← Book details Akidata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 82

Sashe 18

Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ramla tace  "Mummy ƙyaleta dan Allah, me abun haushi kawai, Amma Mummy ta yaya ze iya mana amfani a nan gaba?"

Murmushi Mummy tayi tace "zan miki bayani Ramla, ba zanyi a gaban wannan shashashar ba, dan yanzu na kasa gane inda tasa gaba"

Widad kam, suna zuwa falonta ta tsaya ta juyo ta kalli Yusuf, ta ƙure shi da ido tun daga sama har ƙasa, yayin da shi kuma ya ƙi yadda ya ɗago ido ya kalle ta, ta daɗe tana kallon sa tana nazarinsa.

"Look up" ta faɗa a taƙaice, ɗan ɗagowa yayi ya kalleta ya maida kansa ƙasa.

"Ya aka yi na dawo gidan nan jiya? Meyafaru dani a gurin party jiya?"

Dama Yusuf yasan a rina, dan haka a dake yace

"Eh kin faÉ—i ne akan stage, shine muka taho gida"

"Malam ƙarya kake, ka gayamin meyafaru? Ko kaima kazo ne dan a haɗa kai da kai a cutar dani?"

Yusuf ya girgiza kai yace  "Me yasa kike tunanin za'a haɗa kai dani a cutar dake? Meye riba ta in an haɗa kai dani an cutar dake?"

"Saboda talaka ba abunda baze iyayi akan kuɗi ba, An haɗa kai da kai an turo ka ka cutar dani, in ba hakaba meyasa lokacin da nace kasa hannu a death contract ka yadda ba tare da ko ɗar ba ka cigaba da aiki dani? Wannan shi ne karo na biyu kana min ƙarya, meyasa? Ta yaya zan faɗi haka kurum bani da wani special case, se taɓin hankali, shima kuma ƙaƙabamin shi akayi, ta yaya haka zata faru? Bana tunanin na samu mental attack ne haka kurum a gurin nan, Ka gayamin gaskiya you are here to kill me, you were sent by someone to kill me " cikin ɗaga murya, tare da tsantsar rashin yadda take maganar.

Gaba ɗaya ta birkice, Yusuf yai shiru ya ƙura mata ido yaƙi cewa komai.

A fusace tace  "talk to me!!"

"Am not here to kill you, na karɓi aikin nan ne saboda shine last option ɗina, idan banyi aikin nan ba babu wata hanya da zan samu abunda zan kula da kaina da mahaifiya ta, talaka ze iya komai akan kuɗi, Amma be kai yadda me kuɗi zeyi ba, me kuɗi yafi talaka son kuɗi da aikata komai dan ya mallake su, da zan cutar dake da tuni nayi tunda kika amince kije ko ina tare dani, someone attempts to kidnap you yesterday night, that's all I know"

Dafe kai Widad tayi ta shiga sintiri a gurin, gaba ɗaya idonta yayi Ja se gumi take, a hankali ta  furta
"Jeka falo ka jirani, zamuje gidan Bulama yanzu"
Yusuf ya jinjina kai ya koma babban falon.

Kusan mintuna sha biyar yana jiran ta sannan ta fito, yauma dai babu batun mayafi balle hijjabi a jikin ta, haka suka fita.

Alhaji Haruna ne mahaifin Nurat É—auke da waya a kunnen sa yana waya, yana yi yana sharce gumi duk da sanyin Na'urar sanyaya É—aki dake É—akin amma gumi yake yakicewa, cikin inda inda yake cewa
"wallahi ranka ya daɗe seda aka shirya komai, dan yarinya ta Nurat ta tabbatar min da taje gurin party, taje gidana, dan an gama komai an sumar da ita, ana jiran sahu ya ɗauke azo a ɗauke ta, wani matashi yayiwa Yarinya ta barazana ya ɗauke ta ya tafi da ita, kuma ni a iya sanina ko su Alhaji Musa da muke komai tare dasu muke neman abu ɗaya basu san mun ƙulla alaƙa da kaiba balle ince haɗin baki ne"

Ɗaya ɓangaren yace  "Shikenan zanyi wani shirin na mussman, Amma idan ka bari muka kuma rasa damar mu a karo na biyu zan ajiye ka a gefe in nemo wani"

"Insha Allah baza'a sake samun matsala ba Alhaji Bukar"

Alhaji Bukar yace "Allah yasa, sannan batun wannan matashin kabar komai a hannu na, nasan abunda zanyi"
"Shikenan godiya nake ranka ya daÉ—e " daga nan suka yi sallama.

