← Book details Akidata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 82

Sashe 6

Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amal ta ajiye spoon ɗin hannun ta a ranta  tace "Mhmm Yaya Ramla ina cikin damuwa tabbas, kuma na shiga damuwa ne domin ƙoƙarin samo mafita akan gagarumin lamarin dake barazanar jefani wani bigire da be kamata ba, Amma nasan bazaki taɓa bani goyon baya ba" Amma a zahiri tace
"karki damu bana jin daÉ—i ne kawai"

"Amma yakamata kije kiga likita"

Amal tace "ba abun damuwa bane, zan ware Insha Allah"

Tun Yusuf yana fama da tunani tareda sauraren kira daga uwaÉ—akkinsa har ya fidda rai, ya fara mantawa ya shiga sabgogin sa.

Kusan sati uku kenan da zuwan Yusuf gidan daga nan Amal bata ƙara saka shi a idon ta ba, wasa wasa abu ya ci gaba da damun zuciyar ta, gashi abu na ta faman damun zuciyar ta.

Alhaji Nasir Daula ne zaune a wani ƙaton falo shida wani mutum wanda zeyi sa' ansa, sukw hira tareda ƙyaƙyata dariya kai da gani kasan akwai kyakkyawan kusanci da fahimtar juna a tsakanin su.

"Alhaji Nasir nikam daughter tunda ta dawo ƙasar nan bata zo mun gaisa ba, kota manta dani ne?"

Alhaji Nasir yace "haba Bulama yaza'ayi daughter ta manta da kai, kawai dai kasan halin ta ne Nason kaÉ—aici har yanzu a haka take, Amma insha Allah zan turo maka ita har gida ku gaisa"

Alhaji Bulama yace "kana nufin har yanzu bata dena wannan É—abi'ar ba, ba ta warke ba kenan?"

"kai dai bari kawai, lamarin daughter yana damuna, ace kaf rayuwar ɗan adam be yadda da kowa ba, ba za ta sake da kowa ba, to koni wataran ina ƙasar nan idan bata ga dama ba se tace bata son inje inda take, narasa menene mafita "

Jinjina kai Alhaji bulama yayi yace" "wai shekarun ta nawa ne yanzun?"

"18 to 19, amma menene ma fitar?"

Alhaji Bulama yace "mafita É—aya ce shine kayi mata Aure, idan har aka yi mata Aure zata dena wannan halin nata"

Alhaji Nasir yace "Aure kuma? Dudu du guda nawa daughter take? Yarinya ce ƙarama kuma waze iya jure halayen ta?"

Alhaji Bulama yayi murmushi yace "kai kake ganin yarintarta idan ka aurar da ita daram zata zauna, samun wanda ze zauna da ita da halin ta abune me sauƙi, semu haɗa ta Aure da Fahad yaron guri na da yake karatu a china, dama bata sanshi ba kaga se a haɗa su, hakan ze ƙara zumunci dake tsakanin mu, kuma kaga tunda ita kaɗai Allah ya baka seka samu 'yan jikoki"

"Masha Allah gaskiya naji daÉ—in wannan shawarar taka, amma kasan semun bi a sannu idan nace zan tursa sata, za' a iya samun matsala"

"bakomai mu bi komai a sannu insha Allah babu wata matsala"

Suka cigaba da hirarrakin su.

Misalin ƙarfe goma na dare Yusuf yayi shirin sa tsaf ze kwan ta, wayar sa ta fara ringing, Sunan Abbas ne akan screen ɗin wayar, ya ɗaga suka gaisa

Abbas yace "Yusuf ɗazu Isa megadi ya kirani, yace min yarinyar nan ta bada saƙo tace zaka kaita unguwa gobe misalin ƙarfe goma na safe, ta jadadda goma na safen nan dan haka ka kiyaye"

"Shikenan zan je Insha Allah"

Tunda Yusuf ya kwanta ya gagara cikakken bacci, da yaje sallar Asuba sam be koma bacci ba, ya zauna ya ci gaba da lazumi, da sassafe ya tashi yayi wa mahaifiyarsa aikace2, kaman yadda 'ya mace za tayi haka Yusuf ya share ko' ina yai wanke2 yai girkin karin kumallo.

