← Book details Akidata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 82

Sashe 31

Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta gyara kwanciyar ta sosai ta miƙe ƙafafunta akan doguwar kujerar tare da lumshe idonta, don bawa hawayen idon nata damar gangarowa.

Yusuf a ransa yace 'Ikon Allah, wannan wane irin kuka ne?'

"ko za'a kira likita ne?"

"Ni lafiya ta ƙalau" ta bashi amsa idonta a rufe.

"Jikinki yana rawafa, kamar zazzaɓi ze kamaki fa"

"to ina ruwan ka? Jikin ka ne ko nawa? Ni kaimin kayana É—aki ka tafi ka ban guri"

ÆŠan girgiza kai Yusuf yayi yaje ya ajiye mata kayan ta ya fito, tana nan inda ya barta, yasa kai ya fice.

Yana fitowa ƙofar da zata sa dashi da harabar gidan yaji an riƙo rigarsa, waigawa yayi yaga waye wannan.
Amal ce tsaye tana huci,
"Amal lafiya kuwa?"
"dole kace lafiya mana? Yusuf daga ina kake kai da Widad?, saboda tsabar abu harda cire mata takalmi, Yusuf wai kai wani irin mutum ne dan Allah? Me kake aikatawa ne haka Yusuf? me yasa lallai seka yi abunda zaka birgeta, bayan kullum baka da kima a idon ta? Sau nawa nake gaya maka kusanci da ita tamkar kusanci da mutuwarka ne? "

Yusuf yace " look Amal niba wani abu nake nema a gurin Widad ba, kuma ba neman kusanci nake da ita ba, kawai ina tausayinta ne, kuma ina jin daÉ—in yadda mahaifinta ke mutuntani"

"kace tausayi Yusuf? Yusuf daga tausayi so yake shiga, ban taɓa ganin mutumin daya samu damar da ka samu a gurin ta ba, Yusuf a gidan nan ba kowa keda ikon zuwa inda take ba in bada izinin ta ba, kai kuwa kana iya zuwa gurin ta duk lokacin da kake so a matsayin ka na direbanta, Yusuf ina kishin ka, Yusuf sonka nake wallahi bazan zuba ido abubuwa su cigaba da gudana tsakanin ka da Widad a haka ba"

"Amal, Soyayya tsakanina dake ba zata yuwu ba, Mahaifiyarki bata ƙaunar talaka, kuma ni talaka ne inani ina iya Soyayya dake Amal?Hausawa suka ce ƙwarya tabi ƙwarya, idan tabi akushi zata fashe"

"dakata Yusuf" Amal ta katse shi, hawaye tuni ya fara sintiri a idon ta, tace  "bazaka iya Soyayya dani ba, amma zaka iya da Widad ko?"

"Amal ni ba Soyayya nake da Widad ba, inani ina son mace kamar ta, ita a kanta bata yarda da wata soyayya ba, Amal nayi Soyayya a baya, abun da na fuskanta a soyayya bazan ƙara yadda in sake fuskantar sa ba, ke kanki da kin san wayeni bazaki soni ba, ba zaki so kasancewa da mutum kamar ni ba, kiyi hakuri "

"ba abunda ya shafeni, what I know is that ba zan zuba ido ka faɗa soyayya da mahaukaciya mara tarbiyya ba, kuma bari in gaya maka ba zaka taɓa kuɓucemin ba kasa wannan a ranka"

Tana gama faÉ—ar haka ta juya da sauri ciki tana kuka, jikin Yusuf yayi sanyi a haka ya ja jiki ya fito.

Masallaci ya wuce yai sallolinsa, sannan ya zauna yana karatun Al'qur'ani mai girma, ya daɗe yana addu'a sannan ya miƙe ya nufi titi dan samun abun hawa zuwa gida.

Abunka da unguwar masu kuɗi, tuni unguwar tayi tsit se sanyi bishiyoyi dake kaɗawa, yana ta tafiya a ƙasa yana tunanin abubuwa da dama, ya baro layin su Widad sosai inda security suke, ba tsammani se gani yayi ansha gaban
sa da mota, tsayawa yayi cak yaga ikon Allah.