************************
Bayan fitar su Widad, Mummy tasa aka kira mata Isa mai gadi.
Isa yaje ya same ta a falo, cikin rawar jiki ya gaida ita ta amsa masa a wulaƙance ta kalle shi tace
"Kai na baka aiki amma har yanzu nani shiru ko bazaka iya bane?"
"A'a ranki ya daÉ—e, yaron ne gaba É—aya baya sakin jiki damu yanzu, wani mugun jin kansa yake kamar wani basarake"

Ta jinjina kai tace  "tabbas nima naga hakan, kuma da sannu zan kawo ƙarshen wannan izzar da yake ji da ita, talakan banza asararre, kaje kayi abunda na saka, bana so yasan nasa a bibiye shi ne, ka nemo min inda yake zaune, zan sa ayi maganin sa, tashi ka koma bakin aikin ka"

Ya tashi sumi sumi ya fice.

***********************

Yusuf suna zuwa gidan Bulama suka yi sa'a yana nan, a harabar gidan suka ganshi yana shan lemo, hannun sa É—auke da Jarida.
ÆŠago idon da yayi ya sauke akan Widad yasa shi sakin murmushi, itakam fuskar nan a murtuke ba annuri.

Alhaji Bulama yace  "barka da zuwa lovely daughter"

A ɗan ciki tace  "barka da hutawa Daddy"

"Yawwa barka lovely daughter, ya akayi ne na ganki a haka? Meke faruwane? Ko ciki zamu shiga?"

Yusuf a ransa yace "wata sabuwa, yau kuma Alhaji Bulama take kira da Daddy, idan taga dama kai tsaye take kiran sa da Bulama, wannan yarinya akwai ta da rikici, bata da Alƙibila sam"

Ta yamutsa Fuska tace

"A'a nan ma ya isa, Amma Daddy akwai matsala fa"

Ya tattaro hankalin sa kanta yace  "matsalar me daughter"

"Ana farautar rayuwa ta har yanzu, daga fita jiya aka kusa saceni, nidai tunda Daddy baya nan kamin visa zan bar ƙasar nan, gara in ƙarasa Rayuwa ta a can ƙasashen wajen"

Alhaji Bulama yace "waye yayi attemptin ɗin sace ki, kuma a ina? Shiyasa tuntuni nace a samo masu tsaron lafiyar ki"

"Bashi da mahimmanci kasan inda naje, da wanda yai yunƙurin saceni, duba da tsawon shekaru kun gaza maida hankali ku gano hakan, kuna ɗaukar wasu maganganun nawa  a matsayin maganganub hauka, kawai ka nema min visa zan bar ƙasar nan"

"Haba lovely, saboda me zaki bar ƙasar ki ta haihuwa? kije ki cigaba da rayuwa ke kaɗai a wata uwa duniya? Nace a ɗaukar miki masu tsaron lafiyar ki da zasu dinga miki rakiya kinƙi, kin ɗakko wannan dogarin duk inda zaki yana biye dake kamar inuwa, shiba soja ba, shiba wata tsiya ba ta ina ze iya tsare lafiyar ki?" yai maganar yana nuna Yusuf

Widad ta haɗe fuska tace  "kaikam wani lokacin se in rasa meke damun ka, aini babu me tsaron lafiya ta se Allah, Akan me zan ɗau masu tsaron lafiya ta, haka kurum a haɗa kai da masu tsaron nawa a cutar dani? I don't trust anyone"

Alhaji Bulama yace "shi wannan É—in kina da tabbacin baza'a haÉ—a kai dashi a cuce ki ba?"

