← Book details Akidata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 82

Sashe 66

Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Guri ta zauna ta janye rigar jikinta, ta nuna masa cinyarta, fara tas fiye da fuskarta, sedai tayi ja saboda cizon cinnaka, banda wanda ya gasa mata a hannu.

Yusuf yace  "Sannu bari in tambayi gwaggo inda zaitun ta bani ki shafa"
Zumɓura baki tayi tace  "ni banyi wanka ba"

Haka ya karɓo ruwa tayi wanka, sannan ta dawo ɗakin, ya bata guri ta sa kaya, ya ɗakko zaitun ta zauna ya shafa mata a na hannun, ya fara shafa mata a ƙafarta ne a hankali, haka kurum taji jikinta wani iri, kawai seji yayi ta doke hannunsa tace
"meye haka?"

"Me kuma nayi miki?"

"ban sani ba" ta bashi amsa tare da miƙewa, ɗan sunkuyar da kai yayi yana murmushi.

Daga Asibitin gurin Alhaji Musa Saleh ya wuce, yaje ya sames hi a office É—insa.
Saleh yace  "Ranka ya daɗe kwana biyu bani da lafiya, ko ƙofar ɗaki bana iya fitowa, shiyasa kwana biyu bana zuwa"

Alhaji Haruna yace "Akwai damuwa fa, ko Kasan me Adda ya cemin yarinyar nan sun gudu"

A razane Saleh yace "wace irin maganar banzace wannan? Kamarya sun gudu?"

"Nima dai abunda na gani kenan, gaba É—aya sun mayar mana da aiki baya, yanzu Bukar yace ko a raye ko'a mace anemosu a kashesu kar Asirinmu ya tonu, sannan kaje ka bincika mana wa'aka bawa aikin binciken nan a cikin jam'ian tsaro?"

Saleh yace "Amma fa wani hanzari ba gudu ba, ina kyautata zaton me Adda yana sane ya sake su, wataƙila tace zata bashi kuɗine koma ta ninka masa abunda kuka bashi, shine ya sake su, in bahaka ba ta yaya zasu iya tserewa? Kokuma a cikinku ne wani ya zagaya ya haɗa baki dashi, idan an karɓo abun a gaya masa shikaɗai ba"

Shiru Alhaji Haruna yayi yace "Biri yayi kama da mutum, kuma fa Saleh kayi magana, tabbas dan nasan zata iya, kuma babu Abunda me Adda baze iya akan kuÉ—i ba"

Jinjina mara adadi ga ɗumbin masoya littafin AƘIDATA, niba abunda zance muku se godiya Allah ya bar ƙauna, ga dogon page nan, nima inga dogon sharhi, ga link ɗin telegram nan a ƙasa

https://t.me/joinchat/SYIfEaoQo_JlNDM0

Share, share and share please 🙏 🙏 🙏
Domin gyara sharhi, ko shawara
Ayshercool
07063065680

                       _*AƘIDATA*_
       

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA _
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

NOT EDITED

ELEGANT ONLINE WRITER'S

                         PART1
                                Page 34_35

Saleh ya cigaba da ziga Alhaji Haruna, akan lallai yayi bincike, dan zata iya yuwuwa abokan harƙallaesa ne wani yasa a karɓo masa abun hannun Widad, shiyasa me Adda yace masa sun gudu.

Alhaji Haruna yace "Nagode sosai Saleh, Insha Allah zanyi tunani akai"

Saleh yace "bakomai yallaɓai, bari in ɗanje gida in huta, kasan bana jin daɗin jikin nan nawa"

Alhaji Haruna yace  "shikenan Allah ya sawwake"

Saleh ya tashi ya tafi

Sakina ce fuskarta É—auke sa damuwa ta shiga ofishin Suleiman, Suleiman yace "Sakina lafiya kuwa?"

