← Book details Akidata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 82

Sashe 50

Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yusuf ya ɗakko tsohon layinsa yasa a waya, sedai yana sakawa yaga saƙonnin Nurat na shigowa, messages ɗin ya shiga dubawa ɗaya bayan ɗaya sedai yana cikin dubawar kiran Nurat ya shigo wayar, kamar kar ya ɗaga amma ya ɗaga yace

"Assalamu Alaikum"

Wata nannauyar ajiyar zuciya Nurat tayi tace "Aboki anya duniya da gaskiya, ka manta dani ko?"

"haba ƙawata, ya zan manta dake light, wayata ce ta lalace shiyasa"

"Allah sarki, duk hankalina ya tashi na zata wani abun ne ya same ka"

"ba abunda ya sameni light fatan kina lafiya"

"Lafiya ƙalau, amma ina son ganinka ne Aboki"

"me zaki bani in kin ganni?"

"magana nake so muyi"

"muyi ta a waya mana light, abubuwa sunmin yawa sosai"

Ajiyar zuciya tayi tace  "zefi kyau dai in ganka, mahaifina ne naga yana harka da wasu irin mutane wanda da ganinsu kaga marasa kirki, ga yawan zuwa gidanmu dasu Alhaji Musa suke yi, kace idan naji wani abu wanda zesa a cutar da Widad in gaya maka, amma dai ban san meke faruwa ba"

Gaban Yusuf ne ya faɗi cikin sauri yace  "a ina zamu haɗune Nurat?"

"nace ina son ganinka kace ba lokaci, amma da yake nayi maganar Widad shine kace zaka zo"

"yi haƙuri Light"

Nurat tace "sedai kazo gidanmu, babana yana gari baze yuwu mu haÉ—u ba"

"shikenan insha Allah, zan san yadda zanyi mu haÉ—u"

"Aboki baka gayamin sunanka ba fa"

"ƙawa zan gaya miki very soon insha Allah, dan Allah in an samu wani update ɗin ki sanar dani, sannan akwai ajiyata a wayarki ki kula sosai light"

"Ajiya kuma? Wace irin Ajiya?"

Murmushi Yusuf yayi yace
"Light, light tabbas ina da Ajiya a gurinki, dan Allah ki kula da kanki da kuma wayarki, idaan nazo zan nuna miki ajiyar"

"shikenan Aboki, amma dan Allah ka dena rufe wayarka"

"to shikenan insha Allah"

Tunda Yusuf yaji labarin nan hankalinsa ya tashi, ya shiga tunanin ya Widad take, ba shiri ya miƙe ya shiga shiryawa.
Ya fito tsakar gida, Umma ta kalle shi tace "se ina kuma?"

"zanje gidansu Widad ne?"

"yau kuma, to Adawo lafiya"

Ya amsa da Allah yasa.

Yana zuwa gidan Isa yace "Yusuf ina ka shigane ka dena zuwa gidan nan kusan kwana tara, me gida yasa an kiraka a waya shima ya kira amma layinka baya shiga, ka dena zuwa ba tare da wani dalili ba"

Bece komai ba ya shiga cikin gidan da sauri, yana zuwa ɓangarenta ya nufa ya tarar bata nan, ya fito babban falo yaga Amal.

"Amal dan Allah ina Widad ne"

Banza tayi masa taƙi ce masa komai Anwar ne ya shigo hannunsa riƙe da leda yana ganin Yusuf yace  "bawan Allah kwana da kwanaki ake nemanka baka zuwa, daga samun saɓani ka ɗauke ƙafa Uwar ɗakinka na neman rasa ranta.

Ba ƙaramin razana Yusuf yayi ba yace " tana ina? "

Anwar yace " tana ɓangaren Daddy "

Da sauri Yusuf ya nufi sashin na Alhaji Nasir yana shiga ya tarar da Widad a zaune Daddy yana ta aikin rarrashi tace Abinci amma taƙi se kuka take.