Koda Ummansa ta tashi tayi mamakin inda Yusuf yake gaggawar zuwa, bata son yawan takura masa dan haka ta ƙyaleshi.

Ƙarfe tara dai2 na safe Yusuf ya isa gidan Alhaji Nasir.

Isa na ganin sa yace "kai sannu da ƙoƙari Allah yasa ka ɗore, idan ka ɗore da zuwa akan lokaci saura kuma ƙalubale na gaba"

Yusuf yayi murmushi yace "Malam Isa kenan, Kowace sana'a tana da ƙalubale, sedai fatan Allah ya bamu ikon aikata dai2"

Da yake Isa akwai surutu kaman an ƙona shi aka, haka ya dinga zubawa Yusuf surutu kuma surutun nasa ba'aakan kowa bane se kan 'yar masu gida

Yusuf yace "wai ya sunan ta ne?, nifa har yanzu ko sunan ta ban sani ba"

Isa yace "Ai abune me wuya kaji sun kira sunan ta, ban san sunan ta na gaskiya ba, amma sunan ma dai da' ake kiran ta dashi akwai wuya dan ban riƙe ba"

Yusuf yace "ikon Allah wahalar sunan ta kai ka kasa riƙewa"

"haba Malam Yusuf kaman baka san iyayinku na 'yan binni ba? Wasu sunayen ma karasa sunan tumakine kona taurari"

Ba ƙaramin dariya Isa ya bawa Yusuf ba.

Suna ta ɗan taɓa taɗi, Isa yace "Aff gata can ta fito"

Yusuf ya ɗaga kai ya hango ta, ba ƙaramin kwarjini take da shi ba, taku take na ƙasaita akan wani dogon takalmi, dogon wando ne a jikin ta dark blue da riga light blue me dogon hannu, ta ɗaure kanta da ɗan kwali, amma gashin ta seda ya fito ta baya, fuskarta sanye da wani ƙaton glashi, wayar tace kawai a hannun ta babu jaka se key ɗin mota.
Guri ta samu ta tsaya, yayin da Yusuf yai sauri ya ƙarasa inda take tsaye, gaban sa na ta dukan uku2, yaje gabanta ya ɗan risina yace "barka da safiya ranki ya daɗe"

Bata amsa ba, ta miƙa masa mukullin mota, yasa hannu biyu ya karɓa a hankali ta furta masa Lambar motar da zata hau, kowace mota dake parking space tana da lamba, dan haka be sha wuya gurin gano wadda take nufi ba, abun da ya ɗaure masa kai shine kaddai a haka da wannan shigar zata fita?.

Ya fito da motar, ya fito ya buɗe mata ƙofar Bayan motar, wuce shi tayi taje ta buɗe gaba ta shige ta zauna.
Ya zagayo ya buɗe shima ya zauna yana ta Addu'a, gashi besan inda za suje ba, haka yai shahada ya kunna motar Isa ya buɗe musu gate, taiwa Isa Alama da hannun ta yazo, a guje jiki na rawa Isa ya ƙaraso gefen window ɗin da take zaune ya risina

"kwatanta masa gidan Bulama" ta furta kaman wadda aka yi wa dole, Isa yace
"kina nufin Alhaji Bulama Abokin Alhaji?"
ÆŠauke kai tayi tana kallon wani gurin daban, se Yanzu Isa ya tuna bata maimaita magana, ya gyara tsayuwa yayi wa Yusuf kwatancen gidan.

A hankali Yusuf yaja motar suka bar gidan, tunda suka fara tafiya babu wanda yayi wa wani magana, Yusuf ya dinga bin kwatancen gidan da Isa yayi masa, har zuwa ƙofar wani katafaren gida da suka zo ƙofar gate ɗin Yusuf ya kalle ta yace
"Nan ne ranki ya daÉ—e?"
Shiru tai masa ko motsawa ba tayi ba balle ta kalle shi, ɗan taɓe baki yayi, yai horn megadi ya buɗe ƙofa ya leƙo yana ganin motar ya ja da baya da sauri, ya koma ya buɗe gate ɗin gidan, gidan yayi kyau ya tsaru matuƙa sedai be kai gidan Alhaji Nasir ba.
Yusuf yaje parking space yayi parking, kafin ya sakko ya buÉ—e mata ta buÉ—e motar ta fita.
Fitowa yayi shima ko da wani abu dazata buƙata ya fito ya tsaya a bayan ta, me gadi ya ƙaraso cikin girmamawa yana gaishe ta, bata amsa ba tace "Bulama yana nan ne?"

