← Book details Akidata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 82

Sashe 67

Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhaji Musa yace "Good hakanma yayi, a hana kowa zuwa inda yake muyi yadda muke so, Amma Nifa har yanzu ina mamaki akan guduwar yaran nan, kuma da suka kuɓuta aida zasu dawo a gari a gansu, amma har yanzu babu wanda yaji ɗuriyarsu"

Alhaji Munir yace  "ni kaina abunda yake ɗauremin kai kenan, zuwa yanzu ai yaci ace anji labarin sun dawo, amma babu wanda yaji hakan"

Alhaji Musa yace "shiyasa nake tunanin akwai wata a ƙasa ruwa baya tsami banza, akwai munafiki a cikin mu"

Alhaji Haruna yace "kamarya? Kana nufin a tsakaninmu munafikin yake kokuwa?"

Alhaji Munir yace "kunga ya isa haka, nima nayi zargin haka amma babu lallai da munafuki a tsakaninmu, sedai a wanda suke mana aiki tabbas, kokuma akwai wani a gefe daya ke farautar abunda muke nema"

Alhj Haruna yace  "ba abunda baze iya faruwa ba, Amma kar mu ɗora komai akan zargi semun tabattar"

Kamar yadda Saleh ya bada umarni, aka ginawa Widad nata banɗakin, akwai wata ƙatuwar rijiya a gidan ruwan sam bashi da kyau, haka nan ake amfani dashi a gidan, ko kuma mutum yayi tafiyayyiya yaje rafi ya Ɗebo.

Yusuf kuwa tafiya yake me nisa, yaje ya É—ebo ruwa a wannan borehole guda É—aya tal ta garin, yazo gida ya tafasa idan ya huce seya zuba a randarsu suke amfani da shi a matsayin na sha.

Har yanzu Widad bata saba da kowa a gidan ba, ba ruwanta dasu sedai in sun haɗu a tsakar gida suka mata sannu ta amsa, amma bata shiga sabgar Hari sam, saboda Hari baƙar magana take gaya mata.

Yanzu ma tana tsugune tana brush da yamma, yaran Hari suka kewaye Widad suna kallonta, mussman dogon gashinta dake É—aukar ido, gata ba ma'abociyar saka kallabi ba, abun haushi hadda 'yan matan gidan da suka tasa, se kallonta suke ita ta rasa se yaushe zasu saba da ganinta su dena mata wannan kallon haka?.

Widad tace "kai me kuke kallone, haba bana son kallon nan da kuke min, did i look like a beast?"

Hari tace "yo sunga abunda basu saba gani ba, kin fito tiɓitiɓi da wasu irin kaya ai dole su kalleki ni wallahi da ban zaci ma musulma ce ke kina jin hausa ba"

Widad tace "eh ba musulma bace ni, gunki nake bautawa yana É—aki idan kina so ki ganshi"

Sam hari bata zaci Widad tana da baki hadda baƙar magana ba.

Gwaggo tace "Amarya ƙyaleta kiyi haƙuri"

Sannan ta kalli Hari tace "haba Hari, kin fiye magana wallahi duk haƙurin yarinyar nan kinsa ta fara tanka miki"

Hari tace "yo Yaya yara sunga abunda basu saba gani ba ba dole su kalla ba"

Yusuf yana ta tunanin wace sana'ar ze ɗan fara, saboda ya saukewa mutan gidan ɗawainiyar da'ake dasu, ga Widad bakomai take ciba duk ta rame, ya dawo daga sallar Azahar ya tarar an kawowa Widad gujjiya, tanaci hadda ɓawon, Yusuf yace  "mekike ci ne?"

Ta ɗan taɓe baki tace "na manta sunanshi, amma inaga wake ne wannan maman ce ta bani"

Yusuf ya kwashe da dariya, ta haɗe rai tana kallonsa, yace "haba Madam, wannan ne waken? Kuma da ɓawo kike ci bari kiga"

Ya zauna yana ɓarewa yana bata, ita tunda take bata san wata gujjiya ba, da taci a baki se taji kamar wake, ta zata ma wake ne yazo a haka.