Wasu ƙarti ne suka fito daga motar suka zagaye shi, ɗayan yace  "kaine direban 'yar gidan Alhaji Nasir?"
Ba tare da tsoro ko shakka ba Yusuf yace  "Eh nine"

"Good labari ya ishemu cewar akwai kusanci tsakanin ka da ita, duk inda zata tare kuke zuwa, an samu mu ɗakkota kwanaki amma ka hana, bari in gaya maka wani abu, zamu ƙyaleka ne saboda zakayi mana amfani, zamu ci gaba da bibiyar ka saboda akwai wani abu da muke so ka karɓo mana a gurin ta" cewar ɗaya daga cikin ƙartin

Yusuf yace "Babu wani kusanci tsakanin mu, aiki nake mata tana biyana, ko meye kuje ku tambaye ta ta baku mana"

ÆŠaya daga cikin sune ya sakarwa Yusuf wani mummunan naushi, da seda jini ya fito daga bakin sa, a zuciye Yusuf ya É—ago yana kallonsu, babban yace

"Wallahi idan baka kawo mana abun nan ba se mun kasheka, akwai wasu mahimman abubuwa da muke so ka karɓo mana a gurinta idan kaƙi semun maka yankan rago"

"Bayan yankan ragon se kuma me?" Yusuf ya faÉ—a babu alamar tsoro

Wani naushin suka ƙara masa a gefen ido,
Maimakon Yusuf ya tsorata, ko ya nuna jin zafin naushin, se yayi murmushi yace

"idan kunmin yankan rago, ku kuma ku zauna a naɗe duniya daku?, babu wani mahaluki daya isa yasa Yusuf yin wani abu dan son zuciya da zalunci, kuje ku gayawa wanda ya aiko ku cewar karya kuskura yayi gangancin cin iyakar gonar da ba tasa ba, idan kuma yaƙi zanwa shukokin feshi in ƙone nawa da nashi, kowa ya rasa, wannan saƙon Yusuf ne ga uban gidanku ko wayeshi"

Wani naushin suka yi niyyar kai masa amma ya riƙe hannun ɗayan.

"Waye kai? Waye ya gaya maka wanine ya turomu?" cewar É—aya daga cikin su

"yadda kuka binciko kuka gano nine direban Widad, haka yakamata ku bincika kusan wayeni, nasani aikoku akayi ku koma ku ƙara tabbatarwa wanda ya aikoku nina ɗauke Widad lokacin da yasa a sace ta, ni aikina tuƙata a mota dan haka ya kiyayi yunƙurin cutar dani"

Hausawa sukace 'sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi, sun daki Yusuf sosai, yaso yayi amfani da bindigar sa, amma yin hakan ze rusa masa da yawa daga shirinsa, dan haka ya fasa ɗaukar bindigar, suka daddake shi, wani yana iya ramawa wani kuma baya iyawa.

"zamu cigaba da bibiyarka, harse ka bamu abunda muke nema, zaka gane baka da wayo, Uban taurin kai, Ubangidanmu yafi ƙarfinka"

haka suka barshi a gurin suka tafi.

Da ƙyar Yusuf yaja jikin sa ya hau Napep ya tafi, hancinsa yana ta zubar da jini, jiri ne yake ta ɗibarsa saboda jinin da yake zubarwa da yawa, da ƙyar yaje gida, Allah ya temake shi Umma tayi bacci.

ya cire kayan jikinsa yana goge jinin fuskarsa, Aljihun wandonsa ya taɓa yaji wayar da Widad ta bashi ɗazu.

Hannu yasa ya ɗakko ta yana jujjuya ta  "Ka ɓoye ta kamar yadda zaka ɓoye ranka, wannan wayar tamkar rayuwar ka ce"

Maganar Widad ta dawo masa, kunna wayar yayi, Amma akwai password akai shiru yayi yana nazarin kamar yaya wayar nan tamkar rayuwar sa take? Ajiye wayar yayi ya shiga yayi wanka ya fito, nan ya shiga aikin nasa na tunani dan abubuwa da dama sun faru da suke buƙatar nazari.

