Sashe 24
Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Mhmm Nurat, kija bakinki kiyi shiru da wannan maganar, dan muddin kika bari wani yaji maganar nan mun kaÉ—e a gurin mahaifinki"
"Insha Allah Mum ba wanda zan gayawa"
*************************
Tunda Yusuf ya tafi da ATM ɗin nan Hajiya Halima ke cikin zullumi, dan ba ƙaramar dukiya ce danƙare a account ɗin nan ba, tunani take yadda zata gano inda Yusuf yake, tasa a ƙwato mata ATM card ɗin nan.
Ramla ta aika ta kira mata Isa me gadi, ba tare da ɓata lokaci ba ya biyo Ramla jikin sa na tsuma zuwa falon Matar gidan.
"Kai wani irin sokon gara ne haka? Har yanzu ace ka kasa gano inda wannan talakan banzan yake?"
"Wallahi ranki ya daÉ—e ya dena zama a cikin mu ma, wani girman kai yake ji da shi, yanzu shi kaÉ—ai yake al'amuransa ko inda muke ya dena zuwa, iyakacinmu da shi gaisawa"
Dogon tsaki Hajiya Halima taja tace "dallacan sakarai ni rufemin baki, tashi ka bar nan sakarai kawai, ni na tsaya bi ta kanka, zan nemi wanda zasu yi min aikin".
Isa ya tashi jiki a sanyaye ya bar falon,
Mummy ta kalli Ramla tace "Ramla meye abunyi ne? Me ya kamata muyi?"
"wallahi Mummy kaina ya kulle, na rasa abunyi, yarinyar nan ta tabbata mahaukaciya, Mummy idan dukiyar nan ta salwanta ya zamuyi?"
Hajiya Halima tayi ajiyar zuciya tace "bana tunanin yaron nan ze gudu da ATM ɗin nan, Widad tana da wayo ze iya yuwuwa tarko tayi masa, Amma tunda harta yadda dashi haka, dole mu janyo shi cikin mu"
"Hakane Mummy zeyi mana Amfani, idan har ya kasance a ɓangaren mu, Ammafa kamar zeyi taurin kai gayen"
'idan yaƙi yin yadda muke so, then we should exact power over him, you know what I mean "
Ramla ta jinjina kai tare da yin murmushi tace
"Am proud of you Momma "
*****************************
Kwance yake akan makeken gado a wani tangamemen ɗaki me ɗauke da kayan alatu, ya mimmiƙe ƙafafuwan sa hannun sa riƙe da waya yana kallon hotuna. Gefen sa wani matashin ne zaune a gefen gado yana tattaɓa System.
Hotunan Widad ne akan screen ɗin wayar kala kala yana kallo yana murmushi, kowanne se ya tsaya yayi zooming ɗinsa ya ƙare mata kallo, yanayi yana shafa sajensa tare da tattausan murmushi, ga dukkan alamu yana jin daɗin kallon hotunan nata. A hankali ya furta
"Can't wait to see you darling"
Matashin da ke gefen sa ne ya waigo ya kalle shi yaceÂ
"Nifa ka isheni, se kace akanka aka fara Soyayya, kullum se kayi zancen yarinyar nan seka kalli hotunan ta, kuma ban taɓa jin ko waya kayi da ita ba"
Shafa sumar kansa yayi tare da yin murmushi yace "bazaka gane bane Fahad, yarinyar ce 'yar daru se hankali, dukda ƙanwa tace amma halinta daban yake, ina tunanin yadda zata karɓi soyayya ta idan na bayyana mata"
"saboda me kake wannan tunanin?"
