← Book details Akidata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 82

Sashe 16

Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu kowa a babban Falon dan haka Kai tsaye part É—in ta ya nufa da ita, Ya kwantar da ita akan gadon ta.
Yasa hannu a aljihunsa, ya É—au wayarsa ya kira Abbas, bugu É—aya ya É—auka yace
"Kai ya haka? Zaka kirani a wannan daren?"
"Kai akwai matsala fa"
"Matsalar meke nan?"
"Widad na kai gurin birthday akayi barazanar za'a kasheni idan ban bar gurin ba, ina komawa na neme ta na rasa, da ƙyar na ganta, yanzu haka na dawo da ita gida Amma bata san inda kanta yake ba, I thinks they Use sedative substance on her, nayi niyyar in tsaya da ita a Asibiti Amma naga hakan hatsari ne babba"

Abbas ya numfasa yace  "Gaskiya kam zata farfaɗo Insha Allah, gobe in Allah ya kaimu ka shigo Office kawai za muyi magana"

"Shikenan Allah ya kaimu" suka yi Sallama, ya maida Wayar Aljihunsa ya kalli Widad da take ta bacci bata san meke faruwa ba se sauke numfashi take, Yusuf ya É—auki bargon dake gefen ta ya rufe ta dashi saboda yanayin Sanyi, wayarta ce keta ringing a Jakarta ya buÉ—e Jakar ya É—akko wayar ya kashe ta gaba É—aya, Sannan ya kama hanyar fita.

Yusuf ya fito ya nufi hanyar fita, yaci karo da Ramlah a babban falo, share ta yayi ze wuce.

"Daga ina kuke a daren nan? Me kake a ɗakin Widad a wannan lokacin?" muryar Matar gidan ce, dake tsaye a ƙafar bene.

Yusuf ya juyo ya kalle ta sannan yace "Na kaita unguwa ne"
"Me kake a É—akin ta a wannan lokacin? Bata da lafiya ne, na kaita É—akin ta ne"
"Ka kaita É—akin ta kai a wa?" Ramla ta tambaye shi.

"Ni ba a kowa ba, ni a É—an uwan ta musulmi, kuma ma'aikacinta"

"Kai shashasha rufemin baki" Hajiya Halima ta katse shi cikin tsawa.

"Naga kanka yana rawa, to bari in tuna maka kai ba kowa bane face matsiyacin talaka, ka dena jin kanka kamar wani me iko dan kaga mai gidan nan yana wani baka girma na musamman kai É—in ba kowa bane ba"

Amal da take jiyo hayaniya ta fito daga É—akin ta, tana zuwa ta tarar da mahaifiyar ta ta saka Yusuf a gaba tana zagin sa
"Haba Mummy, me Yusuf yayi miki kike masa wannan cin mutunci haka?"
Ramla tace  "An zage shi ɗin, meye alaƙar ki dashi? Ɗan uban waye shi da ze dinga wani jin kansa, dan yaga ya samu gindin zama, saboda tsabar cin fuska akan wannan banzan waccan mara mutuncin ta dizgani"

Yusuf ya É—an murmusa yace
"Nasani niba kowa bane, talaka ne ni gaba da baya, dan haka ku kwantar da hankalin ku,kuma ni bana sawa kaina ni wani ne" yana gama faÉ—in haka ya juya ya fice.

Amal tace "Mummy koma menene laifin Widad ne, ni banga abunda Yusuf yayi ba"

Hajiya Halima cikin tsawa tace "dalla rufemin baki banza, naga zaƙewar ki kema tana yawa akan yaron nan, ki shiga hankalin ki tunda wuri, ni sam yaron nan be minba, ya fiye kalar munafukai"

Ramla tai caraf tace  "wallahi kuwa Mummy, ni kaina ban yadda dashi ba, Ina jiran sakamakon binciken da kika sa ayi a kansa ne"

Amal tace  "Mummy koma menene Yusuf bare ne aiki ne ya kawo shi gidan nan, bekamata a saka shi a wannan sabgar ba"

"Amal kenan ke har yanzu yarinya ce, baki san inda rayuwa tasa gaba ba, kashedina dake shine, tun wuri ki fita daga sabgar yaron nan, dan muddin na gano wani abu saɓanin abunda nayi zato a tattare dashi ba abunda ze hana insa ayi masa abunda ya dace da shi"

"Amma mum....