Daddy na ganin Yusuf yace  "Alhamdilillah, Yusuf ashe zaka dawo saura ƙiris in fita nemanka da kaina"

Yusuf seda ya firgita Widad ta zabge gaba ɗaya, ta rame sosai ta ƙara haske idanunta a kumbure, juyawa tayi gaba ɗaya taƙi kallon inda Yusuf yake.

Yusuf yace  "Yallaɓai bata da lafiya ne?"

"ciwonta ne ya tashi, ta fara samun sauƙi naga baka zuwa na tambaya, tace min rigima kukayi ka dena zuwa, na mata faɗa naga ta sake shiga damuwa ga kuma batun Auren nan, ta dena cin Abinci ko magana taƙiyi, se kuka munyi magana da wani abokina a Abuja yace akwai babban likitan Ƙwaƙwalwa a international Hospital yana zuwa ranar Talata, idan ba zaka damu ba dan Allah ina so ka temakamin ku tafi tare, na yadda da kai Yusuf nasan ba zaka cutar dani ko 'yata ba, tafiyar tazo daidai da taronmu na shekara idan banje ba akwai matsala, seku sauka a gidan Abokin nawa kuje Asibitin daga nan duk abunda kukayi kuka gama ranar Monday jirginta ze ɗaga Zuwa England, ta koma taje ta ɗan huta, kafin in san me ya kamata inyi, naga tafi samun nutsuwa a can"

Jiki a sanyaye Yusuf yace " Shikenan an fasa Auren nata?"

"eh munyi magana da Bulama, mun yanke shawarar ɗaga Auren se ta samu sauƙi, idan babu matsala baka da wani abunda zakayi ban takura ka ba seku tafi"

"Shikenan Yallaɓai zanje in shirya insha Allah, Allah ya bata lafiya ko nan da birnin Sin ne zanje insha Allah "

"to shikenan masha Allah, nagode sosai Allah yayi Albarka ya jiƙan mahaifa, tafiyar safe nake son kuyi dan kuje da wuri, jibi in Allah ya kaimu zamu kwana a gidan gona, da an idar da sallar Asuba seku tafi, nace kubi jirgi tace A'a"

"Ameen ya Allah Bakomai Yallaɓai, zanje in shirya insha Allah"

Yusuf a ransa yace 'dole inje wannan tafiya, duk cikin aikina ne'

Kallon Widad yake amma sam taƙi kallon inda Yusuf yake.

Miƙewa tayi ta bar ɗakin daddyn gaba ɗaya.

Alhaji Nasir yace  "Yusuf tabbas nasan kana da haƙuri, shiyasa kuka daɗe tare da 'yata, kana da matuƙar tasiri a rayuwarta ko yanzu ka canza mata abubuwa da dama na rayuwarta nagode da wannan namijin ƙoƙari da sadaukarwa ga' yata"

"bakomai Yallaɓai Allah yasa a dace, Allah ya bata lafiya"

********************* **************

"Masha Allah, komai yana tafiya yadda muka tsara, komai zezo ƙarshe koda tsiya koda tsiya tsiya se mun mallaki abunda muke so" cewar Alhaji Munir

Alhaji Musa ya kwashe da dariya yace  "tabbas haka maganar ka take, nayiwa yaran nan jan kunne yadda yakamata baza'a samu matsala ba Saleh yace ze sanar damu duk wani abu da ake ciki"

Alhaji Munir yace  "ƙunrunƙus, yayin da muka ɗauke hankalinsa ta ɓangare ɗaya, ɓangare ɗaya kuma baze halarci taron kasuwanci ba"

Suka ƙyalƙyale da dariya gaba ɗaya.

(RASHIN SANI......)

Share and share please 🙏 🙏 🙏 🙏

Domin gyara sharhi, ko shawara
Ayshercool
07063065680

                       _*AƘIDATA*_
       

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

ELEGANT ONLINE WRITER'S

                         PART1
                                Page 22_23

Yusuf yaso yabi bayan Widad dan ya duba ta, amma yasan halinta tsaf zata yanƙwanashi, dan haka ya yanke shawarar tafiya kawai.