"Eh ranki ya daÉ—e, Amma bana jin ya tashi"

"Ace masa gani na zo, ya tashi ko be tashi ba be dameni ba, bazan haura mintuna talatin a gidan nan ba"

Da sauri megadin yace "Angama ranki ya daÉ—e" nufi cikin gidan.

Ba tare da ta kalli inda Yusuf yake ba tace "biyo ni" ba musu yabi bayan ta, Wata rumfa dake harabar gidan me É—auke da fararen kujeru ta nufa taje ta zauna akan kujera, bayan ta yusuf ya tsaya ba tare da ya zauna ba.

Me gadi ne ya fito tare da wani matashi, matashin na ganin ta ya fara murmushi ya ƙara so inda take zaune

Matashin yace "Manya maganin ƙanana, Dama yaran talaka irin mu na ganin ku?"

Ɗan taɓe baki tayi tace "Gurin Alhaji Bulama nazo, yace yana son gani na, a ce masa gani nazo"

Matashin yayi murmushi yace "Yau kuma a Alhaji Bulama yake ba Daddyn ba, WIDAD kenan, to ki shiga ciki mana ku gaisa da su Hajiya da Iman mana"

Yusuf a ransa ya maimaita "Ikon Allah wani irin suna ne wannan? Widad?

Widad tace "banzo da niyyar ganin su ba a yanzu"

"Shikenan bari ayiwa Daddy magana"

Har ze wuce ya kalli Yusuf yace "am Sorry young man bamu gaisa ba"

Ya miƙawa Yusuf hannu, Yusuf yayi murmushi ya miƙo masa hannu da nufin suyi musabiha, Amma Widad ta kalli Yusuf ta haɗe rai tace
"don't try it"
A hankali Yusuf ya janye hannun sa suka fasa gaisawar, saurayin ya girgiza kai yace "Hmm bari in kira Daddy"

Yusuf a ransa yace "wai ita wannan shikenan kowa se dai yabi abunda take so? Kowa ma wulaƙanci take masa?"

Sunan a harabar gurin, aka turo 'yar aiki da kayan drinks da fruit ta kawo musu, yadda aka ajiye kayan ko kallon su ba tayi ba.

Ba tare da ta kalli inda Yusuf yake ba tace "duk wanda yazo gurin nan ban yadda ka kula shi ba, ba ruwan ka da kowa"

Yusuf yace "angama ranki ya daÉ—e"

Wani babban mutum ne ya fito sanye da jallabiya fara ƙal, aƙalla zeyi sa' an mahaifin widad.

Ya ƙaraso gurin fuskarsa ɗauke da murmushi, yaja kujera ya zauna ya kalli widad yace
"daughter yau kuma cikin gidan nawa ne baza'a shiga ba?"

"Eh bazan shiga ba banyi niyya ba, yanzu ma Daddy ne yace kana nemana nazo" ta bashi amsa kai tsaye

Alhaji Bulama yace "yanzu daughter ace kina Nigeria amma ki kasa zuwa ki ganni mu gaisa, ko na miki laifi ne?"

ÆŠan girgiza kai tayi tace "nafison zamana ni kaÉ—ai ne"

Alhaji Bulama ya kalli Yusuf yace "daughter shi kuma wannan fa?"

"driver nane, ba ruwan ka da shi"

"Shikenan naji ba ruwana da shi, amma idan bodyguards kike buƙata ai za'a iya samo miki, wannan ba abunda ze iyayi miki"

Ba kunya Widad Ta kalli tsabar idon mutumin nan a gadaran ce tace "bana buƙata, bana son kowa ya raɓeni"
Chapter 6 · 0% Book details