Sakina tace "Yallaɓai akwai damuwa, yau sati biyu sa sace Yusuf amma har yanzu babu wani kyakkyawan rahoto, da yake nuna ana bincike akan lamarin nan, anya anyi adalci kuwa duba da yadda Yusuf yake bada gudunmuwa akan harkar tsaro, amma ace shi wannan iftila'in ya faɗa masa amma babu wani yunƙuri da'ake gurin ceto shi, idan ya rasa ransa fa? "  ta ƙarasa maganar kamar zata yi kuka.

Suleiman yace "look Sakina, kiyi wani tunani kodan Albarkacin 'yar babban attajirin da' aka sace su tare, yaci ace an maida hankali akan nemansu, amma har yanzu shiru, shikansa Daulan yana gadon Asibiti a kwance, na kai ƙorafi akan abari muma mu gudanar da namu binciken, amma daga sama aka bani umarnin cewar ba'a samu ba, ana gudanar da bincike akan al'amarin, babu wani abu da zamu iya banda muyi musu Addu'a "

Sakina tace " shikenan Yallaɓai, ubangiji Allah ya kuɓutar dasu lafiya, bari in koma kan aikina"

"Shikenan Sakina, Allah ya taimaka"

Sakina na tafiya, telephone ɗin gaban Suleiman ta fara ringing, ya sa hannu ya ɗaga, jin muryar wanda ya kira shin yasa shi miƙewa tsaye cikin girmamawa yana amsa wayar.

"A cikin ma'aikatanka wa'aka saka akan binciken masu bibiyar Alhaji Nasir Daula?"

Suleiman yace  "Yallaɓai Yusuf ne, wanda aka ƙarawa matsayi kwanan nan"

"A gaggauta kammala binciken nan, a miƙo bayanan binciken nan headquarter"

Suleiman yace "Ok Sir"

Yusuf ya kalli Widad da tayi kicin kicin da fuska yace "ga kayan nan na wankesu, sun bushe ma gaba É—aya"

Tasa hannu ta ciro kayan daga bokiti, taga kayan a haÉ—e dana Yusuf, kwashe nata tayi ta zube masa nasa a gurin, Yusuf yasa hannu ya kwashe ya zuba a jakarsa.

Ya kalleta yace "kinci Abinci kuwa?"

"ni banci wani Abinci ba, kaga fa abunda aka kawo"

Kwano ta miƙa masa, yasa hannu ya buɗe dafaffiyar masarace a ciki da ɓawonta da komai, Yusuf yace "to me yasa baki ciba?"

"ta ina zanci ? Kawai se in kama cin masara, ni ban taɓa ganin anci masara ba, nidai kawai nasan Abinci akeyi da ita, amma ba'aci"

Yusuf yace "ikon Allah, wannan wace irin hausa ce? Waye ya gaya miki ba'a cin masara"

Ya zauna ya ɓare masarar tsaf, ya ɗaurayeta, yace "nasan kece baki taɓa ciba, amma ana cin masara dafaffiya ko gasashiya, ci kiji"

Ɗauke kai tayi taƙi karɓa, Yusuf kuwa yasa masara a gaba ya fara ci, zuba masa ido tayi tana kallon ikon Allah, yana nufin itama haka zata ɗau masarar ta dinga wannan kokawar haka sekace wata saniya.

Plate ya ɗakko ya shiga ɓanɓarowa yana tara mata a plate yace "gashi na ciro miki ɗauki kici"

Ba kunya tasa hannu ta fara tsinta tana kaiwa bakinta, dan bilhaƙƙi ita bata taɓa ganin ana cin masara a haka ba, amma kuma tabbas da daɗi, ya dinga cirowa yana tara mata tana tsinta tana ci, kamar wata 'yar yaye, cikin ikon Allah a haka kuma ta ƙoshi.

Shiru tayi ta tuna lokacin da sukaje restaurant cin Abinci, Yusuf yake gayamata Naira ɗarin cin Abinci tana gagarar wasu, take ganin kamar ƙarya yake, se gashi yanzu ta gani da idonta, da wanine ya bata labarin ana dafa masara aci a matsayin Abinci zata ce ƙaryane dan bata taɓa gani ba.