Office ya wuce kai tsaye, ya tarar da Suleiman yana shirin fita suka gaisa Suleiman yace  "Yusuf akwai wani update ne"?

"Eh yallaɓai gurinka ma nazo"

"shikenan mu koma ciki" suka juya zuwa cikin office É—in gaba É—ayansu.

Nan Yusuf ya zayyanewa Oga Suleiman komai da yake wakana, akan harkar binciken da batun tafiyar da za suyi, da abunda Nurat ta sanar dashi.

Suleiman yace  "Amma baka ganin mu haɗaka da abokan aiki, suyi muku rakiya a wata motar gudun samun matsala?"

Yusuf yace  "Insha Allah babu wata matsala Oga, kasan a slide mistake yarinyar nan zata iya ganewa nikuma bana son ta gane komai a yanzu har bincikenmu ya kammala".

"shikenan Yusuf Allah yayi mana jagora, Insha Allah zakayi Nasara ana ta samun haske akan lamarin, bari ni zan fita ne yanzu zanje headquarter"

"to shikenan Yallaɓai a sauka lafiya"

Bayan tafiyar Suleiman Yusuf ya fito yana shirin tafiya, Suka haɗu da Sakina, Sakina tace 

"Ashe yau ka samu ka shigo, ban samu na maka murnar ƙarin matsayi ba, Allah ya tayaka riƙo"

Yusuf yace  "Ameen nagode"

"sannan ina tayaka murnar rabuwa da mugun aboki wato Abbas"

Cikin mamaki da rashin fahimta yace "kamar yaya?"

"Kamar yadda na gaya maka, Allah ne ya dube ka ya rabaku, a baya nasan koda na faɗa ba zaka yadda ba, yanzunma ban sa ran ka yadda ba amma wataran zaka ce na gaya maka, Allah ya bada sa'a ya tayaka riƙo"

Tayi gaba ta bar Yusuf a gurin yayinda ya bita da kallo.

Da Yusuf ya koma gida yayiwa Umma bayanin tafiyar da zasu yi ya raka Widad, da farko taƙi yadda tace sam bata san zance  ba.

Yusuf yace  "haba Umma, ya za'ayi nida na ɗau Alƙawarin Yiwa jama'a aiki aikin ya taso kice baza'ayi ba, bayan ke kike cewa inyi gaskiya a aikina? Kina so in bari a cutar da ita ne, ba zan iya jure in ga wani mummunan abu ya sameta ba"

"nifa na kasa gane meke wakana tsakaninka da wannan uwar É—akin, ka damu da ita dayawa"

"ba wani abu da yake wakana Umman Yusuf, kawai dai mahaifinta na mutuntani ne sosai"

"shikenan Yusuf, Allah ya bada sa'a zanyi kewarka zakayi kwanaki ba tare da Umma ba"

Yusuf yace  "nikaina ina tunanin hakan, Amma insha Allah ba abunda ze faru kwana biyar ne kawai tafiyar"

"to Allah ya bada sa'a"

Ya amsa da "Ameen"

Haka nan Umman Yusuf take jin kamar akwai wani abu daze faru dalilin tafiyar nan, sedai ta kasa gane na daÉ—ine ko akasin hakan.

Rana bata ƙarya sedai uwar ɗiya taji kunya, Yusuf ya shirya jakarsa da kayansa da ze dinga sawa da ɗan sauran kayan buƙatarsa a traveling bag.

Yaje gaban Ummansa yace "Umma na fito zan tafi, zan kwana a gidan gobe in Allah ya kaimu da Asuba zamu tafi"

Umma ta riƙo hannun Yusuf tace  "ka kula da kanka Yusuf, kai kaɗai ka ragemin, Allah yayi maka Albarka ya sadaka da dukkan Alkhairi, Allah yayi maganin maƙiyanka ya karemin kai.."

Kasa ƙarasawa tayi ta fashe da kuka, gaba ɗaya jikin Yusuf yayi sanyi yace "Umma ko in fasa tafiyar nan?"
Chapter 50 · 0% Book details