"saboda tace shi kansa son bata yadda dashi ba"
Ƙyalƙyalewa da dariya Fahad yayi yace "Wallahi Anwar kana ruwa, se kace ita kaɗaice mace kaje ka nemi wata mana, dama da ganin ta zatayi izza, nifa rabona da ita tun tana yarinya ƙarama sosai"
Anwar yace "hmm tabbas da zaka ga Widad a yanzu ba zaka taɓa cewa in haƙura da ita ba, Ina matuƙar sonta, na ƙagu in koma gida, wallahi yadda na ƙagu in ganta be kai yadda nake son ganin su Amal da Ramla ba, gashi seka rigani komawa da sati biyu"
Fahad yace "lallai ka tsunduma da yawa, nima ina son in koma inga Ramla, dukda ni muna waya da chatting da ita"
"Aishi yasa nake ta Addu'a, Allah ya bani Widad a matsayin mata"
Fahad yace "Hmm Allah dai ya baka me sonka"
***********************
Gaba ɗaya hankalin Hajiya Halima yaƙi kwanciya, gashi duk wanda ze kaiwa Alhaji Nasir ƙarar Widad to lallai zasu ɓata, ranar kwana na bakwai da tafiyar Yusuf, Hajiya Halima se sintiri take tsakanin part ɗinta da babban falo, Widad kam ko a jikin ta shagalin ta kawai take.
Yusuf ne yayi Sallama a falon, Hajiya Halima na zaune a falon tun safe ta kasa sukuni seda Yusuf yazo.
Abunda ya É—aurewa Yusuf kai be wuce yadda yau ta sakar masa fuska ta amsa masa gaisuwar cikin mutunci ba.
Zeyi magana kenan yaji ƙamshin turaren Widad, wanda ya alamta masa ta fito falon, waiwayawa yayi ita ɗin ce kuwa cikin shigarta ta ƙananan kaya kamar yadda ta saba, bakin ta ɗauke da chew gum tana taunawa tare da lumshe ido, a hankali tana taku me ɗaukar hankali ta tako ta ƙarasa shigowa falon, ta samu guri ta zauna ba tare da tace komai ba.
Yusuf ya tako zuwa gaban kujerar da take zaune ya durƙusa a gabanta ze fara magana, katse shi tayi ta hanyar yi masa alama da hannun ta na ya zauna akan kujerar dake kusa da wadda take kai.
Seda ya É—aga ido ya kalli Hajiya Halima sannan ya tashi ya zauna yaceÂ
"Ranki ya daɗe ga saƙon"
Ya miƙa mata ledar wayoyin da receipt ɗinsu da kuma ATM card ɗin. Tasa hannu ta karɓa, ta buɗe ta ciro wayoyin manya masu kyau, ta jujjuya su a hannunta sannan ta kalli Yusuf tace "can i have your phone?"
Kallon ta yayi, tare da yin sororo
"are you deaf?" ta tambaye shi tana tsare shi da ido.
Ciro wayarsa yayi daga aljihu ya miƙa mata, Android phone ce, dukda ba wata me tsada bace Amma hoton sane da Ummansa akan wallpaper ɗin wayar, seda tayi nazarin hoton na wasu seconds sannan ta buɗe wayar Yusuf ta cire sim cards ɗinsa da memory ta haɗa da sabuwar waya guda ɗaya, da tsohuwar wayarsa ta bashi sannan tace
"i want see you tomorrow by 9:am Insha Allah, you will get your salary alert today, you can leave"
"amma ranki ya daÉ—e, wannan wayar ai tayi min girma, kuma..."
Ai ko kallon inda yake bata sake yiba ta miƙe ta nufi part ɗin ta.
Gaba ɗaya hankalin Hajiya Halima akan Yusuf yake, Yusuf ya fita daga falon, ganin bashi da wani aikin da zeyi ya sashi ya ƙudure tafiya gida, yana ta ƙara jinjina kyautar wayar da Widad ta bashi.
Yayiwa su Nura Sallama ya fice ba tare da ya gaya musu abunda Widad ta bashi ba, yana cikin tafiya kafin ya kai ƙarshen layin aka sha gaban sa da mota, tsayawa yayi cak yaga waye wannan.