Can Yusuf yace "inda ƙwaron ya cijeki ya dena zafin?"

Ta gyaÉ—a masa kai alamar eh, yace "hannun da'aka harbe ki fa?"

"yayi sauƙi, ina iya motsa hannun sosai, sedai idan ma bige ne nake jin zafin"

Yusuf yace "masha Allah, Allah ya ƙara miki ingantacciyar lafiya"

Shiru tayi kamar ba taji ba, Yusuf yace "Addu'ar ma bakya so?"

Shiru tayi masa tana sake ƙarewa roofing ɗin ɗakin kallo, tana son gane dame akayi shi.

Yusuf yace "me kike kallone?"

Widad tace  "kai subhanallah, wallahi ka dameni da surutu haba, sekace waccan matar me haƙora"

Yusuf yace "to shikenan na dena gimbiyata"

Ɗagowa tayi ta masa wani irin kallo, ba shiri ya miƙe yayi waje ya bar mata ɗakin yana murmushi.

Wasa2 Ramlah ta ganewa shaye2, bata salla se wajen ƙarfe takwas na safe, da ta idar zata ɗakko Coca-Cola tasha, seta kai ƙarfe biyun rana tana bacci.

Yanzuma Amal ce ta shiga É—akin Ramlah, ta tarar da ita tana girgiza jarkar Coca-Cola.

Amal tace  "Ramlah, wai me yake damunki ne haka? Wane irin coc ne kike sha ba yau ba gobe ga shegen bacci kamae kin haɗiyi kasa"

Ramlah ta kalleta tace "kina da matsala da hakanne?"

"ba wai batun ina da matsala da hakan bane, sedai cewa kina ganganci da rayuwar ki, baccin da kike ya wuce ƙa'ida, kuma wannan coc da kike sha yayi yawa sosai, nifa na fara zargin wani abu kike sha a cikin coc ɗin nan"

"Ke Amal! Ki kiyayeni, dalla wuce ki barmin É—aki, ina ruwanki dani idanma wani abun nake sha?"

Amal tace "shawara ce nake baki, amma

" wallahi Amal in baki barmin ɗaki ba sena miki rashin mutunci, Dalla ƙara gaba kije kiji da kanki"

Amal tace "shikenan Kije ki ƙarata" ta fito daga ɗakin.

Yanzu kusan kullum se Ramlah ta fita, ko tare da Fahad ko ita kaɗai, kuma Hajiya Halima bata taɓa yi mata magana akan hakan ba.

Anwar kam ya tattara yasa musu ido, ya maida hankali akan kula da Alhaji Nasir, kwata kwata ya dena shiga sabgarsu ma.

Abubuwa suka fara cakuɗewa su Alhaji Musa, suka kuma hayar wasu 'yan ta' addan domin a nemo musu  su Me Adda, yayin da Alhaji Haruna ya keta tunani akan maganar da Saleh ya gaya masa game da tserewar Su Yusuf.

Meeting suke akai akai akan yadda zasu ɓullowa al'amarin,
Alhaji Munir yace  "tabbas idan har yaran nan suka kuɓuta suka dawo Asirinmu ze iya tonuwa"

Alhaji Musa yace "yakamata ku kwantar da hankalinku, babu yadda za'ayi Asirinmu ya tonu, yanzu naga Likitan nan yana aikin da muka sashi,  dan yanzu baya gane waye akansa sam"

Alhaji Haruna yace "hakane Daula ya zama abun tausayi, talakawan da yake fafutuka akansu, an hana kowa zuwa inda yake, manyan ƙasar nan ma kowa yayi watsi da lamarinsa, yanzu haka nasa Jam'ian tsaro su hana kowa shiga inda yake, se ɗan matar nan tasa, shi kuma wannan soko ne, ba abunda yake ganewa, shekaranjiya wasu baƙin turawa sunzo duba shi, amma an hana su ganinsa ance yana ƙarƙashin kulawar likita baza'a ganshi ba"
Chapter 66 · 0% Book details