Tun Yusuf yana mamakin bata san abubuwa da yawa ba, har ya dena mussman duba da yanayin rayuwarta, ita ba sakewa take da mutane ba, kuma mafi yawa a waje tayi rayuwarta, dan haka yake mata uzuri a wasu abubuwan.

Yusuf yace "Ina son in fara zuwa kasuwar garin nan, inga me zan fara siyarwa saboda mu ragewa mutanen gidan nan É—awainiyar da suke damu"

"dama akwai kasuwa a dajin nan?"

"daji kuma?"

"Eh mana" ta bashi amsa

Yusuf yace "eh akwai kasuwa amma se anyi tafiya me nisa sosai, nayi magana da megari ya haÉ—ani da yaronsa tare zamuje kasuwar gobe in Allah ya kaimu inga yanayin abubuwan"

Tace "Shikenan" tana ci gaba da cin gujjiyarta, seda ta gama ta kalle shi tace "Wanka"

Yusuf yace "to"  ya haɗa mata ruwa sannan ya fita sallar la'asar

A gurin salla Yusuf yaga abun mamaki, akwai ƙaramin gurin da suke jam'in salla, akwai ƙarancin ilimi ga mutan ƙauyen, liman ya makara wani yaja salla a raka'ar ƙarshe liman yazo, raka'ar ƙarshe kawai ya samu, itama an ɗago daga ruku'u, da'aka idar Yusuf yana jira yaga liman ya tashi ya kawo wadda be samu ba amma yaga liman yayi ƙyam yaja gefe yana laziminsa.

Yusuf ya dinga kallonsa ko ze tashi ya canza sallane, amma yaga aka jima liman ya shafa addu'a ya miƙe ya gaisa da mutane ya ƙara gaba.

Yusuf yayi shiru a ransa yace "wannan mutumin dabe san hukuncin salla ba, shine kuma yake jan salla? Tabbas akwai matsala babba, mutanen garin nan suna buƙatar ilimin Addini, ya barwa ransa cewa zeyi wa megari magana, yaga ta inda ze iya basu gudunmuwa.

Ya shiga cikin gida ya shiga ɗakinsu da sallama, Widad ta fito daga wankan tana shafa mai, ba tare da ta kalle shi ba ta amsa ƙasa ƙasa, ta cigaba da abunda take.

Kusa da ita yaje ya zauna yana kallonta, duk cikin salon son yasa ta kula shi, dan idan har bashi yayi mata magana ba in zasu kwana idan ba wani abu take buƙata ba, ba zata kula shi ba.

Tana jin yadda ya zauna daf da ita ya ƙureta da ido, kamar tasan maganar yake so tayi, taƙi magana.

Cike da fargaba dan yasan ze sha masifa, amma ya maze ya kai hannunsa gashin kanta yace

"wannan gashin yaushe rabonsa da a taje shi? Insha Allah idan na fara zuwa kasuwa  indai naga comb zan siyo, in taje shi da kaina"

Bige hannunsa tayi tace "wai kai meye haka? Me yasa kake son taɓani ne? Na gaya maka bana son karka ƙara taɓani na gaya maka, in ba haka ba duk abunda nayi maka kai ka siya, haba sekace baka da zuciya, ko baka gane magana"

Shiru yayi kawai yana kallonta yadda take ta masa masifa, shi yaga tana magana ma se yaji daÉ—i a ransa, dan yaga ta rage yawan kukan da take yi.

Ga mamakinta murmushi yayi maimakon taga yaji haushi.

"kawo man in tayaki shafawa" yai maganar yana ɗaukar robar man, ƙwacewa tayi tace
"bana so na gama"

Yusuf yace"Shikenan bari in baki guri kisa kaya"

"inma baka bani gurin ba baze hanani sa kayana ba"

Yayi murmushi ya miƙe cike da jin daɗin yasa ta magana, bayansa tabi kallo yana fita ta ajiye abunda ke hannunta ta shiga goge hawayen da ita kaɗai tasan dalilinsu.

Doctor Sufyan yana Office É—insa, yana jiran lokaci yayi ze shiga tiyata, wayarsa yaji ta fara ringin, ya tsaya ya É—aga tareda yin sallama.