"Ke rufemin baki, shashasha kawai"
Mummy tayi maganar tare da juyawa zuwa ɓangaren ta, Ramla ma tabi bayan ta suka bar Amal a falon tsaye.

Yusuf na fitowa, Nura ya biyo shi yace
"A'a kaga ɗan gatan 'yar masu gida, gaskiya Yusuf ka ciri tuta, naga' yar masu gida tana yi da kai, ƙiri Ƙiri ta koreni kuka tafi unguwa, naga duk inda zaka tare kuke tafiya"

Kafin Yusuf ya bashi amsa, Isa mai gadi ma ya nufosu yana cewa
"Nikam Malam Yusuf baka gayamin meyasami Uwar ɗakin ka ba, nifa abun ya bani mamaki, iya sanina dai bata shaye2, sedai taɓun hankali amma meyafaru da ita haka?"

Kallon su yayi É—aya bayan É—aya yana karantar tsantsar munafunci da son jin gulma a fuskokin su, sharesu yayi bece musu komai ba yai gaba abunsa ya fice ya bar gidan.

Yusuf na fita, Nura yace
"Ji shi se kace ɗan uban wani, muna masa magana amma yayi mana banza, da Alhaji ne uban sa bansan wulaƙancin da ze ba"

Isa yace  "Bar mara mutunci, ji yadda muna masa magana ya share mu, Anya Nura mutumin nan ba Asiri yayi wa me gidan nan ba?"

"Ni zance maka Asiri yayi masa hadda 'yar sa ma, kana gani É—azu ta hana Ramla binsu saboda shi, da muka dawo daga filin jirgi se cewa tayi ni in sauka in hau motar haya in tafi gida, shi kuma ya kaita unguwa"

Isa ya jinjina kai yace  "Kana gani duk jin kai da izzar ta, duk Aƙidar ta ta rashin yadda da mutane Amma duk inda zata tare dashi suke tafiya, dudu yaushe yazo gidan nan? Ko wata ɗaya be cika ba ya samu wannan gindin zaman, mu kuwa shekara nawa muna aiki a gidan nan? Ba abunda yake haɗamu da ita se cin mutunci da wulaƙanci "

Nura yace "to ai magana ce a buÉ—e, Allah kaÉ—ai yasan abunda suke yi"

Isa yace "kuma fa hakane zancen ka Nura, taɓ aikuwa zamu ƙara saka ido sosai, zamuyi maganin wannan gani-ganin da yake mana"

Haka suka zauna suka cigaba da gulma, suna muzanta Yusuf da miyagun kalamai.

Yusuf kam kansa ya kulle Sosai, daya koma gida ma kasa bacci yayi, yana ta nazari akan abubuwa da dama yana son gano bakin zaren amma ya rasa ta ina ze fara, gaba ɗaya Al'amuran a cukurkuɗe suke, me zesa Baban Nurat yunƙurin sace Widad? Waye mahaifin Nurat? Dole Akwai dalilin da yasa Widad take da wannan AƘIDA na ƙyamar talaka da nesanta kanta da mutane, yanayin Abubuwan da take yi wasu lokutan yasa Yusuf ya fara gazgata cewar tana da taɓin ƙwaƙwalwa, tunani ya haɗu ya cunkushe massarafar gangar jikinsa wato ƙwaƙwalwarsa, ba shiri ya tsagaita tunanin ya kwanta da ƙudurin dole yaje Office da safe, akwai buƙatar yaga Abbas.

A hankali ta motsa daga nannauyan Baccin da take, ji tayi kanta kamar an ɗora mata wani nannauyan dutse, gaba ɗaya gaɓoɓinta sun mata nauyi, a hankali ta buɗe idon ta ta ƙarewa ɗakin nata kallo, ta mayar da idanunta ta lumshe na wasu daƙiƙu sannan ta sake buɗe su, a hankali taja jikin ta ta miƙe zaune, kallon jikin ta tayi tare da ƙoƙarin son tuna abunda ya faru, sosai take takura ƙwaƙwalwarta don ta tuna mata abunda ya faru, Amma fafur ta kasa tuna komai, dafe kanta tayi wanda taji yana sara mata, ta miƙe jiri na kwasar ta ta tafi banɗaki.