Ta juya ta kalli Yusuf dake tsaye, sannan ta kalli Bulama tace  "Ba'a kansa muke magana ba yanzu , babu ruwanka kasancewarsa tare dani, muna magana akan Visa zakamin in bar ƙasar nan kawai"

"wai tayaya zan miki visa ki bar ƙasar nan? Keda muke saka ran Dawowar Fahad in next couple of weeks a fara zancen Auren ku, meya.......

"shut up please! " ta faÉ—a a hasale tana É—aga masa hannu sannan ta É—ora da cewar

" wai har yanzu baka janye wannan banzan ƙudurin naka ba ko? Kana tunanin abunda na gaya maka ƙarya nake, let me repeat myself, bazan yi Aure ba, babu namijin daya dace dani, ni ba zanyi Aure in zauna a ƙarƙashin wani ba, Allah ya bani dukiya wadda ta isheni rayuwa, bana buƙatar wani Aure, hankalina na kan son ganin bayan maƙiya na, koni ko su, ko kuma muyi mutuwar kasko"

"Widad, dukiya shirme ce idan babu Soyayya da kulawa, ban hanaki gano wanda suka rusa farincikin rayuwar ki ba, Amma aure yana da mahimmanci a rayuwar ki, bakya son ganin 'ya' yan ki a duniya? Aure garkuwa ne Widad"

"Soyayyar banza, is just stupidity and form of mental disorder,  an imagination and bunch of problems, bana buƙatar soyayyar kowa, nikaɗai zan gudanar da rayuwa ta, na ishi kaina rayuwa bana buƙatar kowa yayi min garkuwa"

Zuwa yanzu Yusuf ya saba jin ire iren wannan maganganun na Widad, Amma yana kallon ta a wani iri idan yaji tana faÉ—in wannan kalaman, ta yaya mutum zece ze rayu shi kaÉ—ai, ba abokin rayuwa ba 'yan uwa ba Abokan Arziki? Kafin ya bawa kansa amsar tambayoyin ya tsinkayi murayarta tana cewa

"Wallahi ko kana so ko baka so, ba zan cigaba da zama a ƙasar nan ana farautar rayuwa ta ba, kuma ba zanyi Aure ba babu shi a tsarina"

Bukama yace "Aini bance dama ki zauna a ƙasar nan dole ba, da zarar an ɗaura miki Aure ƙasar nan zaku bari gaba ɗaya keda mijinki, kinga kin tsallake tarkon maƙiyanki"

Cikin izza me bayyanar da tsantsar ikon da take dashi tace
"Wani tabbaci kake da shi shi É—an naka baza'a haÉ—a kai dashi a cutar dani ba?"

"Idan har É—an dana haifa ze cutar dake, da nine mutum na farko da ze cutar dake da mahaifinki, dan a yanzu mahaifinki bashi da ka mata"

Widad ta miƙe tsaye ta dafa teburin ta kalli idon Bulama tace
"Zan bar ƙasar nan ko kana so ko baka so, kuma bazan Auri ɗanka ba, babu Aure a tsari na, ina fatan wannan ya zama karo na ƙarshe da zan gaya maka babu Aure a tsarin Rayuwa ta, Ganin bayan maƙiya na shine a gaba na"

Ta juya ta nufi inda Yusuf yayi parking ɗin mota, da sauri Yusuf ya riga ta ƙarasawa ya buɗe mata gaban mota, dan bata zama a bayan Mota.

Yusuf ya fara tuƙi ba tare da ta kalle shi ba tace  "Muje Farm House" shima be ce mata komai ba, ya ɗauke kan motar zuwa hanyar gidan gona.
Suna tafe Yusuf yana tunanin wani dalili ne yasa kowa yake tsoron Widad haka? Take faÉ—awa kowa abunda ta ga dama komai tsufan sa kuwa? Indan Mahaifinta yana da kuÉ—i ne, suma ai masu kuÉ—i ne.
Chapter 18 · 0% Book details