"Sufyan ne?"

"Eh nine"

"ina son ka kasa kunne ka saurareni dakyau, dukda nasan baka san dawa kake magana ba, hakan ya faru ne sakamakon sanin wanda kake maganar dashi a gurinka bashi da amfani, ina son ka saurareni da kyau kaji abunda zan gaya maka, kana jina ko?"

Sufyan yace "ina jinka"

"kamar yadda aka baka kwangilar sake kwantar da Daula, aka baka miliyoyin kuÉ—i akan karya warke, kuma kayi dan tuni wani percentage ya shiga hannunka, to nima aiki nake son kayi min, niba kwantar da Daula nake so kayi ba, kawar da Daula nake son kayi!!!"

Miƙewa doctor Sufyan yayi tsaye ya shiga waige waige karya je wani yaji abunda ake faɗa masa a waya, cikin rawar murya yace "amm.. Ban gane me kake fada ba fa"

"ƙarya ka keyi ka gane, kuma kaji me nace tunda ka iya karɓar kuɗi kake bashi wrong treatment, to zaka iya karɓar kuɗi ka kasheshi, likita ne kai babu me zarginka, tunda kowa yasan condition ɗinsa yayi worse, bazance ga abunda zan bi yaka ba, sedai da kanka nakeso ka yanke abunda zan bi yaka "

Wani wahallalen gumine ya dinga ratsowa Sufyan, gumi yake ji har tsakanin cinyoyinsa, yace " Amma kisan Alhaji Daula hatsari ne, dole se anyi bincike akan gawar sa, don a tabattar da abunda ya kashe shi, idan aka ganoni fa, ina da iyali da ƙananan yara nasan kasheni za'ayi, Daula babban Attajiri ne"

"meye marabar abunda kake masa yanzu da wanda nace kayi masa, sanin kanka ne wrong treatment ɗinma ze iya kasheshi, baka da damar cewa ba zakayi ba, saboda na maka tarko ta ko'ina, ina da duk yadda akayi ka karɓi kuɗi kake bashi wrong treatment, duk wata hujja daza'a kamaka ina dashi, idan kuma naga dama zan saka ɗauke ɗaya daga
'ya' yan naka ko kayi ko kuma ransa ya salwanta, zaɓi ya rage naka, sannan idan kaga dama ka gayawa wani"

Ƙit aka katse kiran, gaba ɗaya doctor Sufyan yaji kamar an zare masa laka, jikinsa se rawa yake ya duba wayarsa yaga anyi hiding ɗin lambar, dan ko unknown number be fito ba,  duk sanyin Ac dake office ɗin shi gumi yake, kamar wanda ya tuƙa tuwon gidan biki a tsakae rana.

Yau da wuri Yusuf ya shirya, dan zebi É—an megari kasuwa, É—an megarin shima matashi ne be kai Yusuf ba, a bayan gidan megari nasa gidan yake, da matarsa da 'ya' yansa shida.

Har Yusuf ya gama shirinsa, aka kawo musu Abincin safe Widad bacci take, a hankali ya ƙarasa gaban katifarta ya janye bargon jikinta, bacci take hankalinta kwance, se yarintarta ta sake fitowa ta ƙara kyau a idon Yusuf, yayi shiru yana kallonta.

A hankali ya ɗan daki pillow ɗin da take kai, amma bata motsa ba, ya sake taɓa pillow amma still bata motsa ba, hannu yasa ya ɗan daddaki nata hannun, kamar me tashin ƙaramin yaro, juyi tayi amma taƙi buɗe ido.

"Widad" karo na farko a rayuwarta data ji ya kira sunanta, taji zuciyar ta ta buga da ƙarfi, ta buɗe ido ta kalle shi

Yace "ga breakfast an kawo karya huce, kuma inason zan fita ni"

"shine zaka wani durƙuso kaina haka? Kamar zaka shige cikina"

"ke komai nayi miki lefi ne? To sorry tashi karya huce kinji gimbiyar..
Chapter 67 · 0% Book details