Sashe 7
Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Alhaji Bulama yace "A'a daughter sama miki masu tsaron ki yana da mahimmanci, musamman tunda kin san amfanin hakan a tare da ke"
"Bana buƙatar kowa a tare da ni, bana buƙatar saka rayuwar kowa a hatsari, ban yadda da kowa ba dan haka bana buƙatar su"
Alhaji Bulama ya jinjina kai yace
"Amma daughter kin san likita ya hana ki wannan ɗabi'ar kaɗaice kan naki, rayuwa ba zata taɓa yuwuwa a ce kina gudun mutane ba, ya kamata ki samu kiyi aure zaki samu nutsuwa, da kuma farinciki zaki rage kaɗaicin nan"
Karon farko da Yusuf yaga dariya a fuskar ta, ba ƙaramin kyau tayi ba da tayi Dariya ta wani jinjina kai cike da rainin hankali tace
"Alhaji Bulama kenan, an gaya maka rayuwar kaÉ—aicin da nakeyi tana damuna ne? Karnuka na da maguna suna É—ebe min kewa sosai fiye da yadda mutane zasu yi min, tunda nasan sun baza su cutar dani ba"
Ta miƙe tsaye tsam ta kalli Alhaji Bulama ta haɗe rai kaman ba ita ta gama dariya ba tace
"Ka cire wa zuciyar ka cewar ni widad zanyi Aure, ban yadda in zauna a ƙarƙashin wani ba yana juyani yadda yake so ba, in anyi Aure ana neman Aljanna ne, ni kuma idan nayi Aure sedai Rahamar Allah ta shigar dani Aljannah, ba dan zanyi wa wanda nake tare da shi biyayya ba, na faɗa bazan zauna ƙarƙashin wani ba, babu wani farinciki da'ake a tsinta a Aure, babu komai cikin rayuwar aure se takura da matsaloli, NO MARRIAGE IN MY POLICY!!! Rayuwa ta da nake nika ɗai ta fiye min bazan gayyato wa kaina matsala ba bayan wadda nake ciki"
Ba Alhaji Bulama ba hatta Yusuf maganganun Widad sun É—aure masa kai, ita kam wannan wace irin zuciya ce da ita haka?
Inda motar su take ta nufa, hakan yasa Yusuf bin ta da sauri ya riga ta ƙara sawa inda motar take ya buɗe mata.
Suna tafe yana lura da ita, ranta a ɓace yake sosai, haka yayi tuƙi a hankali koda suka je gida part ɗin ta ta nufa ba tare da ta kula kowa ba.
Yusuf kam rasa abunyi yayi, ita ba tace ta sallame shi ba ko A'a, ga mukullin mota bata karɓa ba.
Bayan ya kulle motar Isa ya nufoshi yana murmushi yana zuwa yace
"har kun dawo kenan?"
"Eh min dawo malam Isa"
"to yaya, fatan dai bata maka halin ba?"
Yusuf yayi murmushi yace "niba abunda tayi min, ni yanzu damuwa ta ban sani ba ko ta sallameni ba tace min komai ba, ina son tafiya gida ne"
Isa yace "kaje ina? ai zama zakayi setace ta sallame ka"
Harar Isa Yusuf yayi yace
"shikenan ni bani da Abunyi na kaita inda zan kaita meya rage banda in tafi tawa sabgar, mahaifiya ta Nason ganina dan haka bazan zauna ba"
Yana gama maganar ya nufi ƙofar shiga cikin gidan, yana jin Isa yana kiransa amma yai masa banza.
Yana shiga yayi karo da Amal ta taho da sauri zata fkta.
Tana ganin sa ta tsaya tana ajiyar zuciya, taji wani farinciki na ratsa zuciyar ta Yusuf yace "barka da rana"
"Yawwa barka ya kake ya aikin?"
"Alhamdilillah, ga key ɗin mota nan bata karɓa ba ta tafi, ina son zan tafi gida ne inga mahaifiya ta"
Ya miƙawa Amal, be jira me zata ce ba yai waje abun sa.
Jinjina kai Amal tayi tace "lallai wannan besan wacece Widad ba, da alama shima kansa yana É—an rawa"
Babban abunda ya bata haushi irin yadda be tsaya ko gaisawar kirki sunyi ba.
Koda Yusuf ya koma gida ya sha tambayoyi a gurin Ummansa, seda ya tabattar mata da babu wata matsala sannan hankalin ta ya kwanta.
Tunda ya shiga ɗakinsa yake saƙawa yana warwarewa, abubuwa da yawa sun bashi mamaki yana da tarin tambayoyin da besan me bashi amsar su ba, Amma kusan akwai alamar tambaya akan dukkanin iyalan gidan akwai wani ɓoyayyen abu da kowa yake ɓoyewa a ransa.
"Amma me yasa Widad ta zaɓi rayuwar kaɗaici akan rayuwa da mutane? Me yasa tayi wa Aure mummunar fahimta haka? Me yasa kowa yake biyayya ga Umarnin ta abunda take so, ko da kuwa hakan na nufin ɓacin ran mutane ne?"
Bashi da Amsar tambayoyin nan, Shi ze nemowa kansa amsoshin tambayoyin.
Widad tana kan gadon ta ta ƙurawa sama ido, Hawaye na bin gefen idon ta, Mahaifin ta yayi Sallama a ɗakinta, tana jinsa amma tayi masa shiru, ta miƙe zaune a hankali, ya ƙaraso gefen gadon ta ya zauna ya kalli idon ta yace
"daughter ya akayi ne? Meke faruwa? Abbanki ya gayamin ko gidansa baki shiga ba iyakarki harabar gidan, daughter me yasa?"