Da sassafe ko karyawa Yusuf beyi ba ya fito ze fita. Umma dake kitchen tana ƙoƙarin haɗa Abinci ta leƙo tace
"Yusuf me zan gani haka? Ba zaka tsaya ka karya bane?"
Yusuf yace  "Umma sauri nake ne, bana son in makara akwai aikin da nake son yi"
"Yusuf nifa gaskiya wannan aikin da kake a gidan masu kuɗin nan ba sonsa nake ba, nasan halin masu kuɗi da rashin mutunci da wulaƙanta talaka, nidai gaskiya su canza maka wannan aikin su baka wani, danni gaskiya bana son kaje inda za'a wulaƙanta min kai"
Kallon Umman sa yayi, ya ɗanyi murmushi ya tako gaban ta ya riƙe hannayen ta yace
"Kyakkyawar Uwa, Uwa da babu irin ta, ina Alfahari dake Umma na, yadda kike kula dani Allah ya kulamin dake ko bayan raina, ki kwantar da hankalin ki, basa wulaƙanta ni, kuma yanayin aiki ne yazo a haka, dana Kamm zan koma Office, idan kuma kince ba kyason aikin se in haƙura gaba ɗaya"

Badan ranta yaso ba tace  "Yusuf ba aikin ne bana so ba, ni wannan aikin da suka baka ne bana so, yaushe rabon da muci Abinci tare, in ka fita tun safe se dare, Amma shikenan dai, Allah yayi maka Albarka, Allah ya sadaka da Alkhairi a duk inda kake"

"Ameen Umma na, bari in sauri sena dawo"

"Allah ya kiyaye hanya"
Ya amsa da "Ameen" ya fice.

Kai tsaye headquarters su ta jam'ian tsaro na farin kaya ya tafi.
Kasancewar Yusuf mutumin kirki yasa tun daga gate masu gadi suke gaida shi, ya tsaya suka gama gaisawa sannan ya shige ciki.
Ofishin sa ya nufa kai tsaye, yana zuwa ya tarar da shi tsaf ana shiga a gyara masa dukda baya nan, Na'ura me ƙwaƙwalwarsa ya ɗakko ya kunna, ya ɗan jira kaɗan sannan ya fara daddanawa.
Gaba ɗaya ya nutsu sosai hankalinsa kacokan yana kan Computer, da gani kasan ƙoƙarin gano wani abu yake me mahimmanci.

Sallamar da'akayi a office ɗin ne yasa shi ɗagowa, Sakina ce sanye da suit na aiki kamar yadda ta saba, fuskar ta ɗauke da murmushi ta ƙaraso tana wani fari da ido, Sam Yusuf baya ƙaunar mace mara kamun kai, shiyasa sam Sakina bata burgeshi.

Kujera taja ta zauna, ta kalle shi tace "wata sabon gani, aiki ya ɓoye mana kai gaba ɗaya haka, ba'a jin ɗuriyar ka ko a waya, na kira ka harna gaji baka ɗagawa"

Yusuf "Aikine ya É—anmin yawa shiyasa, Ya aikin?"

Cikin iyayi tace  "Alhamdilillah, Fatan dai kana lafiya?"

Cike da basarwa yace "Lafiya ƙalau"
Ya cigaba da latsa computer sa.

"Kwana biyu da baka zuwa duk gurin nan ba daÉ—i, nayi farincikin zuwan ka sosai"

Bece mata komai ba ya ɗakko wayarsa ya ɗan daddana ya kanga a kunnen sa, ya ɗanyi shiru na wasu daƙiƙu sannan yace
"Ya Abbas ka shigo ne?"

Ya sake yin shiru sannan yace 
"Ok nima na shigo yau akwai buƙatar in ganka, bari inzo office ɗin naka"

Yana gama wayar ya miƙe ya fice ya bar Sakina a gurin, ba tare da yace mata komai ba.

Wani ƙululun baƙin ciki ne ya tokarewa Sakina zuciya, tabi bayan sa da kallo tare da yin ƙwafa.
Chapter 16 · 0% Book details