Ramla ce ta fito daga motar tana masa wani irin kallo, ta kalle shi a yatsine tace "Nasan zakayi mamakin ganina anan, saboda bakamata mace kamarni ta tsaya tana ɓata yawunta akan talaka mutum maƙasƙanci kamar ka ba, sedai ita kasuwar buƙata idan ta taso tamkar guguwa take bata da shamaki, magana nake so muyi da kai me mahimmanci, wadda zata amfaneka, idan ba zaka damu ba ina so ka shiga mota muyi magana"
"talakan mutum maƙasƙanci a gurin ki, amma wataƙila me matsayi a gurin Allah be cancanci ya shiga motar mace me girman kai da tinƙaho ko ince tagumi da haɓar wani ba, bana buƙatar dukkan wani abun Amfani da ze taso daga gare ki komai mahimmancin sa kuwa, a gurin Allah nake nema dan haka ki bar abunki koma menene kuma komai amfaninsa"
"karkayiwa kanka gaggawa, ƙarshe kazo kana cizon yatsa, da da nasanin fatali da abunda ya tunkaro ka kayi masa shinge da riskarka saboda girman kai na banza, talakan mutum me dakakkiya zuciya irinka, zuciyarsa cike take buƙatar samun damarmaki, dama irin wadda kowa ke lalube a duhu ko a sarari, katsam se gashi ka sameta a sarari, Amma ka kasa ƙafa kai fatali da ita, me yasa kayi hakan? "
"lokaci abune me mahimmanci a gurina, ina bashi mahimmanci fiye da yadda kike tunani, zefi kyau ki taƙaita wannan dogon surutan naki marasa amfani, a cikin taƙaitattun kalmomi kimin bayani gwari gwari kamar yadda Uwargida Widad keyi, hakan zefi min sauƙi, kuma ze adana lokacin mu".
Wani kallon banza ta watsa masa sannan tace "ko Uwargida ko ubangida wannan kai ta shafa, ni daban ita daban, dama ta sameka amma ka watsar da ita a yadda kake gaka matashi har matashi, kai dai ba muni ba kuma ba nakasa ba, a wannan shekarun naka da ƙirar da Allah yayi maka kamata yayi ace kana wani ɗan ƙwalisa meji da kansa, katsam sega shi ka ƙare a direba, direban ma maƙasƙanci, kana tuƙa ƙaramar Yarinya tana cin zarafinka yadda taso, bata ganin gjrmanka da aikin da kake mata, da kasan maƙudan kuɗaɗen dake cikin Account ɗin nan da tabbas baka dawo gidan nan ba, dan da kai da talauci har gaban Abada, ba kaiba har 'ya'yan ka da jikokin ka ba zasuyi talauci ba, sedai kash garin yin gwaninta kayiwa kanka mugunta"
Yusuf yace "har yanzu jira nake ki faÉ—i abunda kike tafe dashi, na gaji da sauraren wannan salon maganar taki me tafiyar kura, kiyi gaba kiyi baya kamar kema baki yadda da kanki ba"
"Babu batun rashin yadda da kai sedai ina so muyi tarayya gurin temakon juna ne, ina son ka gayamin password ɗin Widad ne na banki, nayi maka Alƙawarin samun wani gwagwaɓan sakamako indai kayi abunda nace, hakan ze zama madadin wannan shiritar da kayi nayin wasarere da damar daka samu, kuma ze baka damar samun 'yantuwa daga wannan aikin dakake ƙarƙashin wannan Yarinyar me Baƙar Aƙida"
Wani irin kallo Yusuf yayi mata sannan yace
"dukda kasancewa ta talaka maƙasƙanci kamar yadda kuke kirana, Yusuf yafi ƙarfin karɓar abunda zaku bashi saboda wannan baƙin aikin da kuke so inyi, ku tara dukiya da guminku seku yi barazana da ita ko tinƙaho, Bana danasanin aiki na ƙarƙashin Widad, duk inda tayi faɗa ko tsiwa to tabbas an mata ba daidai bane, shiyasa komai tayi take birgeni, kasancewata meyi mata aiki be sa naji cewar ni maƙasƙanci bane, kasancewata me aiki a ƙarƙashinta na sani ƙara samun ilimin rayuwa, dan haka kece maƙasƙanciya da kika ƙallafa rai akan abunda ba naki ba, ni talaka ne me wadatar zuci, dukiyar Widad bata isa ta yanken talauci ba"