"Bana son hayaniya ne, shiyasa na tsaya kawai a harabar gidan" ta bashi Amsa
Alhaji Nasir yayi ajiyar zuciya yace
"Alhaji Bulama ya gayamin yadda kuka yi, Lovely bamu yanke shawarar batun yi miki aure ba sedan na gaji da ganin halin dake ciki, Widad zuciya ta na shiga ƙunci da irin wannan rayuwar da kike yi, kin san larura dake damunki, likita ya hana ki kaɗaicewa, idan kika cigaba a haka fa ze cigaba da taɓa ƙwaƙwalwar ki, dan Allah daughter ki amince da roƙona, kiyi Aure ina son ganin farincikin ki, ko baki yadda da kowa ba, idan dai zaki buɗe ido kiga 'ya' yanki da mijinki zakiji daɗi sosai, dan Allah Widad bani da kowa yanzu seke, se kuma Aminina Bukar Bulama, naso Inkuma samun yara bayan ke, Allah be bani ba, zanji daɗi idan naga 'ya' yanki, please Widad help your Dad, nasan bana tunanin akwai wanda kika tsayar kike so, Amma nida Bulama mun yanke shawarar zaɓa miki mijin da zakiyi Alfahari da shi, wanda ze nuna miki so ya kula dake ko bayan raina, Widad a yau idan na faɗi na mutu bayan Alhaji Bulama bana tunanin Akwai wanda ze kulamin da Rayuwar ki, sannan kinsan a haɗarin da muke daga ni har ke, please Widad ki Amincewa batun Auren nan, am sure if you got true love you will never regret been married, Akwai Soyayya da tausayi a cikin rayuwa da wanda yake son ka, na tabattar da Aure ze wanke miki dukkanin wani pain da yake ranki"
Tunda ta ƙura masa ido ko ƙyaftawa ba tayi, seda ta bari ya gama, ta miƙe tsaye ta fice ta bar masa ɗakin ba tare da tace komai ba.
Alhaji Nasir ya jinjina kai, babu alamar Nasara, Amma ya yanke wa zuciyar sa ze cigaba da lallaɓata yana bin kanta, dan babu wata mafita da ta rage masa se Amincewa da shawarar Alhaji Bulama.
A fili yace "Wannan karon ke zakiyi biyayya ga unarnina daughter, duk wannan abun inayi ne saboda ke"
Widad kam gaba ɗaya maganganun mahaifinta haushi suka bata, kaman korarriya haka ta sakko daga kan bene, ta samu corridor ta tsaya tana zancen zuci, "wai Aure, waya gaya musu akwai Aure a tsarin Rayuwar ta? Taɓɗijan inyi Aure in zauna a ƙarƙashin wani yana juya ni yadda yake so? Ko kuma a haɗa kai da shi a cutar dani, kaman yanda yake ɗabi'ar mutane ne cin amanar wanda ya yadda da su, idan har Akwai mutane masu amana da suka rage a doron ƙasa to sunyi nisa da duniyar da ni Widad nake ciki, waima waye ake cewa za'a haɗa da shi ne Aure? Idan kuma ya zamana yana ɗaya daga cikin mutanen da nake nema fa, hakan yana nufin in masa Alfarma ko in ɗaga masa ƙafa?
A fili tace
"Baze yuwu ba wallahi, ba wani Aure da zanyi, what is their in marriage apart from pains!, hurting each other!, tensions!, regrets and restriction of rights,!! No Impossible i want free life, i can't live under someone's control, i better live alone and die alone than to got married to irresponsible man of now a day's, bazanyi Aure ba, idan har Soyayya da shaƙuwa basa hana ɗan Adam ya cutar da ɗan uwan sa, to tabbas Love doesn't exist is just an imagination, love does not exist talk less of true love, So shike sa ayi Aure, kuma yadda ce ke kawo so ban yadda da kowa ba, Daddy Bulama kayi min katsalandan bisa ga kawo wannan shawarar da ɗaya take da ƙarasa gurgunta rayuwa ta" hawaye ne ya wanke mata fuska sharkaf se ajiyar zuciya take yayin da take maganar.
Ramla da tazo wucewa ta tsaya taji surutan da Widad take yi, ta jinjina kai a ranta tace "to Aure kuma? Waye ze auri wannan Jarababbiyar? Kuma mahaukaciya? Anya Mummy ta san zancen nan kuwa?
Widad kam ji tayi zuciyar ta tana wani irin raÉ—aÉ—i, ta fito harabar gidan da sauri kanta ko É—an kwali babu, dan gaba É—aya ji tayi kaman tana cikin wuta dole ta fita dan ta samu sassauci,
Tana fitowa harabar gidan ta nufi inda Isa yake tace
"ina direban nan yake, yazo ya fita dani ya bar arear nan dani"
Isa ya kalleta ya kalli kayan jikin ta, mini skirt ne a jikin ta se wata riga armless, gashin kanta a baje kaman ta zare, Isa ya ɗan ƙare mata kallo, a ransa yace "Masha Allah, Allah ya yi halitta anan" yace
"Ranki ya daÉ—e a hakan za'a fita dake?"
Kallon da yake mata ne da tambayar da ya tsareta da shi, yasa ta ƙara fusata ba zato ba tsammani Isa yaji saukar lafiyayyen mari a fuskar sa.
Gigicewa yayi ya dafe kuncin sa yace "ranki ya daÉ—e ya tafi tun É—azu, nace ya tsaya amma yace baze tsaya ba yana da uzuri"
Ƙanƙance ido tayi ta dubi Isa, a hankali tayi ƙasa sa muryar ta tace
"ɗan uban waye shi da ze saka hannu akan dukkan sharuɗai na, kuma yau da ya fara min aiki har ya fara saɓamin doka?"
Shiru Isa yayi yana sake shafa kumatunsa dan bashi da amsar da ze bata