar da Mahaifiyar sa ba ƙaramin birge ta yayi ba.
Chapter 26 · 0% Book details