"Me Widad taje yi Hotel? Me ta gani ya sata kuka? Waye ya turo mutanen nan? Ko waye akwai sa hannun wani a gidan su Widad? Amma dagaske Tausayin Widad zesa ya fara sonta? Me yasa tasa a durƙusa a bashi haƙuri yau? Tabbas zata iya yuwuwa akwai Alaƙa tsakanin wani a gidansu Widad da mahaifin Nurat"

Ji yayi kansa kamar ze fashe, dan haka ya rintse idon sa yana addu'a da fatan bacci ya ɗauke shi koze ɗan samu nutsuwa, Amal ta faɗo masa a rai itama, wai ita bilhaƙƙi son shi take.
Wani tunani ya shigayi watanni shida da suka gabata, da yanzu yana nan da Auren sa, katsam a dalilin irin tasa ƙaddarar aka fasa wannan Aure, bayan cin zarafi da wulaƙanci daya fuskanta daga iyayen matar daze Aura, bacci dai se ɓarawo ne ya ɗauke shi.

*******************************

Da safe Yusuf ya tashi da matsanancin zazzabi, kansa har sarawa yake sosai saboda dukan da yasha jiya, juyi kawai yake akan gadon gaba ɗaya jikin sa ciwo yake masa, ganin har kusan ƙarfe tara be fito ba yasa Umma leƙawa ɗakin sa, ta tarar da shi kwance a kan gadon sa, ƙarasawa tayi ta taɓa jikin sa tace  "Yusuf lafiya kuwa? Naga har ƙarfe tara baka fito ba?"

"Bana jin daÉ—i ne Umma"
"dan baka jin daÉ—i seka zo ka kwanta kana juyi, ka tashi ka watsa ruwa, ka karya seka sha magani"
"to Umma"
Yusuf ya miƙe ya shiga yai wanka, kayan breakfast ɗin ta kawo masa ɗaki, ta kalle shi tace 
"Yusuf kamar kumburi nake gani a gefen idonka da bakin ka"

Yusuf yace  "Mun faɗi akan babur ne jiya da daddare"

"Amma ka kasa gayamin? Meye amfanin hakan, haba Yusuf"
Yusuf yace  "Yi haƙuri Umma, bana son ɗaga miki hankali ne"

"Amma ina fatan ba wani mummunan ciwo daka ji?" tai maganar cike da damuwa

"Eh banji ciwo me yawa ba"

Da kanta ta zauna tana bashi Abinci a baki, ta É—akko masa first aid box É—insa ya É—au magani ya sha, ya koma ya kwanta.

Kwanciyar sa ba daɗewa Abbas ya kira shi, da ƙyar Yusuf ya ɗaga wayar, Abbas yace  "Mutumina kana ina ne? Ina son ganin ka"

"Ina gida bana jin daÉ—i ne"

"Subhanallah, meya sameka?"

"Zazzabi ne" Yusuf ya bashi amsa

"Shikenan gani nan zuwa"
Su kayi sallama

**************************

Hajiya Halima na zaune falon ta tana shan tea, Isa mai gadi yazo yana kwaɗa sallama a ƙofar falon ta, A fusace tace "wai meye hakane? Lafiya kame do kamin wannan sallama kamar kana bina bashi?"

"Hajiya nine, Isa ne"
"to ya a kayi?"
"Hajiya gurin ki nazo"
Ta ɗanyi tsaki sannan tace  "shigo"
Ya shiga falon ya durƙusa yace 
"Ina kwana?"
"Kai bana son doguwar gaisuwar nan meke tafe da kai?"

"to Hajiya kin san shi sha'ani na rayuwa kiwon mutum ake ba dabba ba koba haka ba?"

"kai nifa bana son wannan surutam banzae, ka faÉ—amin kanka tsaye meke tafe da kai"
Chapter 31 · 0% Book details